__________________(1)___________________
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Menene matsayin bashin nan na Treasury Bills?
SHAIKH ZAKZAKY: To, Treasury Bills, kamar bashi ne wanda mutane ke ba banki, wanda ba shi da wani bambanci da sauran basussuka da aka riga aka
sani, wanda su bankunan kan bayar ko a
ba su. Wanda in dai da ruwa, to, bai
halatta ba, in ba ruwa kuma, to sunansa
bashi. In kuma jari ne za a zuba, ya
zama ka ci riba. Abin dai da aka sani shi
ne, bashi ba ya jawo kudi a shari'a.
Kuma jari ne yakan jawo riba ba riba
ba.
____________________(2)___________________
TAMBAYA: Meye matsayin mutumin da ya hada salloli hudu bai yi su ba sai da asuba ya hada su gaba daya? Shin yana da sallar ko ba shi da ita, kasantuwar lokacinta ya wuce?
SHAIKH ZAKZAKY: To, ya aikata haram.
Domin bai halatta ga musulmi mai hankali baligi ya bari lokacin salla ya wuce bai yi sallar ba. Sai dai in ya yi, ba za a ce ba shi da salla ba don lokacin ya wuce, domin tana nan a kansa. Ana ce
wa wannan ramuwa.
Lalurar da kawai ke iya halatta mutum ya jinkirta salla har lokacinta ya wuce shi ne, rashin abubuwan tsarkin nan guda biyu, wato ruwa da kasa, wanda idan babu su, ba abin da zai yi illa ya kyale in lokaci ya wuce sai ya biya. Wannan kuma ba laifi bane.
Sai kuma lalurar rashin hankali, wanda idan da barci ne, alal misali, shi ma in ya farka sai ya biya. In kuma hauka ne ko suma in har ya cika lokacin salla din, to, shi ma sallar ta fadi a kan sa. Saboda haka, haka kawai bai halatta ma mutum ya fasa salla ba har lokacinta ya wuce.
Amma in ya yi haka nan ya yi haram, kuma in ya yi salla din bayan lokacinta, ta yi. Kuma ma ta hau kansa ya biya komi dadewa.
_____________________(3)_________________
TAMBAYA: Akramakallahu, shin idan
mutum ya sami dama yana iya zuwa ya
kai wa musulmi taimako akasashen da
kafirai ke yaki da muslmi, misali Falasdinu ko Iraki?
SHAIKH ZAKZAKY: To, lalle ban san shi
abin da yake nufi ba. Wala'alla yana nufin kai gudummawa na kudi ne. Wanda ba ya bukatar sai ya tashi takanas ya tafi da kansa ya kai wannan gudumawa din.
Akwai hanyoyi da daman gaske budaddadu na aikawa da gudummawa, musamman dai Palasdinu, kuma zai wahalar gaske ya zama shi (mai tambaya din in shi ne yake so ya kai), ya zama zai iya zuwa wadannan wurare da ya ambata don ya kai wata gudummawa, ko ma wace iri ce.
Amma dai yana iya bayar da gudummawarsa daidai gwargwadon hali yana zane a nan ba tare da ya tafi can ba. In wannan yake nufi, to, sai mu ce masa eh, yana da kyau haka nan. Sai ya yi musharaka da dukiyarsa a yayin da ba zai yiwu ya yi musharaka da jikinsa ba.
No comments:
Post a Comment