Monday, 26 May 2014

ZUWA GA IYAYE MATA MAKWADAITA

«««~||•HABAA AMMAAA.....!!!???•||~»»»

Ki tina fa, a lokacin da Burazanki ya nemeki ya aure ki bashi da ko gidan kansa, ko dakin kansa bai mallaka bama, kuma bashi da shagon kansa, yana zaune ne a karkashin wani, ko kuma idan yana sana'ar to kananun sana'a yakeyi kila misalin Dinkin takalmi, wanki da guga, yankan farce da sauransu.

Amma ya ganki yace yana sonki, kuma iyayenki basu duba rashinsa ba, suka duba mutuncinsa da kamun kansa ko rikon addininsa, da kokarinsa ga neman halas, suka aura miki shi.

Haka ki zauna a gidansa, yau a daura girki, gobe a jika gari, jibi aci nade da mai asha ruwa, Kaya (sutura) kuwa kila sai salla-salla, yakan dinka miki.

Baku da gidan kanku, kuna gidan haya ne, kullum kina kayan Hijabi a tsakar gidanki, kina daki baki tsira ba, saboda 'yan'uwan mutanen gida kan leko su gaishe ku.

Ana haka wata rana kike jin sallama ace Ina wane? kila ya shiga wanka lokacin; sai yara suce miki sunga motan 'yan sanda da Mai Unguwa suna jiransa a waje. Anzo kame. (Waki'a).

Haka zai fito a tafi da shi, ke da ganinsa sai Allah yayi, ki zauna kina maraici ke da 'yan kananun yaranku. Kila ma da ciki a tattare da ke, mijin na Kurkuku zaki haife, ayi sunan d'a ko 'yan cikin da ya bari.

Haka akai tata wannan jarabawowin, har Allah ya kawo muku budi, sannu a hankali, har yanzu ga wadannan 'ya'yan naku da akai waki'a suna kanana sun tasa. Sun girma a dai dai lokacin da mahaifinsu ya zama Babban Alhaji, ke kuma kin zama Babbar Hajiya, shi da motar hawansa, kema da taki, haka ma 'ya'yanki da nasu na zuwa makaranta.

Gaki da 'ya'ya mata reras a gabanki! Ince ko babban burin uwa ga 'yarta a yayin da ta taso shine taga aurenta?

Abin mamaki, Tsayayyen Buraza ya ganta yace yana sonta zai aureta. Haka 'Yar nan zata murtuke fuska tace Me zanyi da kai? Me zanci A Wajenka? Me kaci me naci? Ina ce wata guda kake yi a nan kana Duty. Duty zanci? Ko Charbi da Turba zamu rika ci? Je ka nemi dai dai da kai Malam!

Kaico! Abin ban mamaki, ke kuma a matsayinki na Uwarta, wacce ki karanci rayuwar duniya da duk wani nau'in kalar juyawarta (ita duniya din), abin idan ki samu labarin wannan danyen wauta da rashin hankalin da ta tafka; Sai ki kirata ki zaunar da ita ki mata nasiha, ki karanta mata rayuwar duniya.

Ki labarta mata yadda al'amarinku ya gudana tin kina budurwa har aka kai ga yanzu. Ki nuna mata arziki ba komai bane face nufin Allah Ta'ala. In yaso kayi yanzu zakayi, haka in yaso ka talauce cikin kankanin lokaci zaka neme sa ka rasa.

Amma ba haka ba; sai kawai kaga Amma ta murtuke fuska, da tazo wucewa zata shiga Husainiyya ko Filin Taro, in ta hango Brazan da yace yana son 'yarta sai tama canza hanya kar ma ya ganta, balle yaga fara'anta.

Wata kam da aka ce mata wani dan'uwa (Haris) yana son 'yarta, sai tace; "Ayya! Ina laifin ya je ya nemi dai dai da shi? Wannan ai kalar ma'aikatan Ofis ne ba kalar Sojoji bace."

Hm, Nace Madam Kenan!!! Kin mance sunan Ma'aikacin Ofis din nan DAN KWADAGO? Kin mance Haris din nan Aikin me yake yi? Duty din wa yake yi? Kin mance cewa Lahira ce Mafi alkairi da dacewa?

Ita fa 'yar nan taki bata ma san akwai Talauci bane yasa ta fadi hakan. Sai ki biye mata? Kin mance wanda ya baku lokacin da baku dashi yana iya bashi ya hanaku kuma bayan kuna da shi?

Da ban mamaki gareki a matsayinki na Uwa amma kana nan yara su fiki tinani.

Domin wata sister (budurwa) ta taba cemin; "Babban abin da yasa Sistocin da suka isa aure suke zaune a gida suka yawaita shine Kwadayin abin duniya!"

Ya Lillahi! Nace mata daga Iyayensu ko daga su? Tace daga Uwayensu mata (su Amma) da kuma su yaran. Amma babban laifin yafi karfi ga Iyaye matan. Dan komai tsayuwar uba, in Amma ta rike ragamar, sai a hankali.

Sai nace:
Anya ba wadanda suka kware a Amanci ya kamata a rika cema Amma din nan ba???

Eh Mana; Ke da ake tinanin Imani daga gareki, an rasa! Ya kuwa za'ai a samu daga 'Yarki?

Wannan yace yana son 'Yarki tace A'a! Kin tayata cewan!! Uba yayi magana kince masa: "Buraza a lura da Kufu'inta!"

Hahaha, kaji masaniyar Kufu'I ba!

Ya kuwa Burazu ba Zasu watsar da Lamarinku suje su Nemi Amawan Gari ba? Tinda Karfi da Yaji Kun zama Amawan Harka Masu Manya-Manyan Hijabai; dame Hijabi mai hawa daya, damai hawa biyu da mai uku!

Ku gwada cire kwadayi da son jin dadin duniya ku gani, yanzu wadannan tilin 'ya'yan naku da kuke jerawa ku tafi Ta'alim ko Tafsir ko Nahjul-Balaga ko sauran Programes tare; mutane suna dauka kishiyoyinku ne.

Yanzu zaku ga zun zabge a gabanku! Burazu sun diba..................

Wassalam.
Saifullahi M. Kabir Saminaka

No comments:

Post a Comment