Monday, 26 May 2014

DALILAN AIKATA BABO


Dalilan Aikata Sabo
Hakika shi mai laifi (zunubi) ba ya aikata laifin face dai sai akwai wani abu ko kuma wani yanayi da yake tunkuda shi ga aikata hakan. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Shin, to, wanda aka kawata masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yana daidai da waninsa)? Saboda haka, lalle, Allah Yana batar da wanda yake so, saboda haka kada ranka ya halaka a kansu domin bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sana'antawa". (Surar Fadir, 35:8)
Duk da cewa abin da yake aikatawa ba kome ba ne, to amma shi mutum yana mai rudin kansa da cewa abin da yake aikatawa shi ne daidai. Hakika Alkur'ani mai girma ya yi bayanin irin wadannan mujirimai:
"Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi barna a cikin kasa", su kance: "Mu masu kyautatawa kawai ne! To lalle ne su, su ne masu barna, kuma amma ba su sansancewa". (Surar Bakara, 2: 11-12)
"Ka ce, ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka? wadanda aikinsu ya bace a cikin rayuwar duniya, alhali kuma suna zaton lalle ne su, suna kyautata (abin da suke gani) aikin kwarai". (Surar Kahfi, 18: 103-104)
Hakika, shi mutum a koda yaushe yana neman mafaka ce ga abubuwan da yake aikatawa domin ita fidiran dan'Adam ba ta kaunar mummunan abu. A dalilin haka ne ma, babu yadda za a yi ya yarda cewa abin da yake aikatawa ba daidai ba ne face ma har ya gano munin aikin nasa. Duk kuwa da cewa fidiran dan'Adam ba ta kaunar mummunan aiki, duk kuwa da cewa mummunan ayyukan suna nan, to amma sai da Musulunci ya kirkiro hanyoyi da tsare-tsaren hana aukuwan laifuffuka kana kuma ya tsaro kyawawan yanayi da zai kare dan'Adam da al'ummar da yake ciki daga fadawa cikin ramukan zunubai. A takaice dai, Musulunci ya yi amfani da duk wata hanya da yake da ita wajen ruguza abubuwan da suke haifar da aikata sabo da munanan ayyuka. Wadannan abubuwa kuwa su ne kamar haka:
1. Jahilci
2. Kaucewa ta tunani.
3. Bukatuwa da wani abu.
4. Rashin kulawa da kyawawan dabi'u da kuma rashin imani da azabar lahira.

1. Jahilci
Jahilci shi ne mafi girman al'amarin da ke hana mutum amfani da kwakwalwa da kuma fidirarsa. Ko shakka babu, duk mutumin da ya rasa cikakken ilimi da masaniya, to lalle ya rasa kwakwalwar tunani da bambance al'amurra, ya raunana ruhi da kuma kyawawan siffofinsa, kana kuma cikin sauki zai iya tunkuda kansa zuwa ga hanyar bata.
Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ko sun riki wadansu abubuwan bautawa, baicinSa? Ka ce (Ya Muhammadu), ku kawo hujjarku. Wannan shi ne ambaton wanda yake tare da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabannina. A'a, mafi yawansu ba su sanin gaskiya, saboda haka su masu bijirewa ne". (Surar Anbiya, 21: 24)
Wannan bayani yana tabbatar da cewa ba kasafai malamai da masana suke aikata munanan ayyuka ba, koda kuwa suna cikin lalatacciyar al'umma ce. Koda yake, yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa kariya ta ainihi daga munanan ayyuka tana samuwa ne ta hanyar mallakar "Ilimi irin na Ubangiji". Domin saboda rasa irin wannan muhimmin al'amari ne, ya sanya da yawa daga cikin malamai da masana suka zamanto masu taimako da kuma shirya barna, zubar da jini, aikata laifuffuka da kuma cutar da dan'Adam. Wadannan munanan dabi'u da kuma son aikata zunubai suna wanzuwa daga wadannan malamai ne, saboda tunani da ilmummukan da babu Allah a ciki ne yake ja-gorantarsu, wanda hakika hakan wani nau'i ne na jahilci, da ke haifar da mummunar sakamako.
Hakika Manzonmu (s.a.w.a) ya yi bayanin irin wannan al'amari, yayin da yake ba da amsar tambayar da aka yi masa cewa su wane ne mafi sharrin mutane? Sai ya amsa da cewa:
"Malamai idan suka lalace"[4].
A saboda wannan dalili ne, Musulunci ya kuduri aniyar yakan jahilci ta hanyar yada hanyoyin neman ilimi wanda hakan shi ne babban asasin gyara. Wannan babban muhimmanci da Musulunci ya bai wa ilimi ya samo asali ne daga irin i'itikadin da yake da shi na cewa rashin kyakkyawan ilimi na iya taimakawa wajen faruwar mummunan ayyuka da zunubai. Sannan kuma mallakar kyakkyawan ilimi mai amfani zai iya samar wa mutum hasken hikima da fahimta kana kuma ya taimaka masa wajen dasa imani, kaunar juna, tausayi da kyautatawa da kuma nuna rashin amincewa da duk wani nau'i na sabo.
"Ya ce, ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma amma ina ganinku, wasu mutane ne, masu jahiltar gaskiya". (Surar Ahkafi, 46: 23)
"Lalle ne kai, ba ka jiyar da matattu, kuma ba ka sa kurame su ji kiranka, idan sun juya suna masu bayar da baya. Kuma kai ba ka zama mai shiryar da dimammu daga bata ba. Ba ka jiyarwa face wanda yake yin imani da ayoyinmu. To, su ne masu sallamawa - al'amari zuwa ga Allah -". (Surar Namli, 27:80-81)
"A'a ha! Wadanda suka yi zalunci sun bi son zuciyoyinsu, ba tare da wani ilimi ba. To, wane ne zai shiryar da wanda Allah Ya batar? Kuma ba su da wadansu mataimaka". (Surar Rum, 30:29)
Hakika Alkur'ani mai girma ya siffanta wadanda suka jawo wa kansu fushin Allah da wadanda jahilci ya rufe musu ido.
Idan muka dubi cikin wadannan ayoyi na Alkur'ani, za mu iya fahimtar dalilan aikata munanan ayyuka a mahangar Alkur'ani:
Na farko, an kwatanta jahilci da cewa makanta da kurmanci ne tun da suna hana mutum yarda da gaskiya da kuma adalci.
Na biyu, an siffanta jahilci a matsayin mutuwa don kuwa yana lalata wa mutum rayuwa. Don duk wata alakar mutum da duk wani bangare na tunani da fahimta yakan lalace. Bugu da kari, Musulunci yana kwadaitar da dan'Adam wajen neman ilimi da masaniya wanda yakan bude masa hanyar shiriya da farin ciki. A saboda wannan dalili ne, Allah Ya aiko da Annabawa da Manzanni don su shiryar da mutane, ta hanyar dalilai da ilimi, zuwa ga hanya madaidaiciya.

2. Kaucewa Ta Tunani
Babu shakka, irin al'ummar da mutum ya taso a ciki da kuma tarbiyyar da ya samu, suna da matukar tasiri ga rayuwa da dabi'unsa. Domin akan haifi mutum ne a cikin mafi tsarkakakken yanayi, ta haka ne zai ci gaba da girma cikin irin yanayin da ya sami kansa a ciki, wadanda su za su tsara masa yadda halaye da dabi'unsa za su kasance.
Matukar dai mutum ya girma cikin kyakkyawan yanayi da kuma tsarkakan al'umma, to ruhinsa yakan sami wani karfi da kuma kulawa wanda ka iya bashi daman samun daukaka da kuma komawa zuwa ga alheri da kyawawan dabi'u. A takaice dai, zai iya samun damar isa ga babban buri da manufar rayuwarsa, wato biyayya da kuma mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki. A daya bangaren kuma, mutumin da ya rasa tsarkakakken yanayi da kuma tarbiyya mai kyau, yakan wayi gari cikin son kai, munanan ayyuka, rashin da'a da kuma rashin sanin ya kamata, wanda sakamakon hakan shi ne samar da wani irin dimaucaccen mutum wanda bai san ya kamata ba. Inda daga karshe mutum yakan zama bawan kyalkyale-kyalkyalen duniya da son zuciyarsa ta inda zai zamanto ya dabi'antu da aikata kisan kai, sace-sace, zinace-zinace, yaudara, shaye-shaye da kuma nisantar kyawawan dabi'u.
A saboda wannan dalili ne, Alkur'ani mai girma ya yi dubi cikin wadansu masu aikata zunubi kana ya nuna cewa addini, wato Musulunci, shi ne hanyar tsira. Sannan kuma mummunar dabi'a, wani takai-taccen yanayi ne na ruhi wanda za a iya magance shi ta hanyar kawar da irin munanan yanayin da yake ciki don a samar wa ruhi da kwakwalwa mutum abubuwan da suka dace da su. Hakika ayoyin Alkur'ani sun bayyanar da irin wadannan masu wuce haddi ta hanyar bayyanar da mummunan tunaninsu. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"Sa'an nan kuma a bayansu Muka aika Musa da Haruna zuwa ga Fir'auna da mashawartansa, tare da ayoyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutane masu laifi". (Surar Yunus, 10: 75)
"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cutar, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna yi na karya". (Surar Bakara, 2: 10)
"Kuma idan an karanta ayoyinmu a gare shi, sai ya juya baya, yana mai girman kai, kamar dai bai saurare su ba, kamar dai akwai wani danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushara da azaba mai radadi". (Surar Lukman, 31:7)
"Kuma suka yi musunsu, alhali zukatansu, sun natsu da su, domin zalunci da girman kai. To, ka dubi yadda karshen mabarnata ta kasance". (Surar Namli, 27:14)
"Idan aka karanta masa ayoyinMu, sai ya ce tatsuniyoyin mutanen farko ne". (Surar Mudaffifina, 83: 13)
"Za ni karkatar da wadanda suke yin girman kai a cikin kasa ba da wani hakki ba, daga ayoyiNa, kuma idan sun ga dukkan aya, ba za su yi imani da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiri-ya, ba za su rike ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar bata, sai su rike ta hanya. Wancan ne, domin lalle ne su, sun karyata da ayoyinMu, kuma sun kasance, daga burinsu gafilai". (Surar A'arafi, 7: 146)
Hakika daga wadannan bayanai na Alkur'ani, za mu iya fahimtar wani muhimmin al'amari, shi ne kuwa cewa wadannan batattun mutane, son zuciya da alfahari ne yake rudinsu. Don haka ne zukatansu suka kekashe, ba sa iya tunani mai kyau da fahimtar al'amurra. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"To, don me masu hankali ba su kasance daga mutanen karnonin da suke a gabanninku ba, suna hani daga barna a cikin kasa? Face kadan daga wanda muka kubutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma wadanda suka yi zalunci suka bi abin da aka ni'imatar da su a cikinsa, suka kasance masu laifi". (Surar Hud, 11: 116)
Hakika Alkur'ani mai girma ya ta kawo wadannan bayanai ne don ya shiryar da dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya, hakan kuwa don amfani 'yan'Adam da kuma daukakan gaskiya da adalci ne.
"Domin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya bata karya, kuma koda masu laifi sun ki). (Surar Anfali, 8: 8)

