BABU WANI MUTUM DA KE DA ZUCIYA BIYU SABODA HAKA BABU YADDA ZA'A YI MUTUM YA HADA SOYAYYAR MUHAMMAD DA AALI MUHAMMAD DA KUMA SOYAYYAR MAKIYANSU.
Kamar ko wace Laraba, yau ma Sayyid Zakzaky (h) ya gabatar da tafsirin Qur'ani mai girma. A yau an yi tafsirin ne a cikin Suratul Baqara aya ta 97-100
بسم الله الرحمن الرحيم
قل من كان عدوا لجبريل فإنه مزله على قلبك بإذن الله مصدقا لما بين يديه و هدى بشرى للمؤمنين
KA CE YA KAI WANNAN MANZO DUK WANDA YA KASANCE MAKIYIN JIBRILU, TO SHI NE YA SAUKAR DA SHI (ALQUR'ANI) A ZUCIYARKA DA IZININ ALLAH YANA MAI GASKATA ABIN DA KE GABANINSA (NA SAUKAKKUN LITTATTAFAI) KUMA SHIRIYA DA ALBISHIR GA MUMINAI.
A sharhin wannan ayar wanda Malam ya karanto daga tafsirul Imam Askariy (a.s), ya yi bayanin asalin wannan gabar da yahudawa KE yi da mala'ika Jibril da kuma falalar Qur'ani da yadda ya zama shiriya da kuma albishir ga muminai. Daga ciki akwai cewa Qur'ani zai zo a siffar mutun ranar kiyama sai ya zo da wanda ya karanta shi kuma ya fahimci abin da ya karanta din sannan ya aikata shi, ya nemi cetonsa a gaban Al'arshi kuma a ba shi. Sannan a nemo iyayen shi ma'abocin Qur'anin a ba shi cetonsu kuma a sanya musu tufafin da kimarsu ya fi duk duniya da abin da ke cikinta. Sai su yi mamaki su ce: Ya Rabbi ta yaya muka sami wannan ba da ayyukanmu ba? Sai a ce musu suna mamaki ne? To akwai kambun (crown) karama da za'a sanya musu wanda ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, sannan bai fadawa zuciyar wani ba.
Sai a ce musu WANNAN SHI NE LADAN KOYAR DA DANSU QUR'ANI DA SUKA YI DA KUMA KOYA MASA SOYAYYAR MUHAMMAD (S) DA ALI (A.S) WADANDA BABU WANDA ALLAH ZAI KARBI AIKINSA SAI DA WILAYARSU DA KIN MAKIYANSU. WANNAN LAZIM NE DOMIN BA'A HADA SOYAYYAR MUTUM DA SOYAYYAR MAKIYINSA. SHI NE MA'ANAR ALLAH BAI SANYA ZUCIYA BIYU GA WANI MUTUM BA.
من كان عدوالله وملإكته ورسله و جبريل و ميكال فإن الله عدو الكافرين
WANDA DUK YA ZAMA MAKIYIN ALLAH DA MALA'IKUNSA DA MANZANNINSA DA JIBRILU DA MIKA'ILU TO ALLAH MAKIYI NE GA KAFURAI.
A sharhin wannan ayar Malam ya yi bayanin cewa tunda a ayar da ta gabata an kawo kissar dalilin gaban yahudawa da Jibril (a.s) (mu bamu kawo ba SABODA takaitawa). Dalilinsu wai shi ne Jibrilu na saukar musu da musifu ne kuma yana rusa mulkinsu, amma shi Mika'ilu shi ne ke saukar da yalwa da kuma karkafafa mulkinsu. Ya zo cewa su yahudu sun tura wani hazikin bayahude mai ido daya mai suna Abdullah bn Suriyya ya yi ma Annabi tambayoyi da yawa KUMA Annabi na bashi amsa, yana cewa ka yi gaskiya. Sai da ya gama sai ya ce saura abu guda kuma in har Annabi ya amsa masa, to zai yi imani. Sai ya ce wa ke kawo maka wahayi? Sai ya ce Jibril, sai bayahudan ya ce ai wannan makiyinmu ne da dai Mika'il ne da mun yi imani.
Malam ya karanto kissar Bukhtanasar wanda annabawan bani isra'ila suka bayar da labarin cewa zai zama sarki kuma ya rusa Baitul Muqaddas. To lokacin da yake yaro mai rauni SAI yahudawa suka aiki Annabi Daniel domin ya kashe shi sai Jibril ya kare ya ce BA'A hukunta mutum sai ya aikata laifi ko da kuwa an san nan gaba zai aikata. To da ya girma ya zama sarki kuma ya rusa Qudus din shi ne suka kulla gaba da Jibril.
To su kuma nasibawa na wannan al'ummar da suka ga Imam Ali na yaki fiye da yadda karfin dan'adam ke iya yi, sai suka ce yaya aka yi haka? Sai aka ce musu Jibril ne a damanshi, Mika'ilu kuma a hagunshi. Sai suka hada gaban Ali da na mataimakan nasa biyu. To shi ne Allah ya yi musu raddi a wannan ayar tare da yahudawa makiyan Jibril. Fadin Allah cewa cewa Allah makiyin kafurai ne ya nuna cewa masu gaban nan kafurai.
ولقد أنزلنا إليكءايت بينت وما يكفر بها إلا
الفسقون
HAKIKA MUN SAUKAR MAKA DA AYOYI MASU BAYANI BABU WANDA YAKE KAFURCEWA DA SU SAI FASIKAI.
Ma'ana ayoyi masu bayani akan wilayar dan'uwanka kuma babu masu kafirce musu sai masu fita daga da'an Allah da ManzonSa.
أوكلما عهدوا عهدا نبذه فريق منهم بل أكثرهم القانون
DUK LOKACIN DA SUKA DAUKI WANI ALKAWARI SAI WASU GAGA CIKINSU SU WATSAR DA ALKAWARIN KUMA DA YAWANSU BASU YIN IMANI.
Wannan alkawarin shi ne na cewa in Annabi ya bayyana zasu bi shi. An gaya musu cewa shari'arsa ita ce kammalalliya kuma zata kawo karshen shari'arsu. Sai suka ce su ba zasu fifita wani annabi akan annabinsu ba kuma ba zasu fifita wani littafi akan littafinsu ba kuma ba zasu fifita iyalan wani annabi akan na annabinsu ba sannan ba zasu fifita sahabban wani annabi akan nasu ba. Sai Allah ya daga dutse a birbishinsu, sai suka ji tsoro suka fadi suna masu sujuda ta gefen goshi (ta'afir), suna hange dutsen domin tsoron kar ya fado musu. A haka suka dauki akawarin. Fadin Allah cewa wani bangare daga cikinsu ya nuna akwai kalilan daga cikinsu da suka rike alkawarin kyamkyam kamar Abdullahi bn Salam wanda ya musulunta.
____________________
SHAFIN SHI'A NIGERIA NA YIN KIRA DA BABBAN MURYA GA AL'UMMAR MUSULMI DA SU NEMI CD TAFSIRIN DOMIN CIKAKKIYAR FA'IDA SANNAN KUMA MALAM (H) YA CE GA MAI SON KARIN BAYANI YA DUBA TAFSIRUL IMAM ASKARIY SHAFI 448-451.
No comments:
Post a Comment