Nasiha ga 'yan uwa daga bakin Sayyid Zakzaky (H).
A taron Yaumu Shuhada' na bara 1434.
Ga yadda nasihar ta kasance, Sayyid Al-Zakzaky (H) Yace:
"To, daidai gwargwado na san dai na d'an tatta'bo kowane janibi, bari in 'kare da yin nasiha ga 'yan uwa 'generally'.
Kai da ake ta hanqoran kullum ana son a ga bayanka, to kai kuma kar ka kwanta kana barci. 'Bata hankalin dare, raya dare da addu'a, yi salla, karanta Al-qur'ani, memi kyautata alaqarka da Allah, ka tabbatar da cewa BAKA CI HARAM BA. KAR KA CI HARAM, KAR KA CI HAQQIN WANI. Wannan muhimmin abu ne.
Nemi na kanka, KAR KA ZAMA 'DAWAINIYA GA WASU. KUMA KA TABBATAR DA CEWA ABINDA KAKE KAI WA CIKIN HALAL NE.
Domin ya zo a hadisi cewa, wanda ya ci haram, in yayi sa'a ne ya yi barci, in ba haka ba zai sa'bi Allah ne. Ka tabbatar da cewa halas kake ci. Halas ne abincinka, halas ne suturarka, halas ne wurin zamanka.
Ba murd'iya ba, ba sata ba, ba almundahana ba, ba qarya ba, ba cin amana ba.
Cikin amanar kuwa HAR DA AMANONIN DA AKE BAYARWA NA 'YAN UWA. KAR KA 'DAUKA CEWA WANNAN AI NA KOWA DA KOWA NE. Don wasu sun d'auka dukiyar hukuma kamar na kowa ne, suna ganin kamar ba mai shi ne.
A'a dukiyar al'umma ne, saboda haka cin amana ne in dukiyar ta zo hannunka ka ci.
Ku tabbatar da cewa kun ci halas, kun yi aikin kirki. Wannan muhimmin abu ne.
Kuma kar mutum ya ga kamar ana yin abin ne da shi, ya ga cewa shi ma 'bangare na abin. Kar ka ga abu na tafiya lafiya lau, amma kai ba lafiya kake gani ba, saboda kowa kabarinsa daban ne.
Kuma kowa za'ayi masa hisabi kan aikinsa. Kai a qashin kanka, dubi kanka ka gani ya kake ?!
To, in ya zama ka kyautatu, irinka wane ya kyautatu, aka samu kyautatattu, sai mu had'a majmu'a na kyautatattun mutane,
kuma na sha fad'in cewa in har dai za mu canza wannan al'umma, to dole sai mu ma mun canza.
Ba yadda za ayi mu iya gyara al'ummar nan alhali mu ba mu gyaru ba.
Na fi jin takaicin na ga mummunan hali tare da 'yan uwa. Idan ya zama suna yin d'abi'a irin ta 'yan Nijeriya, to Nijeriya tana nan kenan.
Yanzu mutane sun d'auka qarya da rashin riqon amana ya zama wani zaunannen abu ne. Sun d'auka qarya ba wani abu bane. Mutum sai ya sharara qarya, yana ganin indai zai samu shi ke nan, ya ji ya gani.
To, haka nan mutane suke, ba su d'auka akwai wata d'abi'a da ya kamata su yi iltizami da shi ba.
Na sha fad'a a wurare da dama cewa na'am in ka kwatanta mu da sauran mutane, mun fi sauran mutane.
Ko taronmu ne za ka ga natsuwa a ciki ya fi na saura; amma ba yana nufin lafiya lau ne ba. Mu burinmu mu wuce hakan. Muna so mu ga an wuce hakan. Ta nan za mu san cewa sauyi na nan tafe in sha Allah.
Wannan al'umma ta sani, kuma har da maqiya cewa fatanmu kawai shi ne wannan taro namu, shi ne mustaqbal wannan al'umma. Da baicin haka ba, sai mu ce ba wani fata.
Da ba don da wannan fatan ba, sai Mutum yace don me ma zai rayu a qasar nan ne ?! Rayuwa kawai azaba kawai.
K'asar da muke da man fetur amma ba man fetur d'in. K'asar da ke da arziqi, amma mutane na fama da talauci. Wahaloli, ba lantarki, ba ruwan famfo, ba man fetur, ba abin hawa.
Miliyoyi mutanen qasar nan har yanzu qajagoji ne ake sayowa, wuqaqe, suna ta kashe mutane. Duk da haka kuma ba a kyale mu ba, sai masifofi. A 'bullo da wannan, a 'bullo da wannan, har da wani shi Boko-haram. To yanzu yayi 'failing' zasu qirqiro wani abin."
------------------------------------
WANNAN SHI NE NASIHAR MAULANA SAYYID ZAKZAKY (H) GA 'YAN UWA, DA FATAN ALLAH YA TAIMAKA MANA MU FI QARFIN SON ZUKATANMU, MU YI AIKI DA WA'DANNAN MUHIMMAN NASIHOHI TA SU SAYYID (H).
SU KUMA SU SAYYID (H), ALLAH YA QARA MASU LAFIYA DA KARIYA TA MUSAMMAN DAGA SHARRIN DUKKAN MAI SHARRI, DA MAKIRCIN DUKKAN MAI MAKIRCI.
MU KUMA ALLAH YA QARA MANA BIYAYYA GA HADAFI DA UMURNIN SAYYID AL-ZAKZAKY (H) KAI TSAYE BA TARE DA KARKACEWA KO KADAN BA.
No comments:
Post a Comment