Monday, 26 May 2014

TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)


____________________(35)_________________

TAMBAYA: Allah ya jikan Malam, menene ingancin hannun da ake sanya zobe, shin a hannun dama ake sanyawa, ko a hannun hagu bisa sunna ta Manzon Allah (SAW)?

SHAIKH ZAKZAKY: Idan kwara daya ne rak, dama ya dace da shi, idan kuwa ya fi daya, in ka sa hagu da dama babu laifi. Bilhasali, mustahabbi ne ka sa daya a dama, daya a hagu. A 'binsari' zai sa na dama. Sannan kuma a hagu, sai ya sa a 'khinsari'.

____________________(36)_________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halatta mutumin wata jiha ya yi takardar zama dan wata jiha don ya sami aikin gwamnati a wannan jiha?

SHAIKH ZAKZAKY: In an fahimce shi a kan cewa ya canza jiha ne, yanzu ya koma dan wata jiha, to babu laifi da shi. Amma in yaudara ya yi, to ya yi laifi. Idan su sun dauka shi dan jihar ne, amma shi ya yi yaudara ne, ya yi karya kenan, ya nuna cewa shi dan jiha ne kawai don ya sami wannan, alhali shi ba dan jiha bane.
Ala ayyi halin dai, na san kana iya canza mazauni idan ka ga dama. Saboda haka in wannan canza mazunin ka yi, ka ce yanzu ka koma dan waje kaza, babu laifi.

In fata a 'unwanin' canzawa ya yi daga wata jiha zuwa wata jiha, ba a 'unwanin' yaudara da karya ba. In karya ne da yaudara, ya zama haramun. Kuma in ya sami wani hakki a nan wanda yake ba nasa bane, zai zama ya ci hakkin wani kenan.

__________________(37)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko sanya wata da tauraro da musulmi suke yi a masallaci yana da asali?

SHAIKH ZAKZAKY: Ba za mu ce ba shi da asali ba, kuma ba za mu ce yana da asali ba, wato mu ce yana da matsayi a shari'a wanda ta ce a yi ba.

Sai dai wani abu ne wanda yake a tarihi a kan cewa mayaka sukan kasance suna da alamomi wanda yake bambanta su daga sauran, wanda sukan sa a tutocin su. Wannan wani abu ne ma'alumi adatan.

Kuma a lokacin Annabi ma an yi amfani da irin wannan. Wanda aka ce ma a tutar Manzon Allah akwai mikiya. Kuma wani lokacin da aka yi yakin Afranj, Faranjawa, wadanda ake ce wa 'Crusaders' kenan, sukan zo da alamomin sakandami a tutocinsu. A wannan lokacin sai ya zama su ma Musulmi sukan sa wata da tauraro a tutocinsu.

Haka kuma dauloli da daman gaske sun yi amfani da irin wannan, har yau da kullum ya zama wani abu wanda ake alamta al'ummar musulmi da shi.

Wato ba za mu ce ba shi da asali ba, ba kuma za mu ce yana da asali a shari'a ba. Sai dai a shari'a, duk abin da ba a hana ka ba kana iya yi.

An san akan yi alami na mayaka ko ta al'umma, kuma babu laifi idan ku mayakan musulmi ko kuma al'ummar musulmi suka dauki alami, kamar wanda suka ga yana da dangantaka da addininsu, suka sa shi a matsayin alamarsu.

Kamar tauraro, masalan, ko kuma da jaririn wata wanda yake al'ummar musulmi suna ba jaririn wata muhimmanci saboda ayyukan ibadodinsu na azumi da Hajji da sauransu. To in suka dauko shi suka ce saboda wannan ya alamta wani abu nasu, ba wani laifi da shi.

____________________(38)_________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Menene hukuncin tsai da haihuwa da wasu ke yi da umurnin Likita ko ba da umurninsa ba?

SHAIKH ZAKZAKY: In dai ba da azalu ne ko kuma kaurace ma mace a lokacin da ba a bukatar ta dauki ciki ba, wato wanda za a yi yarjejeniya tsakanin mata da miji ba, wanda yake shi an san shi, wadansu hanyoyi da yanzu ake amfani da su, sun nuna tamkar zubar da ciki ne da wayo.

Domin ya tabbata cewa magungunan da mutane suke sha na maganin hana daukar ciki, ashe ba yana hana daukar ciki bane, yana tarwaatsa cikin ne in ya dauku. Ko dai a lokacin da kwan ya sami matsattsakun namiji a kan bututun nan nasu da ya fito, kafin ya kai ga mahaifa sai ya tarwatse, don shi wannan maganin zai hana shi zuwa ga wurin, ko kuma in ya je mahaifar, zai zama ba zai iya mannuwa da mahaifar ta yadda zai zama da ba, sai ya dagwargwaje ya zube.

Ka ga tamkar zubar da ciki ne ta wata fuska, tun yana dan karami. Saboda haka idan mutane suka dauki matakin da shari'a ta sani, kamar irin na azalu da kauracewa domin gudun kar a dauki ciki a wani lokacin da ake tsammanin za a dauka. Za mu iya cewa ba laifi da shi, in tsakanin ma'aura biyu suka yi yarjejeniya, hakkin miji ne hakkin mata ne, sai sun yarda dukkansu. Da shawarar Likita ko ba da shawarar Likita ba.

Amma idan ana batun kamar in ta dauki ciki, zai kai ta ga mutuwa ne, masalan, ta inda ba zai yiwu ta yi ciki ta haihu ba tare da ta mutu ba, to wannan sai ya zama hana daukar cikin zai zama ya halasta, ko ma ya wajaba.

No comments:

Post a Comment