Tasirin Sabo Ga Mutum
Sabo wani irin al'amari ne da yake tare da dan'Adam, to amma yana tabbatuwa ne a duk lokacin da mutum ya zabi ya bayyanar da shi. Don haka, daga lokacin da aka bayyanar da shi, to yakan bakanta zuciyar mutum. Sannan kuma daga lokacin da zunubi da sabo suka mamaye wannan guri (zuciya), to mutum yakan rasa shaukin aikata alheri da abubuwa masu kyau, kuma zahirinsa yakan misaltu da aikata muggan ayyuka da kuma mugunta. A saboda wannan dalili, za mu ga duk mutumin da ya rasa kimarsa na dan'Adamtaka yakan yi kunnen uwar shegu da kuma nuna rashin damuwarsa kan aikata ayyukan alheri. Irin wannan mutum yakan zama kasurgumin mai aikata laifuffuka da zunubai. Alkur'ani mai girma yana bayani kan irin wannan mummunan al'amari, cewa:
"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi, saboda abin da suka kasance suna yi na karya". (Surar Bakara, 2: 10)
"A'a ha! Ba haka ba abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu". (Surar Mudaffifin, 83: 14)
"...to, a lokacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukatansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasikai". (Surar Saff, 61:5)
"Sa'an nan kuma zukatanku, suka kekashe daga bayan wancan. Saboda haka suka zama kamar duwatsu ko mafi tsanani ga kekashewa". (Surar Bakara, 2: 74)
"To, saboda warwarewarsu ga alkawarinsu, da kafiratarsu da ayoyin Allah, da kisan su ga Anna-bawa ba da hakki ba, da cewarsu, zukatammu suna cikin rufi. A'a, Allah ne Ya yunke a kansu saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan". (Surar Nisa'i, 4: 155)
Daga wannan bayani na Alkur'ani, za mu fahimci cewa, an arzurta dan'Adam da hankali, hangen nesa da kuma karfin godiya. A dalilin haka, yake son aika-ta alheri da ayyukan alheri kwarai. Kana kuma yana nesantar munanan ayyuka wadanda suka bar mummunan tasirinsu a kwakwalwarsa, ta yadda bai damu da aikata duk wani laifi ba kana ya zamanto ya dabi'antu da aikata zunubai ba tare da nuna damuwa da yin nadama ba. Sannan ya zamanto wani irin mutum mai kiyayya da duk wani bangare na kyakkyawan rayuwar dan'Adam, kuma ya rasa duk wani irin nau'i na mutunci, karama, tsarkaka da dan'Adamtaka. A takaice dai, zai iya zama kasurgumin mai laifi.
Don haka, Alkur'ani mai girma ya lissafa irin mummunan tasirin da aikata sabo da zunubi da kuma ci gaba da aikata su yake haifarwa. Inda ya kawo mafi hadarinsu kamar haka:
1. Al-Zaigh : Kaucewa daga tafarki madaidaici.
2. Al-Maradh : Cuta (ciwo).
3. Al-Rain : Tsatsar zuciya.
4. Al-Kaswa : Kekashewar zuciya.
5. Al-Tab'i alal Kalb : Lullubewar zuciya.
Saboda haka, daga lokacin da mutum ya saba da aikata zunubai da sabo, to zuciyarsa takan cutu ta yadda za ta katangu daga fahimtar abin da ya dace. Zuciyar mutum takan bakanta ta yadda duk rayuwarsa za ta zamanto cikin aikata sabo da laifuffuka.
Dangane da wannan al'amari, maganganun Imam Sadik (a.s.) sun bayyana irin mummunan tasiri da sabo yake yi a kan mutunci dan'Adam, kana yana mai karin haske kan ma'anonin wadancan ayoyin Alkur'ani da suka gabata. Don haka, aka gargadi musulmi da cewa babu wani bambanci tsakanin karamin zunubi da babba, kana ya ci daga da neman gafarar Ubangiji don ya sami damar gujewa hanyar bata kuma da samun damar rayuwa wacce take cike da tsoron Allah da kuma tsarkaka.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"Babu wani abin da yake lalata zuciyar mutum kamar zunubi, zuciyarsa takan gurbata da zunubai ta yadda shi zai zamanto bawanta - sai abin da ta so zai aikata -"[3].
3. Usul al-Kafi na Kulayni, juzu'i na biyu, shafi na 268, bugu na uku.
No comments:
Post a Comment