Monday, 26 May 2014

NAU'O'IN SABO


Nau'o'in Sabo
Kamar yadda aka sani ne cewa sabo shi ne bijire wa dokokin Allah da kuma barin tafarkin gaskiya da adalci, don haka ne ake ganinsa a matsayin mummu-nan al'amari wanda ya saba wa hankali. Kana kuma a dalilin haka ne ma Musulunci yake ganin duk wani aikin da ya saba wa ka'idojin kyawawan dabi'u a matsayin mummunan aiki kana kuma mai cutar da dan'Adam. A saboda la'akari da hakan, Musulunci bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyanar da ayyuka da dabi'un da suke munana ne kuma zunubai ne:
1. Rashin aikata wajibai kamar salla, azumi, aikin hajji da dai sauransu.
2. Sabo yakan tabbata ta hanyar aikata ayyukan da aka haramta, kamar shan giya, riya, zina, jiji-da-kai, hassada, rawa da dai sauransu.
Hakika wadannan masu sabo ba su kyauta wa kansu ba ta hanyar bayyanar da kansu ga azaba da kaskanta da kuma fushin Allah.
3. Ayyukan sabon da cutarwarsu yakan shafi sauran mutane. Wadannan masu aikata sabo sukan cutar da dai-daikun mutane da kuma al'umma gaba daya ta hanyar aikata munanan ayyukan da suke janyo barazana ga zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalin al'umma.
A bisa tsarin Musulunci, aikata munanan ayyuka kamar kisan kai, sata, cin amana, yaudara, zalunci, cuta, cin kudin ruwa, boye kayayyakin amfanin yau da kullum don ya yi tsada[1] da dai sauransu, sukan haifar da cutarwa mai yawan gaske ga ayyuka da mu'amalolin jama'a. Koda yake, a dokokin tsarin Sekula[2], manyan munanan ayyuka kamar cin kudin ruwa, boye kayayyakin amfani, shan giya da muggan kwayoyi ba a dauke su a matsayin laifuffukan da za a iya hukumta mutum a kansu ba.
A saboda wannan dalili ne, al'ummomin da suke karkashin irin wannan tsari suke fuskantar hawa-hawan faruwan muggan laifuffuka da suke haifar da barazana ga salin tushen zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma. Inda kuma aka halalta ayyuka irin zina, luwadi, shan giya, safaran muggan kwayoyi, caca da sauransu, sannan a wasu lokuta ma ake bayyanar da su a matsayin ayyukan da aikata su ba laifi ba ne. Idan har aka yi la'akari da wadannan bayanai, za a ga cewa rundunar shedanci da kuma laifuffuka da ke cikin mutane a sake suke kana al'umma kuma suna fuskantar yaduwar zubar da jini, kashe-kashe, yake-yake da muggan cututtuka. To amma shi Musulunci a nasa bangaren ya yi iyakacin nasa kokarin wajen fadakarwa da kuma tsara al'amur-ran 'yan'Adam da kuma kirkiro shirye-shirye don rage tasirin miyagun ayyuka da kuma gabatar da dokoki da tsare-tsaren gyara wanda zai bai wa mutum da al'ummar da yake ciki damar rayuwa cikin aminci da kwanciyar hankali.
1. A baya-bayan nan wasu tsarurrukan siyasa sun dauki boye kayayaki a matsayin laifi wanda ake hukumta mutane a kai.
2. An fassara tsarin "Sekula" da cewa wasu tsarurruka ne wadanda dan'Adam ya kirkiro ba tare da la'akari da dokokin Allah ba.

No comments:

Post a Comment