Raja’a
1- Ma’anar Raja’a
Raja’a tana nufin Allah madaukaki zai dawo da wasu mutane duniya bayan sun mutu a surar su da suka kasance a kan ta da can, kuma wadannan sun kasu kashi biyu daga cikinsu akwai mai imani tsantsa a rayuwarsa ta farko da kuma wanda yake mai tsantsar kafirci, sannan sai Allah ya ya juya ranakunsu ya saka wa masu gaskiya a kan masu barna, wanda aka zalunta a kan azzalumi, kuma wannan zai faru ne lokacin bayyanr Imam Mahadi (A.S) sannan sai su sake mutuwa.
Akwai wanda ya fassara raja’a da ma’anar dawowar gaskiya da karfinta da ikonta ta hannun imam Mahadi (A.S) Kuma yana ganin al’amarin bai shafi rayar da matattu ba da komowar mutane duniya ba.
Ra’ayi na farko shi ne wanda ya shahara a gun imamiyya riko da wannan daga abin da ya zo daga Ahlul baiti (A.S) musamman a lokacin Saduk, da shaihul Mufid, da Sayyid Murtada, da Shaikh Tusi, da Allama majlisi, da Hurrul amili, da sauran malamai na wanan zamani.
2- Matsayin Akidar Raja’a
Sanannen abu shi ne cewa akidar musulunci tana da usul da aka yi ittifaki a kansu da kuma furu’a da ana samun sabani a cikinta ta wata fuska. Raja’a ba ta cikin wadannan usul da ba a saba a kansu ba, hakika Shaikh Muhammad Husaini Aali Kashiful gidaa ya kyautata a bayaninsa yayin da ya ce: “Lizimtar imani da Raja’a a mazhabin Ahlul baiti (A.S) ba dole ba ne, kuma musunta ba ya cutarwa duk da tana cikin larurai gunsu, sai dai samuwar shi’anci da rashinsa bai damfaru da ita ba, ita wata abu ce daga abubuwan da suka shafi alamomin tashin kiyama kamar saukar Isa (A.S) daga sama, da bayayyanar Dujal, da bayyanar Sufyani, da sauransu[3].
Raja’a da wannan ma’ana wani bangare ne da yake kammala fikirar bayyanar Mahadi (A.S) a musulunci, saboda haka ne ma zaka gan su suna tarayya a ma’ana daya, wanda yake shi ne taimakon adalci da kuma rushe barna a karshen duniya, wanda yake nuna cewa tsarin duniya zai fuskanta zuwa ga gaskiya, Idan addinan sama na Allah sun yi imani da bayyanar sashen annabawa, kuma musulmi Shi'a da Sunna sun yi imani da bayyanar Mahadi, ba abin da zai hana imani da Raja’a a matsayinta na mai karfafa wa ga zuwan Mahadi (A.S).
Da haka ne muke cewa, Raja’a tana zuwa ne a matsayin mai kammala wa ga asalin fikirar bayyanar Mahadi (A.S) wacce dukkan musulmi suka yi imani da ita, idan wannan abu ne da aka yi ittifaki tsakanin musulmi a cikinsa, to karfafa wannan asasi da kuma zurfafa wa cikinsa hade da kuma abin da littafi da sunna suka zo da shi na karfafawar yana matsayin fifiko ne da yake cancantar girmama, tare da haka Raja’a kamar yadda Sayyid Muhsin Amini Amili yake cewa ne: “Ita al’amari ne da aka rawaito, idan hadisi ya inganta wajibi ne yin imani da ita, in ba haka ba, imani da ita ba wajibi ba ne” [4].
Don haka ne muka samu wasu daga malaman imamiyya wadanda ma’anar wadannan hadisai ba ta bayyana garesu da ma’anar da ya yi daidai da Raja’a ba, sun fassara su da wata ma’ana da ba ta yi daidai da ma’anar dawowa duniya bayan mutuwa ba, sai suka tafi a kan ma’anar dawowar gaskiya da adalci da kuma rushewar zalunci da dagawa[5].
3- Dalilai A kan Tabbatar Akidar Raja’a
Tabbatar da Raja’a yana bin marhaloli uku ne:
A- Marhalar tabbatar da yiwuwar Raja’a ko mustahilancinta.
