An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Monday, 26 May 2014
TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
___________________(31)__________________
TANBAYA: Assalamu alaikum. Shin ya halasta na yi shamfo don mijina?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ni ban san Shamfo ba. Amma dai abin da zan iya cewa shi ne duk abin da ba a hana ka ba a shari'a, shi kenan kana iya yi. Amma ban san menene Shamfo ba.
Amma in dai shi ne mace ta fece gashinta ta shafa masa mai maimakon ta yi kitso, ko kuma ta yi kitso, to ta samu ta yi kowanne, duk halas ne.
___________________(32)__________________
TAMBAYA: Akramakallahu. Shin ya halasta in yi amfani da magani domin jin dadin jima'i.
SHAIKH ZAKZAKY: Idan ba zai cutar ba, babu laifi, sai dai kuma barinsa shi ne a'ala. Saboda galiba abubuwa sukan zama suna samar da wani irin sakamako. Wala'alla yanzu ya zama ya yi dadi amma daga baya ya kawar da sha'awa ko kuma ya rage karfi.
___________________(33)__________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Shin ya halasta in yi amfani da mai na shafe- shafe don canza fatar jikina?
SHAIKH ZAKZAKY: Shi ma in ba zai cutar ba, in ba zai cutar da mutum ba, babu laifi. Sai dai bari zai fi, don galiba wadanan abubuwan wani lokaci sukan haifar da wadansu abubuwa daga baya, ko da ba a sani ba yanzu. Amma in an aminta cewa babu wani cuta dangane da shi, babu komai.
Tana iya yiwuwa mutum ya ce ai Shaidan ya ce zai yi wa mutane wahayi su canza halittar Allah, to an fahimci cewa canza halittar Allah din shi ne umurtar su da su yi wadansu miyagun ayyuka wadanda suka saba ma yadda aka sani bisa fitira da ma dabi'a ta mutum, kamar yadda ya yi masu wahayi na yadda maza ke zaike wa 'yan uwansu ko mata suke zaike wa 'yan uwansu (Ludu ko madigo), yana daga cikin canza halitta din.
Da ire-iren wadansu abubuwan da Shaidan yakan kikiro su. Hatta ma shi wancan canje-canjen fata din in ta kai ma mikidarin wani aiki da wahayin shaidan, to shi ma yana iya zama irin haka din.
_________________(34)____________________
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Meye hukuncin karin jini a asibiti, alhali jinin najasa ne kuma ba ka san jinin wanene ba aka kara maka?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai shi karin jini ba shan jini bane, shan jini ne ya haramta. Kuma na san ko da ma nama ne, ai ba a cin na mutum. Saboda haka in dai karin jini ne ko ma karin fata ne, in zai yiwu a yanko fata daga wani wuri a dasa ma wani ya dasu, shi ma zai zama
babu laifi da shi.
Kuma wannan ma ko wane iri ne, ko da kafiri ne ko musulmi ne shi, idan jinin nasa ya shiga cikin jikin nasa, insha Allahu ya zama jinin musulmi.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment