Monday, 26 May 2014

GWAMNATI TA KASHE ALBANI DON WANI BURINTA

JAWABIN SAYYID ZAKZAKY (H) A YAMMACIN YAU LITINI 10/8/2014.

- Gwamnati ta kashe Albani domin wani buri nata.

- In mutum ya isa ya fito da wata gaskiyar ba wannan ba

- Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky(H).

Daga: Ammar Muhammad Rajab

Da yammacin yau Litinin 10/4/1435 (10/2/2014) jagoran harkar musulunci a Nijeriya Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ya fasa kwai ga me da shirin yunkurin kai masa hari da kuma fallasa ko su waye suka kashe shehin malamin Salafiyya dake zaune a Birin Zariya, da sauran bayanai.

Yayi wannan bayani ne jim kadan bayan kammala karatun Littafin Nahjul Balagah da aka saba karantawa a duk ranar Litinin a muhallin Husainiyyah Baqiyyatullah.

Ga cikakkaen jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) din jim kadan bayan kammala karatun Littafin Nahjul Balagah din;

***

Insha Allah mai yiwuwa ‘yan uwa da yawa suna da labarin shekaran jiya asabat an kai hari Gyallesu.

Daman mun samu labari na cewa wasu mutanen nan sunyi ‘Planning’, sun shirya cewa zasu je Gyallesu zasu zuba makamai, sai suzo sai suce sun kama makamai, wanda da shi ne aka kashe Albani wancan Asabat din. Saboda haka shi’a ne suka kashe shi. Daganan kuma sai suyi kashe-kashe.

To, ni da naji wannan maganan har ma dariya ya bani. Nace aiko zai zama katon wauta. Wannan ba karamin wauta ba ne, tunda yake ainihin zaku tonawa kanku asiri ne ai. Ku nuna cewa kune kukayi kisan kan.

Domin mun kaddara koda da gaske ne kaga makami, Ya akai ka tabbatar cewa ne da wannan ne akayi kisan? Me yasa kuma Gyallesu? Don wauta! A rasa inda za a ga makamin sai wai a Gyallesu. Zasu je Sai su danganta tashi da.

To Shikenan dai na dauka kila a samu wani mai hankali a cikinsu yace wannan gurguwar dabara ce, kawai kwatsam sai gasu sunzo ranar asabar, to wannan ma gurguwar dabarar na su ta cika yawa,

waccan Asabar din kunyi kisan kai a wajen Gaskiya, kuma wannan Asabar din an ganku a Gyallesu. Wa kuka zo kashe wa kenan? Ai ma basai an baka bayani ba, daganin su a Gyallesu kasan sunzo kashe wanene? To shike nan dai, suka kwanan anan.

Daman muna da mutanen boye, amma sai mukace a nuna musu na bayyane tunda baza suga na boyan ba. Sai suka mutane duk inda sukayi ana biye dasu, to kuma dai hakanan sai Allah yasa musu razani wasu suka tashi tun cikin daren.

Da safe sai suka yada cewa wai sunzo ne kare Malam. Wai suna da ‘Intelligents’ wai suna da labarin cewa ‘yan salafiya zasu kawo mishi hari ne shiyasa sukazo kare shi, to sai kuma suka tafi abun su, to idan da gaskene basai ku cigaba da zama ba, kuma duk inda zamu yi kuyi tabinmu don ku kare mu daga salafiyya?

Sai suka shirya cewa ranar Litinin (yau kenan) in an taso Nahjul Balagah akan hanya zasu zo su bude wuta, sai suce yauwa daman sun yada cewa sunje kare Malam akan ‘yan salafiyya zasu kai hari to yanzu ga ‘yan Salafiyya sun kai hari (Bansan ko sunanan akan hanya suna jira ba), sun dai ce zasuyi Litinin, idan basuyi ba ko watarana idan an tashi karatu daga Husainiyyah ko in za a zo Husainiyyah zasu bude wuta.

Fakam da yawa mukanji shiri bamu cika damuwa da mu gaya muku ba, saboda me ne? Wani lokacin iyakan shi shirin ne kawai. Ba yakan zama sun zartar ba, iya kanta shirin ne kawai (ba bukatan ai magana).

Alal misali; muna da labarin sun shirya cewa zasu aukawa maulidi (Maulidin nan da akayi na bana), sai suka sauwala cewa su fara aukawa maulidin Kano ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ran 17 kuma su aukawa na Zariya.

Tun a batun na Kanon suka samu sabani a tsakanin su da su ‘yan ‘Security’ din da su ‘yan siyasa din, wasu suka ce su basu yarda, Shikenan sai ya kwaranye. Bamu ma fada ba. Bamuce komai ba. Saboda shi wannan iya kanta ya rage ai ‘Alarm’ ba a kai ga aikatawa ba.

Saboda haka wannan ma da suka ce zasu zo su zuba makamai a Gyallesu ba da don mun gansu ba baza mu fada ba (don ba magana ba ne).

To amma sai sukayi yunkurin yi! shiyasa muke gaya muku. Mai yiwuwa yanzu ko shima zasu tsaya a bakin hanya (don sunsha yin ‘Attempt’ in za a zo Husainiyyah suyi harbi), sunsha yin ‘Attempt’ kuma mukan wuce kuma bama fada.

Ko a wani ‘Usubu'ul Wahada’ wata ranar Juma'a lallai sun ajiye masu harbi, kuma munzo ko maganan ma ba muyi ba sun riga yanzu sun san munsan da masu harbin.

