Sunday, 25 May 2014

YA YA ZAMU GUJEWA SHARRIN RAYUWA?

Hakika dan'Adam ma'abucin manufa da sako ne, to amma abin tambaya a nan shi ne mene ne sakonsa a wannan duniya?
An halicci dan'Adam ne don neman alheri da kuma sa'ada a rayuwa, kana kuma ya guje wa sharrori da kuma abubuwan da za su kai shi zuwa ga halaka. Don haka cikin rayuwa akwai alheri da kuma sharri, dan'Adam shi ne mai zaba wa kansa abin da ya dace da shi na daga alheri da kuma nesantar abubuwan sharri wadanda ba su dace da shi ba.
Ya 'yan'uwa, idan da a ce wani mutumin da ba mu san shi ba zai ba mu abinci ko kuma halawa, shin za mu kama ci ko sha ne haka kawai daga ya ba mu, ko kuma za mu tsaya mu gani cewa wannan abinci ko kuma halawar suna da tsabta alal akalla?
Lalle mu mukan zabi tsabta cikin dukkan abin da za mu ci ko kuma za mu yi amfani da shi don kiyaye kanmu daga kwayoyin cutar da za su janyo mana cututtuka da kuma sanya lafiyarmu cikin hatsari. Don haka wajibi ne mu aikata haka ga munanan ayyukan da suke lalata mana dabi'u da kuma mutumci.
Sannan kuma a duk lokacin da mutum ya kamu da wata cuta yakan tafi wajen likita don neman maganin wannan cuta, sai dai kuma a wasu lokuta yakan kamu da cutar ruhi, to amma sai ya ki zuwa neman magani; don kuwa ba ya ganinta a fili, amma kuwa tana iya lalata masa al'amurra daga karshe.
Dukkanmu, baya ga jiki, muna da ruhi da kuma hankali, don haka mafi munin sharrin rayuwa shi ne abin da yake damun ruhinmu da kuma lalata mana tsare-tsarenmu mu na kyawawan halaye.
Wadannan tsare-tsare na kyawawan halaye su ne suke nuni da daukakar dan'Adam da kuma ruhinsa, don haka idan dan'Adam ya rasa wadannan tsare-tsare, to babu abin da ya saura masa in ban da kawai abubuwa marasa amfani a rayuwarsa kuma zai yi rayuwa ce irin ta dabbobi da tsirrai.
Siffofin daukaka da alheri sukan arzurta mutum da abubuwan da za su taimaka masa da kuma sanya shi ya zamanto mabubbugar alheri ga kansa da kuma sauran mutanen da yake tare da su.
Baya ga haka kuma, akwai wata hakikar, ita ce kuwa cewa, mutum a wannan rayuwa yana nan ne tsakanin tuddan alheri da kuma na sharri.....don haka duk lokacin da ya kusanci tudun alheri, da hakan ne kuma zai nesanci tudun sharri.....
Idan waninmu yana da wani aboki da yake sadaukar da kansa dominsa a duk lokacin da yake fuskantar wata matsala, to a hakikanin gaskiya babu yadda za a yi ya cuce shi ko kuma ha'ince shi.....don haka sakamakon hakan shi ne son abokanmu da kuma fahimtar abubuwan da suke kewaye da mu.
Haka nan kuma idan wani daga cikinmu ya kasance mai biyayya ga mahaifansa, hakan yana nuni da cewa kenan ba za mu saba musu ba, kuma babu makawa abin da za mu samu shi ne kauna da kuma girmamawarsu gare mu, ko kuma kaunar sauran mutane da kuma girmamawarsu gare mu. Sannan kuma sama da hakan shi ne kauna da kuma yardar Ubangiji Madaukakin Sarki gare mu.
Wadansu mutane suna kokarin nuna mana cewa ma'anar alheri shi ne nisantar dadin duniya da kuma kaurace musu. To amma a gaskiya ma'anar alheri shi ne kyautata mu'amala da ni'imomi da iyawan da aka arzurtamu da su. Shi ne kuwa amfani da wadannan abubuwan jin dadi ta hanyar da ta dace.
Don kuwa Wanda Ya arzurtamu da wadannan ni'imomi da kuma iyawa ba Ya so ya haramta mana dadinsu, face dai so Yake mu yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace da za su sanya mu a kan tafarkin alheri har abada.
Saboda haka sharri shi ne mu gagara amfani da wadannan ni'imomi ta hanyar da ta dace da kuma mance manufofin da suka sa aka arzurtamu da su. To amma tambayar da take da muhimmanci a nan ita ce, mene ne yake sanya mu a wasu lokuta mukan zabi sharri duk kuwa da irin bala'in da ke tattare da shi ko kuma muke ba shi damar ya shiga cikin rayuwarmu ta samartaka mai kyawun fuska?!
Amsa wannan tambaya tana bukatuwa da gabatar da wasu tambayoyin na daban.

Shin muna daga cikin mutanen da suke kaskantar da kansu da cin mutumcin kansu ne? idan kuwa har haka ne, to sharri zai mamaye mu.......

Babu wani daga cikinmu da zai yarda a ce masa wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashe ko kuma ja-gora daga cikin ja-gorori zai sunkuya kasa don daukan wani abu maras amfani.
Mai yiyuwa ne wannan abu yana da girma da muhimmanci ga wasu, to amma irin girman shugaba ko kuma ja-gora zai hana shi damuwa da wannan abu, kuma bai kamance shi yayi hakan ba. Hakan nan ma, bai dace da mu 'yan'Adam ba mu bar kawukanmu su zamanto wajajen gwajin munanan ayyuka, hassada, zalunci, karya, sata, da dai zunubai da sharrori

No comments:

Post a Comment