Wednesday, 28 May 2014

HAKKIN HANNU



Haqqin Hannu
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma haqqin hannunka shi ne kada ka shimfixa ta kan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -qiyama- da wannan shimfixawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya-. Sannan kada ka riqe ta daga abin da Allah ya wajabta mata, sai dai ka kiyaye ta da riqe ta daga mafi yawan abin da bai halatta gareta ba, da shimfixa ta zuwa ga mafi yawan abin da bai zama wajibi a kanta ba, sai ta kasance ta yi hankali, ta xaukaka a wannan gida -duniya-, sannan lada kyakkyawa ya wajaba gareta daga Allah a gidan gobe -lahira-".

Shimfixa hannu da aka hana daga dukkan wani abu da bai halatta ba shi ne sanya hannu domin xauka ko karvar duk wani abu da bai halatta ba. Idan mutum ya xauki wani abu da ba nasa ba, alhalin babu izinin mai shi, ko ya bayar da wani abu da ba nasa ba wanda ba shi da haqqi a kansa, to ya shimfixa hannunsa inda bai halatta ba. Sannan sai Imam (a.s) ya yi nuni da cewa sakamakon hakan shi ne mutum ya faxa cikin fushin Allah a ranar qiyama, sannan kuma ya samu suka da zargin mutane a ranar lahira.
Kamar yadda shimfixa hannu zuwa ga abin da bai halatta ba yake laifi haka ma riqe hannu daga aikta abin da yake wajibi yake laifi. Akasin haka kuma kamar yadda shimfixa hannu zuwa ga abin da yake wajibi yake tilas, haka na riqe hannun daga abin da yake haram ne yake wajibi. Sava wa duka wannan lamurran biyu yana iya kai mutum ga azabar Allah maxaukaki a ranar qiyama, kuma mutane su zarge shi da muzantawa a wannan gida na duniya.
Sannan ba a son mutum ya yi duk abin da ya ga dama ko da halal ne, an fi so ya tsaqaita a rayuwarsa, shi bai bai taqaita ba, shi kuma bai yawaita da shige gona da iri ba. Sau da yawa shugabannin tarbiyyar kai suka taqaita da abin da yake wadatar da su a rayuwa koda kuwa suna da yalwa.

Hannun a harshen larabci yana da ma'anoni masu yawa da wasu daga ciki an yi amfani da su a ayoyin Kur'ani mai daraja, yana da ma'anar qarfi kamar a cikin faxinsa maxaukaki "Ka ambaci bawanmu Dawud ma'abocin qarfi…" . Kuma ta zo da ma'anar ni'ima a faxinsa "… sai dai hannayensa shimfixaxxu ne yana ciyarwa yadda ya so…", Surar Ma'ida: 64. A hausa bahaushe yakan ce: "Wane yana da sakin hannu", idan yana da kyauta da baiwa ga mutane.
Amma a wannan ayar ma yana iya zama da ma'anar iko da qarfi da qudura ne yahudawa suka ce: "Hannun Allah yana da ququmi…" Surar Ma'ida: 64, saboda abin da suke nufi a nan shi ne cewar; Allah ya riga ya saukar da hukuncin shari'a, kuma ba zai iya shafe shi ya kawo wani ba. Da wannan ne ya shahara gun yahudawa cewa suna inkarin masu shafewa da ababan shafewa na daga ayoyin Kur'ani "Nasihu da Mansuh".
A xaya vangaren kuma yana koma wa zuwa ga musun "Canja qaddarar Allah" da aka fi sani da "Bada" da larabci. Sai Allah ya yi musu da raddi cewa yana iya shafe hukuncin shari'a ya zo da wani, hannunsa ba shi da ququmi a kan hakan, kuma yana iya canja abin da ya qaddara kan mutane ko wani mutum ya sauya musu da wata qaddarar daban, don haka hannunsa ba shi da ququmi a buxe yake.
Sannan a nan zamu so mu yi nuni da wasu abubuwa biyu da suka shafi "Dokar hannu", da kuma "Dokar ya hau kan hannu". Dokar hannu ita ce qa'idan nan mai cewa duk wani abu da aka samu a hannun wani mutum to yana nuna nasa ne, don haka idan zai sayar ko zai bayar kyauta za a iya karva a yi amfani da shi sai dai idan akwai wani dalili na musamman da ya tabbatar da cewa ba nasa ba ne. Wannan doka ta zo a cikin littattafai masu yawa kamar; Wasa'il, j 17, s 525, babi 8, h 4.

Amma "Dokar ya hau kan hannu" ita kuma doka ce wacce take wajbta girmama dukiyoyin mutane, tana mai cewa duk wanda ya lalata dukiyar wani to dole ne ya biya. Kamar wanda ya yi qwace, ko ya yi sata, ko ya yi sakaci da dukiyar wasu, da sauransu duk waxannan ya hau kansu ne su biya. Akwai ruwayoyi masu yawa da suke nuni da wannan kamar: mustadrak, j 3, babin qwace, s 145-6. da Sunan Ibn majah: j 2, s 802. Da yake ba muna maganar fiqihu ne ba don haka muka taqaita da waxannan taqaitattun kalamai.
Hannu wani abu ne da ake yin amfani da shi wurin duka a qasashenmu, sau da yawa masu qarfi ko iko kamar a hanya da titina, ko kuma 'yan sanda, ko kuma malamai da xaliban manyan aji sukan yi amfani da hannunsu ko wani abu da suke xauke da shi domin dukan wasu. Yana da kyau mu sani babu wani wuri da addinin musulunci mai tsari ya yarda wani ya doke wani, idan kuwa ya doke shi a bisa qa'ida sai ya biya diyyar duka, kuma idan wurin ya tashi kamar ya yi ja, ko baqi, duk akwai diyya.
Duka ba ya halatta sai ga mace mai qin mijinta a mataki na uku bayan matakai biyu na wa'azi da qauracewa a kwanciya. Sai kuma ga yara da iyayensa musamman uba zai ladabtar da shi domin gyaran halinsa ba don huce haushi ba, ko kuma bawa da ubangijinsa zai iya dukansa don gyaran halinsa. Amma dukan malami ga yara xalibansa don ladabtarwa yana buqatar izinin uba ko shugaban daular musulunci idan akwai shi.

Sannan duk inda aka yarda da duka don ladabtarwa ba a son ya wuce sau biyar, imma dai sau xaya, ko biyu, ko uku, amma tsanantawa ga yaro shi ne sau shida, shi ma da waxancan dokoki da muka ambata. Haka nan ladabtar da bawa ba a son ya wuce sau biyar idan za a doke shi, da sauran hukunce-hukuncen duka.
Magana kan duka tana buqatar babban littafi ne, sai dai wanda yake son ya samu wasu qarin bayanai yana iya duba littafin: Durrul Mandhud, na Gulpaigani: mas'ala ta huxu game da dukan yara, s 181, da sauran littattafai.
Haka nan hannu wani abu ne da ake amfani da shi domin nuna wani abu, ko sanya wata alama, ko nuna musiba, sai dai game da musiba an hana dukan fuska da kai da sauran jiki ko yakushinsa yayin musiba, kamar yadda aka hana faxin kalmomin da ba su dace ba.

No comments:

Post a Comment