An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Sunday, 25 May 2014
YADDA MUSULUNCI YA MAGANCE MATSALAR SABO
Yadda Musulunci Ya Magance Matsalar Sabo
Saboda la'akari da kasantuwan sabo na daga cikin ayyukan da suke ruguza al'umma, Musulunci ya yi amfani da duk wani karfi da yake da shi wajen tsige tushen wannan bala'i, don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al'umma. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ya mutanen littafi! Lalle ne, ManzonMu ya je muku, yana bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kuna boyewa da littafi, kuma yana rangwame daga abu mai yawa. Hakika, wani haske da wani littafi mai bayyanawa ya je muku daga Allah. Da shi, Allah Yana shiryar da wanda ya bi yardarSa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininSa, kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya". (Surar Ma'ida, 5: 15-16)
Musulunci ya yi hakan ne saboda la'akari da ka'idojin da suka dace da ci gaban dan'Adam da al'ummar da yake ciki, don kuwa Musulunci ya kasance addini ne na ilimi da kuma shiryarwa irin ta ruhi. Kana kuma, Alkur'ani a fili ya bayyana cewa manufar Musulunci ita ce shiryar da dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya ta hanyar fitar da shi daga duhu zuwa ga haske don ya samu damar rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. A takaice dai don mutum ya sami kyakkyawan raywua da kwanciyar hankali, Musulunci ya dauki wasu matakai da tsare-tsare don ruguza kangin sabo da rashin biyayya, sannan kuma ya bude kofofin biyayya da kuma mika wuya ga gaskiya da kyawawan al'amurra. Daga cikinsu, akwai:
1- Yada Ilmi da Masaniyya da kuma Yakar Jahilci da Camfe-Camfe
Don ba wa mutum daman kiyaye shu'uri, tunani da mutuncinsa, Musulunci ya jaddada muhimmancin amfani da wa'ayi da kuma kwakwalwa. Alkur'ani mai girma, dangane da hakan, yana cewa:
"….Malamai kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa….". (Surar Fadir, 35: 28)
Dangane da hakan ma, Imam Musa al-Kazim (a.s.) yana cewa:
"Hakika an halicci mutane ne don su yi da'a wa Allah. Ceto ba ya yiyuwa ba tare da biyayya ba, kuma biyayya ba ta yiyuwa sai da ilimi"[8].
2- Imani Da Adalcin Allah Da Kuma Sakama-kon Lahira.
Wannan al'amari ya kasance daya daga cikin shika-shikan akidar Musulunci, kuma an yi bayanin wannan al'amari cikin Alkur'ani mai girma:
"To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
Saboda karfafa wannan tabbatacciyar akida, mumini yakan sadaukar da kansa ga kyawawan dabi'u da kuma guje wa munana. Wadannan ayoyi na Alkur'ani mai girma masu zuwa, sun yi bayanin wannan lamari:
"Kuma ku tsayar da su, lalle su, abin tambaya ne". (Surar Saffati, 37: 24)
"Kuma kowane mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a ranar lahira da littafi wanda zai hadu da shi budadde". (Surar Isra', 17: 13)
Hakika daga lokacin da mutum ya damfaru da wannan akida, to zai fahimci dadin da ke cikin biyayya da kuma aiki daidai da dokoki da ka'idojin kyakkyawan rayuwa wacce take cike da farin ciki da daukaka. Ko kuma ana iya cewa, ayyuka da daukakan dan'Adam zai samu tsarkaka.
"….kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku....". (Surar Bakara, 2: 235)
"Allah Ya san yaudarar idanu da abin da kiraza ke boyewa". (Surar Ghafir, 40: 19)
3- Biyan Bukatun Dan'Adam Da Kuma Magance Talauci.
A koda yaushe wannan babban al'amari yana nuna irin kokarin da Musulunci yake yi wajen kawar da tasirin tsananin talauci. Don kuwa, Musulunci ya sanya biya wa dan'Adam bukatunsa na yau da kullum a matsayin daya daga cikin wajibansa, ta hanyar kirkiro da harajoji na wajibi kamar su zakka, khumsi (daya bisa biyar na kudin shigan mutum) don kubutar da 'yan'Adam daga barazanar talauci. Hakika tun farko halittar dan'Adam aka kafa wadannan wajibai. Dangane da hakan Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Lalle ne ka samu, ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba". (Surar D.H., 20: 118)
"Saboda haka, sai su bauta wa Ubangijin wannan gida (Ka'aba). Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsoro". (Surar Kuraish, 106: 3-4)
4- Kariya ta Shari'a
Daga cikin muhimman siffofin sakon Musulunci shi ne cewa yana daukan kwararan matakan tsaro da kuma kariya daga aikata zunubi kafin hukumta wanda ya aikata shi, hakan kuwa ta hanya tsara dokoki da ka'idojin da za su tabbatar da tsaro ga dan'Adam. Hakika Musulunci ya haramta kisan kai, sata da yin zina, to amma bai tabbatar da hakan ba tare da ya tsige duk wasu munanan hanyoyi (da suke janyo hakan) ba, kamar giya, caca da hotuna da fila-filan batsa da dai sauransu.
