____'Yusuf Ikara......................?'____
*** YA SUBHANALLAH!!! ***
Nayi zaton a matsayin 'Yan Izala na masu karatu, za su ma 'Dan'uwansu "Yusuf Ikara" raddi akan rashin hankalin da ya tabka na cewa:
"Don (Nana Fatima) tayi fushi da sayyadina Abubakar, har ta mutu bata magana da sayyadina Abubakar ko umar, BA WANI ABU BANE, nana fatima ba_ta_da wuta, bata da ALjannah.... "
Amma abin takaici sai naga a comment din su a cikin wannan post din na 'Sister Zainab', suna ta kokarin tabbatar da cewa ya yi daidai ne. Kuma ma suna kokarin nuna mana haka Fahimtarsu (Aqidarsu) yake akan Sayyida Fatima (SA).
Na'am, a cikin maganar nasa, yace:
" Nana fatima ita ba Allah bace, kuma ita ba annabiya bace, ita baiwa ce daga bayin ALLAH."
EH! HAKA NE! ITA BA ALLAH BACE! BA KUMA ANNABIYA BACE! DAGASKE ITA BAIWAR ALLAH CE DAGA CIKIN BAYIN ALLAH! AMMA TAFI DUK BAYIN ALLAH GIRMAN DARAJA IN BANDA MUTUM 2!
Amma cewar 'Yusuf Ikara' akan Sayyida Fatima Azzahara (SA):
"Don tayi fushi da sayyadina Abubakar, har ta mutu bata magana da sayyadina Abubakar ko umar, BA WANI ABU BANE, nana fatima ba_ta_da wuta, bata da ALjannah.... "
SAI MUCE MASA, IN HAR DAGASKE NE BAI SANI BA, TO YA KAMATA YA KIYAYI FADA MA SAYYIDA ZAHARA (S) HAKA! YAJE YA NEMI SANIN KO WACECE ITA!
Sayyida Fatima (SA) tafi karfin tayi fushi da wani ace kuma BA WANI ABU BANE! Wallahil Azeem mutum ya ma kansa karya!
1- Hakim ya fitar da Hadisi a cikin Mustadraku dinsa, J-3, shafi na 153 ('Dab'in; Haidar Abad) Manzon Allah (S) yana cewa:
"LALLAI ALLAH YANA YARDA DA YARDAR FATIMA (BINTU MUHAMMAD (S)."
* Yanzu 'Yusuf Ikara' Ya Amsa cewa Fatima ta mutu tana fushi da Abubakar da Umar, ya kuma ce ba komai! Shin Fushi ba Kishiyar Yarda bane!
Me kake so kace ma Duniya kenan? Kana son kace ma Musulmin Duniya Annabi Muhammad (S) da ya fadi hakan ya yi Karya ne? Ko kuwa Hakim da ya ruwaito kuma ya inganta Hadisin Makaryaci ne shi a wajen 'Yan Izala?
2- Duba Littafin Kasa'isul Kubra na Siyudi, Juzu'I na 2, shafi na 220 (bugun Haidar Abad). A ciki ya kawo Hadisi daga Manzon Allah (S) cewa:
"FARKON WANDA ZAI FARA SHIGA ALJANNA ITACE FATIMA (RA)."
* Muna mika tambaya izuwa gareka ya kai Yusuf! Zai yiwu Masu Fushi da junansu dukkansu su shiga Aljannar Allah???
Ko kuwa wannan katoton Malamin Ahlus-Sunnah din (Imamu Siyudi) ya shantaka ma Annabi (S) Karya ne!? Dama Malaman Sunnah Makaryata ne su a wajen 'Yan Izala?
3- Ibn Hajar (Daya daga manyan Malaman Sunnah) ya fitar da Hadisi daga Annabi (S) a cikin littafinsa 'Sawa'ik al-Muhrika' da Siyudi a cikin 'Dur-al Mansur' cewa:
"BIYAYYA DA KYAUTATAWA DA SOYAYYAR FATIMA (RA) YA WAJJABA AKAN AL'UMMAR MUSULMI."
