Monday, 26 May 2014

TAMBAYA DA AMSA TARE DA SAYYID ZAKZAKY (H)

___________________(109)_________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, shin me ke kawo girgizar kasa ne, fushin Allah ne ko yanayi ne?

MALAM ZAKZAKY: To ita girgizar kasa tana daga cikin ayoyi. Don haka ne ma ake yin sallar Aya a lokacin da ta auku, kamar na khusufin wata da rana, duk ana yin sallolin ayoyi. Ko ma wadansu abubuwa wadanda mutane sukan gani, wadanda ba a saba ba, masu figitarwa.

Amma ita girgizar kasa tana iya zuwa ta hanyoyi daban-daban. Kamar yadda ka san yawan ruwa, ko ambaliyar ruwa shi ma yana iya zuwa. Amma ba yadda za a yi mutum ya ce lalle in ya auku yana nufin fushin Allah ne.

Kodayake Allah (T) ya halaka wasu al'ummu a baya da girgizar kasa. Amma ba wai lalle abin da yake nufi kenan ba, domin yanayi na iya kawo shi, tunda in ka lura a wadansu wurare ba ma a yin ta sam, kamar mu a nan nahiyarmu ba a san ta ba. Ga wadansu wurare, kuma wuri ne mai yawan aukuwa kowane lokaci.

Domin ana cewa a cikin motsin duwatsu da ke karkashin kasa ne ke kawo ta, wanda wani dutsen nan da nan sai ya motsa ya Ci wani wuri, sai ya bar wagegen gibi na kasa, sai ya rinka tasowa sama, har yayin da ya bayyana sama sai kasa din ta yi motsi.

To kuma wannan akwai wuraren da ake yawan samun sa.

__________________(110)__________________

TAMBAYA: Shin mutum zai iya yin hijira zuwa wata kasar da ake yin shari'a Musulunci, musamman a irin wannan lokacin?

SHAIKH ZAKZAKY: Ina ganin ita hijira ai ba wai kawai haka nan kawai kana zaune ne sai ka ce bari ke tashi ka yi hijira ba.

Da haka Annabi (S) ya yi da ba a sami addini ba. Zai gudu kenan. Ba sai ya tashi ya yi kira ga shari'a din ba? Ai sai ya yi ta kokari a yi shari'a din.

Amma na'am, idan ya ga akwai wani muhalli da ake addini wand yake can ya fiye masa, in ya fita can ba laifi. Sai dai ba sunansa ya yi hijira bane, sunansa ya gudu ne!

__________________(111)__________________

TAMBAYA: Dangane da yadda mutanen gari suke sakin matansu shin sun saku, kuma dan uwa na iya aura?

SHAIKH ZAKZAKY: To idan ya inganta a wajen su mutanen garin shi kenan, ko da a wurinsa shi bai inganta ba, in dai a wurinsu bisa mazhabarsu a yadda suke gani a hukuncin da ke hannunsu cewa wannan matar ta saku, to shi kenan ta saku din. Shi ma sai ya iya auren ta.

Kamar alal misali wadda ta gama idda bayan an sake ta saki uku a kalma daya masalan, mu a wurinmu wannan sakin bai inganta ba, ba ta 'ba'intu' daga gare shi ba, amma tunda su suna ganin ta 'ba'intu' shi kenan.

Ba zai ce tunda an yi sakin da ya saba ka'ida a wurina, saboda haka ta nan a matar wancan mutumin ba, don shi mutumin a ganinsa an riga an gama, ita ma tana ganin an riga an gama.

Saboda haka ita ba matar wancan bace, in ta gama iddarta shi kenan za ta iya halatta gare shi ya aure ta.
____________________(117)________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya in bi jam'in salla a bayyane, alhali ina nufin salla ni kadai?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh ya halatta. Kuma kana iya ruku'u da sujada tare da Liman alhali kai da unwanin kai kadai kake salla.

Kuma ma kana iya bin Liman a wani wuri a wani bangare na sallar kuma ka koma kana yi kai kadai a wani bangare, wato kamar dama can ka fara bin shi daga wani lokacin, kuma sai ka yanke shawarar ka fasa bi, yanzu ka zama mai sallarka.