3. Bukatuwa
Hakika tabbataccen al'amari ne cewa biyan bukatan dan'Adam na duniya ako da yaushe yana daga cikin dalilan da suke kawo kyakkyawa kana tsarkakakkiyar rayuwa. Rahsin hakan kuwa na iya sa mutum ya gagara kare kansa daga fadawa cikin aikata munanan ayyuka da kuma laifuffuka. Don haka ne ma, Musulunci ya ba da gagarumin muhimmanci ga abubuwan bukatuwa na rayuwa ta hanyar tsara dokoki da ka'idoji wadanda za su taimaka wa mutum wajen gudanar da kyakkyawan rayuwa cikin farin ciki da daukaka.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da wannan al'amari, yayin da yake cewa:
"Babu abin da yafi taimakawa ikhlasi da gaskiya mutum kamar wadata"[5].
Sannan kuma yana cewa:
"Wadatar da take kare ka daga aikata zalunci ita ta fi fakircin da ke janka zuwa sabo"[6].
Kana kuma an ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da yake yabon Ubangiji, yana cewa:
"Ka albarkace mu da biredi (abinci), kada Ka raba tsakaninmu da shi, idan har babu abinci, to ba za mu sami daman yin salla, azumi da sauran wajibai ba"[7].
Don haka, Musulunci ya ba da matukar muhim-manci ga wannan al'amari ta inda har ya bayyana cewa babu laifi ga mutumin da ya aikata haramun yayin da yake cikin talaucin da rashin aikata wannan aiki zai kai shi ga rasa ransa. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"....to, wanda aka matsa, wanin dan tawaye, kuma banda mai zalunci, to, babu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin kai". (Surar Bakara, 2: 173)
Daga wannan bayani, za mu fahimci cewa wuce haddin dan'Adam ya samo asali ne daga rashin wadata. A takaice dai, a wasu lokuta, mutum yakan aikata zunubai a bisa tilas. A bisa haka, ana iya cewa al'ummomin da ba na Musulunci ba, ba su yi adalci wa dan'Adam ba don kuwa an bar shi ba tare da kare shi daga barazanar talauci, kuma aka raba shi daga ni'imar kyakkyawar rayuwa da kuma ilimi mai amfani. Hakika babu wani dalilin da za a tuhimci mutane kana a yanke musu hukumci kan aikin da suka aikata cikin tilas (ba da son ransu ba).

4- Rashin Kulawa da Kyawawan Dabi'u da Kuma Rashin Imani Da Azabar Lahira:
A duk lokacin da mutum ya rasa shaukin kyawa-wan dabi'u da rashin sanin ya kamata kana ya hadu da rashin imani da Allah da akidar sakamako da azaba bayan mutuwa, to jure wa rashin aikata zunubi zai yi masa wuya. Abu mai muhimmanci a wannnan al'amari, shi ne imani da Allah, Masanin abin da ke boye (gaibi), wanda Shi ne mabubbugar duk wani alheri da albarka kana Mai kula da duk wasu halaye na dan'Adam. Daga karshe, hakika Musulunci ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan ilimin akida da kuma wani tsari da zai kula da rayuwar mutum ta bayyane da ta ruhi.
4. Tuhaf al-Ukul na al-Harani, shafi na 36, bugu na biyar.
5. Usul al-Kafi na Kulaini, juzu'i na 5, shafi na 71.
6. Kamar na sama, shafi na 72.
7. Kamar na sama, shafi na 73.

No comments:

Post a Comment