Monday, 26 May 2014

"_TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)


____________________(4)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Menene hukuncin tuka mota ga matar aure?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ba wani abin da aka samu dangane da wannan. Sawa'un matar aure ce ko wadda ba ta yi aure ba, wadda ba ta da miji. Saboda haka, a shari'a kuwa, asalin komai shi ne halasci sai in haramci ya zo. Kuma abin da ba a haramta maka ba, ya halatta.

Saboda haka in dai hukunci ne, to, sai mu ce halas ne, matar aure ko ba matar aure ba, babu bambanci a nan. Mace in tana da aure ko ba ta da aure dangane da tukin mota.

_____________________(5)__________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina hukuncin wanda ya shafi zakarinsa alhali yana da alwala?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ba wani abin da ya hau kansa. A Malikiyya an ce alwalarsa ta baci, dogaro bisa wata riwaya wacce aka ce, wani cikin magabata yana ma wani shiftar Alkur'ani, sai ya ga ya yi susa, sai ya ce, "ko ka taba al'aurarka?" Ya ce eh! Sai Malamin ya ce masa, "tashi ka yi alwala." A kan wannan ne.

Kuma wanda su Malikiyyar ne kawai koma bayan sauran Mazhabobi suke da wannan ra'ayin, duk sauran mazhabobi ba su da wannan ra'ayin. To, shi ma a Malikiyan in muka koma, za a ga cewa shi kansa wannan riwaya din, muna iya cewa, wannan wurin, babu inda aka ji shi.

Duk sauran mazhabobi ba su san da hadisin ba, ba su kuma san daga ina aka samo shi ba. Saboda haka abin da za mu iya cewa shi ne, a Malikiyya suna cewa haka nan, kodayake shi ma ba dogaro bisa wani hujja kakkarfa ba. Amma sauran mazhabobin Musulunci ba su san da haka nan ba.

____________________(6)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Dan uwa ne yake aiki a Hukumar wutar lantarki ta kasa NEPA, sai aka ajiye shi a fannin yanke wuta. Shin idan ya yanke wutar wadanda ba su biya ba, ya yi zunubi?

Kuma wani lokaci idan mun yanke wutar, akan bi mu a ba mu wasu 'yan kudi don mu mayar masu da wutar tasu.

Shin muna iya mu mayar. Kuma idan da ma mun taba cin irin wannan kudin, to, menene matsayinsu?

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai aiki kamar yadda aka sani yana da ka'ida. Saboda haka su ma'aikatar da suka dauke ka aiki, da ma suna da ka'idojinsu, kuma a kan wadannan ka'idojin ne suka dauke ka aiki. In ka ga abin da ya saba wa shari'a a ka'idojin nasu, to, da ma tun farko ba za ka yi aikin ba.

Kuma idan yana ganin shi a fahimtarsa bai kamata a je a yanke wa mutane wutar lantarki ba, saboda zalunci, to tun farko ba zai yi aikin bane, saboda su abin da suke yi kenan.

Na'am, muna iya cewa, na farko dai, ba shi mai yanke wutar ba, ita NEPA din, ya kamata a ce ta yanke wutar lantarkin mutane? Sai mu ce lalle bai kamata ba. Ta wata fuskar ma ana iya cewa bai halatta ba, ganin cewa da wuta da ruwa, duk hakkoki ne na al'umma. Kuma a wannan lokaci namu, duk al'ummomin duniya suna samar wa al'ummunsu da wadannan a cikin kudade saukaka.

Wanda sauran al'ummu ba za taba sawwala cewa za a iya zuwa a yanke masu ba. Sai dai ta yiwu ita Hukuma din ta san su mutane mabukata ne ga wadannan abubuwa, ruwa da wuta sai ta sami hanyar da ta bi wajen karbar kudinta daga wajensu, amma ba ta hanyar yanke masu ba.

Saboda haka idan ya zama ka'idar aikin da ma ya ga ya saba, kuma ba zai yi ba, zai bar aikin ne. Sannan kuma kudaden da suke karba (su ma'aikatan), shi ma zai kasance yana da matsayi a ka'idar aikin nasu ai. Idan sun karbi kudin da ma wa suke ba? Suna mayarwa ne cikin aljihun NEPA, ko kuwa aljihunansu?

Idan aljihun NEPA ne, to, shike nan in zalunci ne, ya taimaka masu wajen zaluntar al'uuma, idan kuma aljihunsu suke zubawa, to, sai a tambaye su har wal yau, a bisa ka'ida da ma wadannan kudaden a aljihunansu ya kamata ya shiga? Idan eh ne, to shike nan halak malak, sai ya ci abinsa.

No comments:

Post a Comment