___________________(118)_________________

TAMBAYA: Akramakallah, ko ya halasta mutum ya dauki dan siyasa a mashin su tafi kamfe a matsayin haya?

SHAIKH ZAKZAKY: To, shi dai da a ce misali zai dauki mutum ya kai shi wani
wuri ne shi kenan, daga nan sai ya biya shi ladansa, to sai mu ce wannan babu laifi da shi.

Amma idan misali in zai shiga kwararon kamfen din ne ana fantsan-fantsan a manna wa mashin din Fosta, shi kuma a rika cewa sai wane! To lallai yana kamfe ne.

Kuma abin da ya same shi a tafarkin wannan kamfe din dai yana daidai da abin da ya shafi wadancan. Alal misali kila ma ya yi shahada a wannan kamfe din.

Alal misali ya dauke su ne suka lika fosta din suna kamfe din su, tana iya yiwuwa 'yan adawa su far masu. To ka ga a nan ma tana iya yiwuwa wa ya yi shahada a
wannan kamfen, ka ga ya yi shahadar siyasa kenan ko? Saboda haka ya danganta da yadda al'amarin yake ne.

Amma in misali wannan dan siyasa ne (ya ce) ka dauke ni ka kai ni wuri kaza, kuma wurin nan za ka je ka sauke shi ne, shi kuma can za shi kamfe ne, ka ga ai wannan kai bai shafe ka ba, za ka iya yi. Kai ba kamfen kake yi ba.

Amma yanzu ka dauke shi ku bi titi yana wakar jam'iyyarsa, ana haya-haya, ana yabo, ana zagi, har ma a harbo dutse, to ke ga kana cikin kamfe. Saboda haka makomarka makomarsa kenan.

___________________(119)_________________

TAMBAYA: An ce mace ba ta bayyana
karatu a wajen da ake bayyanawa. To idan ta manta ta bayyana, yaya sallarta?

SHAIKH ZAKZAKY: To tana iya bayyanawa. An hana ta bayyanawa ga jin wani ajnabi ne. Idan a dakinta take sallah, ba wanda zai ji, sai mijinta, sai muharramanta, ta samu ta bayyana muryarta. An hana bayyana muryar ga wani ne na waje, ba bayyana muryar ne kawai aka hana ba.

Saboda haka ba da mantuwa ba, ko da gangan ne, tana iya yi, idan dai wani ba zai ji ba. Amma idan mantuwar ya sa ta manta ta yi, kuma wani ajnabi ya ji, to wannan bai bata sallarta ba. Sai dai abin da ta yi tunda mantuwa ne, to ba komai. Da gangan ne ba za ta yi ba.

___________________(120)_________________

TAMBAYA: Mutum zai iya canza taklidi daga Mai risala zuwa Mujtahidi?

SHAIKH ZAKZAKY: To ni ban san ma'anar Mai risala ba. Domin abin da muka sani (shi ne) ana yin taklidi da Mujtahidi ne, shi Mujtahidi ne yake rubuta Risala. Risala kamar sako ne na hukunce-hukuncen da shi Mujtahidin ya rubuta.

(Saboda a nan kamar abin da ya nuna kamar Mujtahidi daban, Mai risala
daban. Da ma abin da yake tambaya shi
ne mutum yana iya canza taklidi daga
Risalar wani Mujtahidi zuwa Risalar
wani Mujtahidi, wanda yake nufin kawai
daga Mujtahidi zuwa wani Mujtahidi,
tambayan kenan).

Sai mu ce masa, in haka nan ne daga Mujtahidi zuwa Mujtahidi yake nufi, sai mu ce eh!

Amma kalmar Mai Risala, lallai ba ta da wani ma'ana a nan, don Mujtahidai ne ke rubuta Risala, kuma ba masu Risala ake ce masu ba.

1 comment:

  1. Allah ya saka da alheri, don Imamul-Hujja (A.F) a taimaka mana da app ɗin littafin nan

    ReplyDelete