Mafififcin abin da ake la’akari da shi a nan game da ita shi ne Raja’a nau’in dawowa ne ba bambanci, sai dai shi dawowa ne a duniya a karshen zamani ga wasu mutane da suke jagororin kafirci da kuma jagororin imani amma komowa ranar lahira ta shafi kowane mutum ne, saboda haka duk abin da za a iya zuwa da shi a matsayin dalili a kan yiwuwar alkiyama yana iya zama dalili a kan yiyuwar Raja’a, saboda haka a marhalar dalili na hankali abu guda ne ba bambanci, don haka wadancan dalilai sun wadatar.
B- Marhalar rashin karo da juna na wannan akida da kuma sauran akidu na musulunci, domin idan ta kasance zata yiwuwa, amma shin imani da ita zai ci karo da wasu akidu na musulunci ko kuma zai raunana wani bangare na akidar msulmi ko kuwa?
Amsa ga wannan: Akidar Raja’a tana da hanya biyu da aka tabbatar da ita:
A- Akidar Raja’a ba ta karo da wata akida daga akidun musulunci, kai tana ma karfafawa ne ga usuluddin guda biyar, ita tana nuna bayyanar karfin Allah ne (S.W.T) maras iyaka, da kuma adalcin tafarkin annabawa, da kuma samuwar imami, da karfafa faruwar tashin kiyama.
B- Wannan akida ta faru a al’ummu da suka gabata kamar yadda kur’ani yake kawo wa wanda yake nuna wa cewa akidar Raja’a ba wani abu ba ne da yake karo da akidar musulunci, kai yana ma lizimtarsa ne, domin kur’ani mai girma ba ya magana da abin da yake kore tauhidi, kai yana ma kawo abin da yake karfafa shi ne, bai kuma tsayu da kawo ta ba kawai sai da ya maimaita wannan ishara da yake nuna karfafawa gareta, wanda daya daga cikin misalai shi ne abin da ya zo a surar bakara da muke karantawa a fadinsa: “Shin ba ka ga wadannan da suka fita daga gidajensu ba suna dubunnai domin tsoron mutuwa sai Allah ya ce da su ku mutu sannan ya raya su, lallai Allah ma’abocin falala ne ga mutane sai dai mafi yawancin mutane ba su godewa” [6].
Masu fassara sun rawaito, daga cikin su akwai Ibn Jarir Tabari, ruwayoyi masu yawa daga Ibn Abbas da Wahab Dan Munbah da Mujahid, da Saddi, da Ata’a, cewa wannan aya ta sauka ne game da wasu mutane daga Bani Isra’il da suka gudu daga annoba da ya faru a alkaryarsu sai Allah ya dauke rayukansu, sai annabinsu mai suna “Hazkil” ya tsaya yana mai tunanin al’amarinsu, ga jikinsu ya rididdige, sai Allah ya yi masa wahayi cewa; Shin kana son in nuna maka yanda zan raya su? Sai Allah ya raya masa su, haka nan Suyudi ya rawaito kwatankwacin hakan[7].
Haka nan muke karanta fadin Allah (S.W.T) yan cewa: “Yayin da kuka ce ya Musa ba zamu yi imani da kai ba har sai ka nuna mana Allah a fili sai tsawa ta rike ku kuna kallo, sannan sai muka tayar da ku bayan mutuwarku domin ku gode” [8]. A cikin wannan masana tafsiri wanda Tabari yana cikinsu da cewa sun mutu gaba daya bayan wannan magana da suka fadda sai Musa (A.S) ya kafu yana mai rokon Allah, sai ya dawo musu da rayukansu[9].
Haka nan fadinsa: “Ko kamar wanda ya wuce wata alkarya alhalin tana mayofinciya a kan rassanta, sai ya ce: Yaya Allah zai rayar da wannan bayan mutuwarta, sai Allah ya dauki ransa tsawon shekara dari sannan sai ya tayar da shi, sai ya ce: Tsawon lokaci nawa ka dauka (a hakan) sai ya ce: Na dauki wuni daya ko sashen wuni, sai ya ce da shi: Ka zauna shekara dari ne, duba ka ga abincinka, da abin shanka basu canja ba, duba jakinka, kuma domin mu sanya ka aya ga mutane, kuma ka duba zuwa ga kasusuwa yanda muke motsa (karfafa) su, sannan sai mu tufatar da su da nama, yayin da ta bayyana gareshi sai ya ce: na san hakika Allah mai iko ne a kan komai” [10].
Masu tafsiri a cikin su akwai Tabari sun ambaci wasu daga wasu ruwayoyi da suke nuna cewa Uzair da Armiya sun wuce Baitil mukaddas bayan Bukhtanasar ya rusa ta, sai Allah ya nuna masa ikonsa a kan haka ta hanyar buga masa misali a kansa kamar yadda aya ta bayar da labari[11].
Akwai kuma ayoyi da yawa da suke nuna tabbatar dawowa bayan mutuwa idan Allah ya so ga mutum ko dabba, daga ciki akwai ayoyi kamar haka:
Fadinsa madaukakin saraki: “Sai muka ce: Ku dake shi da sashenta, haka nan Allah yake rayar da matacce kuma yake nuna muku ayoyinsa ko kwa hankalta” [12].
Fadinsa madaukakin saraki: “Yayin da Ibrahim ya ce: Ya Ubangiji! Ka nuna mini yadda kake rayar da matattu, sai ya ce: Shin ba ka yi imani ba ne? Sai ya ce: A’a, sai domin zuciya ta ta natsu, sai ya ce: Ka dauki hudu daga tsuntsaye ka karkatar da su zuwa gareka, ka yanka su, sannan sai ka sanya yanki daga kowanensu a kan kowane dutse, sannan sai ka kira su zasu zo maka suna masu gaggawa, ka sani Allah mabuwayi ne mai hikima” [13].
Fadinsa madaukaki: “Ban ce da su komai ba sai abin da ka umarce ni da shi na ku bauta wa Allah ubangijina ubangijinku, kuma na kasance shaida a kansu matukar da na kasance a cikinsu, amma yayin da ka dauki raina kai ne mai kula da su kuma kai mahalarci ne a kan komai”.
Fadinsa madaukaki: “Yayin da Allah ya ce: Ya Isa! Ni mai cika maka ne kuma mai daukaka ka zuwa gareni, mai tsarkake ka daga wadanda suka kafirta, mai sanya wadanda suka bi ka saman wadanda suka kafirta zuwa ranar alkiyama, sannan zuwa gareni ne makomarku sai in yi hukunci tsakaninku cikin abin da kuka kasance kuna sabawa” [14].
Daga dukkan wannan zamu ga cewa kur’ani ya karfafa a kan wanann bayani karfafawa mai yawa ba sau daya ba, a kuma yanayin bayanai masu yawa da yake kawowa game da al’ummar da ta gabata, al’amarin da ba makawa ya zama akwai wani hadafi da kur’ani yake son ya cimma ta hakan, kuma ba makawa wannan yana komawa ga al’amarin tauhidi ne da akida da kuma karfafa[15].
C- Marhalar tabbatar da faruwar Raja’a a nan gaba a cikin wannan al’umma ta mu, domin yiwuwar faruwar abu wani abu ne daban, haka nan faruwarsa wani abu ne daban.
Shin kur’ani mai girma da sunnar annabi (S.A.W) sun zo da wani abu da yake nuna cewa al’ummar musulmi zata samu Raja’a a nan gaba?
Muminai suna amsawa game da Raja’a da na’am zata faru a nan gaba da kuma tabbatarwa yanke, suna masu dogaro da wannan aya ta kur’ani mai girma da hadisan Annabi (S.A.W) madaukaka:
1- Fadin Allah madaukaki: “Ranar da zamu tayar da wani gungu na jama’a daga kowace al’umma, daga cikin wadanda suke karyata ayoyinmu, ana kokkora su” [16].
Wannan aya tana magana a game da wani tashin da zai kasance ga wasu sashen mutane kuma irin wannan tashin ba yadda za a yi ya kasance a ranar kiyama domin tashin kiyama ya shafi dukkan mutane ne, to menene ma’anar kebance shi da wasu sashen mutane wanda Kur’ani yake ambaton wasu ayoyi guda uku daga ayoyin tashin kiyama da fadinsa: “Ranar da za a yi busa a kaho sai duk wanda yake sama da kasa ya firgita sai wanda Allah ya so. Da kuma dukkansu masu zo masa ne gaba daya”. Alamomin Alkiyama a bayyane suke a wannan aya amma banda waccen ayar, da ayar da ta gabata tana maganar alkiyama ne da ya zama maimaitawa maras ma’ana.
