Monday, 26 May 2014

_TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

__________________(97)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne matarsa ta nemi da ya bar ta ta rika zuwa makaranta, amma ya hana, kuma shi ya ki ya koya mata. To yaya za ta yi?

SHAIKH ZAKZAKY: To wajibi ne dai ta bidi ilimi. In ilimin nan na aikata wajibi ne, to shi ma bidarsa ya zama wajibi.

Saboda haka in ya hana mata, to lalle ta samu ta tafi ko da bai yarda ba. Amma wannan zai fi kyau ya zamana ba kawai tafiyar za ta yi ba, sai ta kai shi kara, har ya zama a sasanta tsakaninsu, a nuna masa wajibin ya kyale ta ta bidi ilimi.

____________________(98)_________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. An ce idan mutum ya wayi gari da janaba azuminsa ya baci. Shin zai yi kaffara ne?

SHAIKH ZAKZAKY: Idan da gangan ne ya bar janabar har lokacin da alfijir ya keto, to, lalle ramuwa da kaffara sun hau kansa. Amma idan da rashin sani ne masalan, to babu komai, sai ya yi wanka din. In kuma da mantuwa ne shi ma babu komai. Amma a dukkan wadannan ramuwa ne kawai ya hau kansa.

__________________(99)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan mace ta sa kayan da Musulunci ya amince mata ta sa, kuma ta sa takalmi wanda idan tana tarfiya ana jin karar tafiyarta. Shin ta saba doka kenan ko kuwa?

SHAIKH ZAKZAKY: To, idan da ma shi wannan takalmin an yi shi ne don ya jawo hankali ya saba mana.

A cikin Alkur'ani Allah (T) yana cewa, "kada su buga kafafuwansu don a san abin da suka boye na kayan ado."

A wancan lokacin mata kan sa kwandagai a kafa, saboda haka mace bayan ta sa hijabi, in tana son a san tana da kwandagai na zinarori, sai ta buga kafanta, sai a ji su suna kara. Aka ce kar su yi haka nan.

To, shi ma wannan buga takalmi mai kara ya so ya yi kama da shigen iren wadannan. In da ma shi takalmin yakan jawo hankali ne cewa ga mace na wucewa. Amma in wanda yake dama adatan ne, karar takalmi wanda bai sabawa al'ada ba. Kodayake shi wannan yana nufin na jan hankalin ne ko?

Sai mu ce haramun ne kamar buga kafa don a ji adon kwandagai ne.

___________________(100)_________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Wani ya shaida mani cewa, Malam ya ce idan mace ta zauna a wuri ta tashi, to kada ka zauna har sai wurin ya sha iska. To wannan ya yake?

SHAIKH ZAKZAKY: To haka din ne yana daga cikin 'gara'ib' na hukunce- hukuncen mata, cewa yana da kyau idan mace ta tashi a wuri, kada namiji ba mijinta ba ya zauna, har sai ya yi sanyi.

___________________(101)_________________

TAMBAYA: Akramakallahu. Ko ya halasta na ba yaro nono alhalin ina cikin janaba?

SHAIKH ZAKZAKY: Ai ko da ya haramta, da shayarwa ta yi wahala. To lalle ba wani abu da aka samu dangane da haramcin ba da nono a yayin janaba. Bilhasali ma zamanin janaba yana iya daukar lokaci, shi kuma yaron yana iya yiwuwa ma da nonon ya dogara. A takaice dai shi nonon ba ya janaba.



___________________(102)_________________

TAMBAYA: Akramakallah. Ko mace za ta iya zuwa makarantar da gwamnati ta bude don koya wa mata sana'a?

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da ya kamata ya zama shi ne kawai, mace za ta iya zuwa makaranta don koyon sana'a? Da alama abin da ya dami ita mai tambayar ita ce gwamnati ce ta bude.

To, in dai ba wadansu ka'idodi ne aka gindaya wadanda suke saba wa shari'a ba, shi kenan sunanta makaranta kawai.

___________________(103)_________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Wadanne hanyoyi ya kamata mutum ya bi kafin ya saki matarsa?

SHAIKH ZAKZAKY: Matakai ne kamar hudu ko biyar. Na karshensu ne saki.

Amma a takaice akwai wa'azi; akwai kaurace mata; akwai ya dan yi mata fada; da zare ido, idan duk wannan bai yi ba. Ya danganta da abin da ya sa yake so ya sake ta din ne.

Sannan kuma in hakan ya ki sai a nemo masu sasantawa - da nasa bangaren da nata bangaren. Sai in ya ki, ya zama dai kawai maslahar shi ne saki, to shi ne sai ya jira har sai ta yi tsarki daga haila, kuma a lokacin tsarkin bai tabe ta ba. Sannan ya yi 'insha'in' saki din ga shaidu, adalai guda biyu akalla.

__________________(104)__________________

TAMBAYA: Akramakallh. Zai kira shaidun ne ya ce ku shaida na saki matata, ko sakinta kawai zai yi?

SHAIKH ZAKZAKY: A'a ba lalle ne ya ce masu su yi shaida ba. Idan dai a gaban adilai ya yi, ko bai ce masu ku zo ku yi shaida ba, sun zama shaidu.

Abin nufi dai a yayin da ya yi 'inshain' sakin, wasu mutane adilai sun ji. Amma ba lalle ne ya ce wane da wane ku zo ku yi mani shaida ba.

___________________(105)_________________

TAMBAYA: Ko ya halatsa mutum ya yi wa 'yarsa auren dole?

SHAIKH ZAKZAKY: Idan yarinya ce karama wacce ba ta balaga ba, ba ta hankalta ta san wanene ya kamata ta aura ba, kuma maslaha ne aurar da ita, saboda wani dalili masalan, kamar lafiyarta ko wani abu, ko don jin tsoron lalacewarta, ko abin da ya yi kama da haka nan, kuma ya sami wanda ga nazarin shari'a, shi ne ya fi dacewa. Amma sai ya zama ita saboda rashin hankali, tana ganin ba shi ne ya fi ba, to a nan ne kawai yake da iko.

To, amma kuma Uba ne kawai da Kaka, wato Uban Uba suke da wannan.

Amma in banda haka, shi aure ana so ya kasance akwai neman yardar yarinya.

Har ma aka ce wacce ta taba aure, wato bazawara kenan, ta amsa da bakinta ta ce "eh." Karamar yarinya kuma ta ba da izini da yin shiru.

Wannan ana son haka nan, sai dai idan maslaha ne ya zama dole. Sai in dole ne za a cimma wannan maslala din, to wannan kuwa.

No comments:

Post a Comment