Wannan ya bani mamaki, wautan (gurguwar dabarar) tasu ta cika tsanani, mu kaddara, da sunyi wannan wauta din da sun tona ma kansu asiri ba kadan ba. Kuma da sun san wadanda suka taba ba irin wadanda zasu taba bane suji shiru ba ne. Yauwa!

Munsan su suka kashe Albani, amma munsan mutanen su suna jin tsoron su fada, amma mu sai mu fito musu da komai da komai, sai muce da wane da wane ne sukayi, mu in mune zamu iya fada, amma su sun sani amma ba za su iya fada ba suna jin tsoro, mu ko bamu jin tsoron kowa.

Wannan wauta har ina? Idan da ace mu masu kisan kai ne harma da za kace, banda wauta (kace ka jingina ma mazhabar addini kisan kai) ai sai dai kace wane ne yayi kisa ko? Kila shiyasa suka zabi suce Gyallesu. Don ace wane ne yayi kisan kenan. To inda mu masu kisan kai ne (masu kashe wani ne) da mun kashe wadanda suka bude mana wuta rana tsaka amma akan ganmu har muna hannu da su.

Wanda suka bada umurni suka bude wuta akanmu rana tsaka mun san su, sun san mun sani amma har muna hannu da su (sukan miko hannu mu gaisa), amma iyakan sanin mu Albani har suka kashe shi bai taba kashe kazar mu ba ko ya fasa kwanmu. Ko kuna da labarin ya taba kashe mana kaza?

To ga wanda suka bude mana wuta
rana tsaka mun san su, wa muka kashe a cikin su?

Ballatana kuma, ko su magidantan su na waje Amerika da Isra’ila, duk kirkiro kungiyoyin ta’addanci da suke yi suna cewa kungiyan kaza na musulmi basu iya kirkiro kungiyan shi’a na ta’addanci ba. Bai yiwun musu ba. Sun iya kirkiro na ‘Ama’ ne saboda su ‘Ama’ karazube suke basu da shugaba (kowa shugaban kan sa ne),

su ko shi’a hatta ka mari mutum baza ka iya yi ba sai da izinin ‘Mushtahidi’ (Mushtahidi yana nufin Ayatullah). shi’a ba yana daukan yayi abun da ransa ya ga dama ba ne, komai zaiyi dole ya zama bisa ka’ida ne, saboda haka horo wanda za a ji zafi ‘ittifakan’ ka tambaya, ba ayi sai da Izinin ‘Mushtahidi’ ballantana kisa.

Horo wanda za aji zafi koda duka ne mutum bazai yi ba sai da izinin ‘Mushtahidi’, wannan a duk duniyan shi’a haka yake ba a sabani ba ra’ayi na biyu.

Sannan yaki ‘Iftida’a’ (aje a samu wadansu mutane a yake su) da unuwanun ana yakansu su shiga musulunci ba wanda ke da izinin ba da wannan sai Imam Mahdi in ya bayyana. Wannan ‘ittifakan’ duk kaje duniyan shi’a gaba daya kowane duk wanda ya karanta abun dazai gaya maka kenan.

Saboda haka bayanda za ayi kaji wani yaje da unuwanin jahadi yaje yakai hari indai shi’i ne ba a taba ji ba. Don haka ne ma su masu kirkiro kungiyoyin ta’adda (Amerika da Isra’ila) su jinginawa musulmi basu taba kirkiro kungiyar shi’a ba suka kai wani hari. Na ‘Ama’sukeyi don haka ma sunayen su sai kaji ance sunna kaza, basu taba cewa na shi’a ba. Saboda sun san ba wanda zai yarda.

Saboda ba yanda za ayi shi’i ya kai ma wani hari. Shi’i yasan cewa indai yaki ne da unuwanin yaki sai dai Imam Mahdi ya bayyana, amma da unwanin kariya shi ne ya zama wajibi (akai maka hari ka kare kanka wannan kuwa). Amma ba da unuwanin kai kakai hari da nufin jahadi bazai yiwu ba sai Imam Mahdi ya bayyana.

Saboda haka wannan zai zama wauta, bayan kunyi ta’addancin ku, kuzo kuce zaku jinginawa wani wannan shi ake cewa ‘Botani’.

Bayan ku kukayi wannan aika-aika kuma kuna neman wai zaku kala wani kuma ku ka rasa wanda zaku kala wa sai wanda ba yanda za ayi ku kala mashi wani ya yarda duk duniya.

Ko kana zaune anan kaji ance; wasu shi’a a kashmir sun kai hari wuri kaza kasan karya ne. Kasan karya ne, don bazai yiwu ba. Ba dai shi’a ba.

To Ala hayya halin wa’innan wawaye wanda na kira su ‘Bunch of Idiots’, lallai wautan su ta cika yawa, dama kullum wautan dai kenan.

Da yake Basu da wani tunani illa suna da bindiga zasuyi harbi to shikenan zasuyi harbin ne, sun dauka bindiga shi ne komai. To bindiga ba shi ne komai ba, ba ita take yin komai ba. Amma ita kuke da. To muna da abun da yafi bindiga, muna tinkaho da Allah (T) ne da addini sahihi wanda ya aiko Annabi da shi da a’immatul ma’asumin wanda su muke bi.

In mutum ya isa ya fito da wata gaskiya ba wannan ba. Don ita gaskiya kwara daya ce.

Alhamdu lillah mungode ma Allah da ya kasamce tana tare damu muna tare da ita. Insha Alllahul azim.

Wasallahu ala Muhammadin wa’alihid dahirin.

No comments:

Post a Comment