5- Kange Mutane da Kuma Tsarurrukan Gyara
An siffanta mutum da cewa shi wata halitta ce wanda halaye da mu'amalarsa da sauran 'yan'uwansa yana da wani irin gagarumin tasiri ga dabi'unsa, koda yake irin kaskantar da shi da mutane za su yi a duk lokacin da ya saba wa wata ka'ida ta kyawawan dabi'u za ta iya kaskantar da shi ya zama ba kome ba. A sakamakon haka, zai yi kokarin boye kansa daga mutane don ya tserar da kansa daga cin mutuncin mutane.
Don haka, an halitta wa mutum wannan mika wuya na fidira ce don ya yi daidai da hikimar Ubangiji wacce ta kasance take amfanar da mutum wajen kaunar dokoki da adalci. Bayan da ya wajabta wa mutum aikata kyawawan dabi'u da kuma hana shi aikata munana, Musulunci ya samu nasara wajen ware wadannan mutane (masu sabo) da niyyar sanya su cikin kunci da jin kunya don ya motsar da fidirar alheri da daukaka ta inda za su sami sauyin ra'ayi kan aikata sabo.
An ruwaito Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"A duk lokacin da wani ya kawo maka zancen wani, to ka ce masa, idan har kana son ka zauna da mu, to dole ne ka bar aikata hakan, idan har bai bari ba, ya zama dole ku kore shi"[9].
6- Tuba Da Kuma Fatan Gafarar Ubangiji.
Tuba wata hanya ce da Allah, cikin ni'ima da rahamarSa, Ya arzurta bayinSa da ita don su sami mafaka daga zunubansu. Allah Yana gaya wa masu barna cewa:
"Ka ce: (Allah Ya ce), Ya bayiNa wadanda suka yi barna a kan rayukansu! Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Na gafarta zunu-bai gaba daya. Lalle Shi, Shi ne Mai gafara, Mai jin kai". (Surar Zumar, 39: 53)
Daga wannan bayani, za mu fahimci cewa tuba ta kasance tana da tasiri wajen dawo da mutum zuwa ga fidirarsa, kana tana ba shi daman tuntuni cikin zunubansa da suka gabata da kuma daura aniyar aikata alheri da barin sabo. A saboda tunanin gafarar Ubangiji da sabuwar hanyar da ya kama, shi wannan mai tuba, saboda tasirin wannan sabon yanayi da ya samu, zai sami karfin gwuiwa da kyakkyawan rayuwa.
Karfin Mulki (Shari'a) Da Kuma Tarbiyyantarwa.
Hakika a fili yake cewa hukumta masu laifi zai kare su daga ci gaba da wannan mummunan aiki nasu don su kare mutuncinsu. Alkur'ani mai girma ya yi bayanin muhimmancin hukumta masu laifi:
"Kuma kuna da rayuwa a cikin kisasi, ya ma'abuta hankula; tsammaninku, za ku yi takawa". (Surar Bakara, 2: 179)
Dangane da wannan al'amari Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Abubuwan da doka (hukuma) za ta iya hanawa ta hanyar mai mulki, ba zai yiyu ga Alkur'ani ya hana ba"[10].
Bayan da aka riga aka gano tasirin hukumci wajen hana aikata laifi, Musulunci ya kirkiro haddi (hukumci) a matsayin wata muhimmiyar hanya wajen hana aikata laifuffuka a lokacin da ilimi da tarbiyya suka gagara samun nasara. Don haka, gudanar da hukumce-hukumce tare da kira ga kyawawan dabi'u sun kasance mafi dacewan al'amari wajen gyaran al'umma.
8. Tuhaful Ukul na Al-Harani, shafi na 289.
9. Wasa'il al-Shia na Hur al-Amili, juzu'i na 11, shafi na 410, bugu na biyu.
10. Hadisin Kudsi.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment