Monday, 26 May 2014

"_TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)_"


___________________(11)__________________

TAMABAYA: Ko akwai fifiko tsakanin 'yan uwa masu gwagwarmaya na kauye da na birni?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ayyukan ibada, Allah (T) yana ba da sakamakonsu ba ya la'akari da cewa ko kai bakauye ne ko kai babirne ne. Aikin da ka yi ne za ka sami lada.

Wala'alla kila wani aikin ya zama ya fi lada in an yi shi a kauye fiye da birni, wani kuma tana iya yiwuwa ya zama in an yi shi a birni ya fi lada fiye da a kauye. Ya danganta da aikin ne. Amma ladan ba shi da dangantaka da kauye ko da birni.

Aikin ake la'akari da shi, ba wai mutum ina ya yi aikin ba.

___________________(12)__________________

TAMBAYA: Shin ya halasta dan uwa ya rikayin wasan nan na SNOOKER?

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai wasan Snooker, ba wani abin da aka sani dangane da haramci a kansa. Kuma kamar yadda na sha nanatawa, abin da ba a hana ka ba, to, shi kenan ka na iya yi, sai dai idan ya shiga eriyar da za a ce masa wargi, 'Lagawu,' banzantar da lokaci, to, shi kuma ya san wannan.

Kowanne irin wasa yana iya fita haddin da ya halatta, ko da ma halas din ne. Wato in ya zama ya kai ma yana cinye lokaci da kuma shagalta da shi koma bayan ayyukan kirki.

____________________(13)_________________

TAMBAYA:Shin mutum zai iya cin yankan arnan kasar nan, kuma zai iya cin abincinsu, tun da ana ce da su Ahlul kitabi?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ban san abin da yake nufi da arnan kasar nan ba, domin kalmar arna ba kalma ce ta addini ba. In yana nufin kiristoci ne, to sai mu ce, mu a tamu fahimtar, ko da aka halatta mana cin abincin Ahlul kitabi, ba a halatta mana cin yankan su ba. Kodayake akwai sabanin ra'ayi a wadansu mazhabobi.

Wasu na ganin cewa abin da suka yanka na abin da ya halasta masu su su ci, to, mu ma muna iya ci. Amma sun yanka domin su su ci ne, ba domin mu mu ci ba.
Amma mu a fahimtarmu lallai wannan din ma bai halatta ba. Sai dai abincinsu da ya halatta a wajenmu, sune abin da bai shafi yanka ba, kamar kwaya (tsaba),
ko 'ya'yan itatuwa, ko wani abin da ya yi kama da haka nan. Amma ba abin da suka yanka ba, ko da ya halatta mana ya halatta masu. Ballantana ma akasin haka.

No comments:

Post a Comment