* Shin Shi Abubakar da Umar ba Musulmi bane su a wajen 'Yan Izala? Me sukai ma Fatima tayi Fushi da Su din? Ashe ba saba mata sukai ba? To zai taba yiwuwa a wajabta maka son mutum, kuma mutum din ya mutu da Fushinka, kuma ya zama BA WANI ABU BA!!!??
4- Muslim a cikin Sahihin Littafinsa, Juzu'I na 7, shafi na 140, ya kawo Hadisi daga Annabi (S) dake cewa:
"FATIMA (RA) TSOKAR JIKINA CE, ABIN DA YA SAMETA YANA SAMUNA, KUMA ABIN DA YA CUTAR DA ITA YANA CUTAR DA NI"
* Billahi alaik! 'Yusuf Ikara', Shin abin da Abubakar da Umar suka samar ma Fatima (RA) na bakin ciki har tayi fushi da su a bayan wafatin Babanta (S) har kuma ta yi Shahada tana mai fushi da bakin cikin cutarwar da sukai mata, bai sami Manzon Allah (S) ba?
Ashe wani zai cutar da Annabi (S) ya zama BA KOMAI BA!? Ko Muslim ya shantaka ma Annabi karya a sahihinsa ne kake son kace mana? Ashe Imamu Muslim makaryaci ne a wajen 'Yan Izala???
5- Ibn Hajar har wala yau ya kawo a Sawa'ik al-Muhrika din nasa, a shafi na 230 (bugun Abdulladiyf -Masar), Annabi (S) yana cewa:
"FATIMA TSOKAR JIKINA CE, ABIN DA DUK YA FARANTA MATA YANA FARANTA MIN."
* Ina gama 'Yusuf Ikara' da Allah! Ashe a cikin ruwayar da Fatima ta fada ga Abubakar a Sahihin Bukhari bata ce, hakika kun bata min rai ba? Kun yanke farin cikina?
Dan Allah wacce faranta ranta faranta ran Manzon Allah (s) ne, shin wani zai bakanta mata rai ya zama BA KOMAI BA!!!?
6- To gashi ma baro-baro a cikin littafin Sunanil Kubura na Allama Baihaki (Dab'in Haidar Abad), Juzu'I na 10, shafi na 201, Manzon Allah (S) yana cewa:
"FATIMA TSOKAR JIKINA CE, DUK WANDA YA FUSATA TA HAKIKA YA FUSATANI."
* Dan Allah baka ji kunyar cewa "DAN FATIMA TA MUTU TANA FUSHI DA ABUBAKAR DA UMAR BA KOMAI BANE" ba!?
Ka karyata Annabi (S) kenan, saboda soyayyarka ga Abubakar da Umar!??
Mun shiga 3 da wannan bala'in na Izala!!! Yusuf babanka Abubakar Imam Ikara ance fa Malami ne, ya akai kai bakai karatu ba wai???
NAJI WANI MARE KUNYA, WAWA, DOLO, SAKARAI, SHASHA-SHA! YANA CEWA FATIMA (SA) BA KOWA BACE! MUTUM CE KAMAR SAURAN MUTANE, MACE CE KAMAR SAURAN MATA
Inna lillahi wa Inna ilaihir Raji'un!
In dai haka ne Izala. Allah ya kiyaye mu da sharrin IZALA wallahi. Tir da ita! Tirrrr wallahi!
* Ashe ba Imamu Nasa'I ne ya kawo Hadisin Annabi (S) a cikin 'Al-Kasa'is' din sa, shafi na 34 (bugun Masar) cewa;
"FATIMA (RA) CE SHUGABAN DUKKAN MATAN TALIKAI"
Ba?
Ashe Shugaba na daya da mabiyansa? Sonka da Nana A'isha 'Yar Abubakar yakai kace Fatima 'Yar Muhammad (S) kuma Tsokar JikinSa (S) ba komai bace ita ba kuma kowa ba???
WAI DAN ALLAH ME MANZON ALLAH (S) YA MA 'YAN IZALA NE DA SUKA TSANE SHI, SUKA KUMA TSANI ZURIYARSA???
- Dan Allah Kuba mu Amsa!?
No comments:
Post a Comment