TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ni ne na yi alkawari zan taimaki makarantar Fudiyya da kudi Naira 200, kowane wata, amma na yi watanni 30 ban ba da ba, zan ba da rabin abin da na yi furuci da farko ne, ko zan biya gaba daya ne?
SHAIKH ZAKZAKY: Alkawari dai wajibi ne mutum ya cika shi, musamman idan ya hada shi da alwashi. Idan ya aje shi da alwashi zai zama kaffara ya hau kansa.
Amma tunda alkawari ne, za mu dauka ba tare da alwashi bane, saboda haka babu batun kaffara. Amma abin da ya hau kansa, tamkar bashi. Abin nan da ya ce zai rika biya duk wata, to ko da ya kwashe wata nawa ne bai biya ba, jimlarsa yana kansa.
__________________(122)__________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sana'ata wanki da guga, menene hukuncin kayan da masu kawo wanki suka bar ni da su? Don akwai kayan mutanen da suka shekara biyar ko sama da haka a wajena.
SHAIKH ZAKZAKY: To hukuncinsu zai koma tamkar hukuncin kayan tsintuwa, kodayake su wannan an ba shi ne amana, amma bai san wanene ya ba shi ba. Sai ya yi ta bincike, ya yi ta bincike, har sai ya gano wanene ya ba shi din.
Kuma matsawar bai gano ba, zai ta ajiyewa, tunda amana ce. Inda ya bambanta da tsintuwa kenan. Tsintuwa ba ka san mai shi ba dama, shi kuwa wannan ka san wani ya ba ka.
Saboda haka sai ka ajiye daidai gwargwadon shekara guda, idan ka tabbatar da cewa ba ka gane mai shi ba, to shi kenan kana iya sarrafa shi ta fuskar duk da ka so, amma kai ne mai lamuni.
Fuskokin ya hada da ko ka bayar sadaka, ko ka sayar ka dauki kudin ka yi sadaka da fatan ladan ya je ga shi mai kayan.
Amma duk ran da mai kayan ya zo, to lazim ne ka biya shi. Ba za ka ce ai na yi maka sadaka da shi ba.
Amma idan ya san takamaimen mai shi (wannan idan na fahimci maganar bai fahimci waye mai kayan ba),sai ya zama mai kayan ya tashi ya tafi wani wuri, to ko shekara nawa ya yi ba zai salwantar da kayan ba, zai ajiye masa, tunda ya koma tamkar hukuncin ajiya, ba na
tsintuwa ba.
Idan mutum ya ba ka ajiya, za ka yi ta ajiyarsa, sai dai in an kai ga wannan abin zai salwanta, ya lalace sakamakon ajiya, to ba za ka bar shi ya lalace ba, saboda haka sai ka sayar da shi ko ka sarrafa shi ta wata hanya don ya zama kiyayewa gare shi, kudin kuma zai zama na wannan mutumin ne. Duk lokacin da ya dawo sai ka ce masa ka bar kayanka, bayan shekara kaza muka ga alamar zai lalace, saboda haka mun sayar.
Idan kuma ya yaye masa cewa mai kayan misali ya mutu ne, to na magadansa ne. Sai ya kai wa magadan kayan.
Idan kuma ya san wadanda suke da dangantaka da mutumin, in ba shi nan ko da ma ya bace ne, yana iya kai musu.
____________________(123)________________
TAMBAYA: Akramakallahu. Menene bambanci tsakanin Mahr da Sadak?
SHAIKH ZAKZAKY: Akwai luggogi na sadaki a Larabci, amma a Hausa ba mu da mishkila a kan wannan, saboda sadakin kawai muke ce masa. Ba ma kiran shi da wani suna, akalla a addinance.
A al'adance akwai abubuwan da suke ce masu ko dukiyar aure, kayan asin da asin, ko toshi, wadanda duk ba su a cikin ma'anar sadaki.
___________________(121)_________________

No comments:
Post a Comment