2- Fadinsa madaukaki: “Yaya zaku kafirce wa Allah, alhalin kun kasance rasassu sai ya rayar da ku sannan yake dauke ranku, sannan yake rayar da ku sannan zuwa gareshi ne kuke komawa” [17]. Abin nufi a nan Allah ya ambaci rayuwa biyu ga mutum da komawa biyu, rayuwar farko ta duniya, rayuwa ta biyu tana tsakanin rayuwar farko da kuma komawa zuwa gareshi, kuma ba zata yiwu ba in ba raja’a ba.
3- Fadinsa madaukakin saraki: “Ya ubangiji ka rasar da mu sau biyu ka kuma rayar da mu sau biyu mun yi furuci da zunubanmu shin akwai wata mafita” [18]. A nan zamu ga kashewa ba ta kasancewa sai ga wanda da ya kasance yana da rayuwa, shi ya sa ya ce: “ ka rasar da mu sau biyu”. Wato rasarwa biyu bayan rayarwa biyu, rasarwa ta farko sananniya ce domin ita ce take biyo wa bayan rayuwarsu da aka sani, amma mecece rasarwa ta biyu idan ba su samu wata rayuwa ta biyu ba, sannan sai bayanta su koma zuwa ga mutuwa sai ya zama suna da rayuwa biyu da rasuwa biyu kamar yadda ya zo.
Masu sabawa da wannan mahanga sun kawo wasu tawiloli ga wannan aya da ba yadda za a yi su zama daidai: Wasunsu suka ce: Ma’anar wannan shi ne; Allah yana halittar matattu kafin rayuwa!. Wannan kuwa batacce ne a fili ba zai yi daidai da lugga a larabci ba, domin wanda Allah ya halicce shi matacce ba a cewa ya rasar da shi.
Wasu suka ce: Mutuwa ta biyu zata zama bayan rayuwarsu ta kabari domin a tambaye su!. Wannan ma batacce ne ta wata fuska domin rayuwa ba ta zama domin takalifi ba ballantana mutum ya yi nadama a kan abin da ya kubuce masa a cikinta, ayar kuma tana nuna mana nadamar wadannan ne a game da abin da ya kubuce musu na rayuwa biyu, ashe kenan ba rayuwar tambaya ba ce[19].
Wannan su ne wasu daga cikin dalilai a game da Raja’a, kuma akwai adadi mai yawa na hadisai daga annabi (S.A.W) da Ahlin gidansa ma’asumai (A.S) da aka rawaito da suke tabbatar da Raja’a da masu ruwayar hadisai na imamiyya da malaman tafsiransu suka rawaito shi a littattafansu da suka shafi wannan maudu’i[20].
Wannan kadan kenan daga cikin abin da yake nuna aukuwar Raja’a a karshen zamani kuma duk yadda aka juya Raja’a akida ce karbabbiya kuma mai musu sai ya kawo dalilai, yana ma iya musu ba dalilai sai dai wannan kuma ba karbabbe ba ne domin musun wani abu yana bukatar dalilai.
3. Asalusshi’a Wa Usuliha: 35.
4. Nakdul Washi’a: 376.
5. Majma’al Bayan: 7\366 Tafsirin Aya 83 Ta Surar Namli.
6. Bakara: 243.
7. Tafsirin Tabari: 2\586-588.
8. Bakara: 55-56.
9. Tafsirin Tabari 1\290-293.
10. Bakara: 259.
11. Tafsirin Tabari: 3\28-47.
12. Bakara: 73.
13. Bakara: 260.
14. Ali Imran: 55.
15. Ma’ida: 117.
16. Naml: 83.
17. Bakara: 28.
18. Mumin: 11.
19. Masa’ilus Sirriwiyya: 33.
20. Malamai da yawa sun wallafa littattafai kusan arba’in game da Raja’a.
21. Siran Nabawiyya Ibn Hisham: 4\305. Da Dabakatul Kubra Na Ibn Sa’ad: 2\266.
22. Abdulhusaini Amini ya kawo bayanai da suke nuna wuce gona da iri na malaman koyarwar halifofi a juzu’i na sha daya na littafinsa na gadir, daga cikinsu akwai labarai da suke dauke da ma’anar raja’a.
23. Tahzibut Tahzib: 3\410.
No comments:
Post a Comment