An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Wednesday, 28 May 2014
BADA'IN ALLAH (T)
BADA'IN ALLAH MADAUDAKI
“Bada” ga mutum; shi ne wani sabon ra’ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra’ayin ba, wato ya canja niyyarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi domin faruwar wani abu gareshi da zai sanya canji a ra’ayinsa da saninsa, sai ya canja niyya sai ya bar aikata shi bayan da can yana nufin ya aiwatar da shi, wannan kuwa ya faru ne sakamakon jahiltar maslaha da kuma yin nadama a kan abin da ya gabata. “Bada” da wannan ma’anar mustahili ne ga Allah (S.W.T) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa, wannan kuwa ya koru ga Ubangiji, kuma Shi’a Imamiyya ba su yarda da shi ba. Imam Sadik (A.S) ya ce: “Wanda ya yi da’awar cewa canji cikin wani abu ya faru ga Allah (S.W.T) game da wani abu canji irin na nadama, to a gurinmu wannan ya kafirta da Allah mai girma”. Kuma ya ce: “Wanda ya raya cewa wani abu na canjin ra’ayi ya faru ga Allah wanda ya kasance bai san shi ba jiya to ka barranta daga gareshi”.
Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kusan nuni da ma’anar “Bada” kamar yadda ta gabata, kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (A.S) cewa: “Wani abu bai taba bayyana ba ga Allah kamar yadda ya bayyana gareshi game da Isma’ila dana”. Don haka ne wadansu daga marubutan musulmi suka danganta Bada ga Shi’a Imamiyya da waccan ma’ana domin suka ga mazhaba kuma tafarki na Ahlul Baiti (AS), suka sanya wannan daya daga abubuwan da suke suka da aibata shi’a da shi. Sahihiyar magana a nan ita ce, mu muna fadi kamar yadda ubangiji ya fada a littafinsa ne cewa:
“Allah yana shafe abin da ya so kuma yana tabbarwa kuma Ummul kitab a gunsa take ”. Surar Ra’ad: 39.
Abin nufi shi ne cewa Allah (S.W.T) na iya bayyanar da wani abu ta harshen Annabinsa ko waliyyinSa ko kuma a zahiri saboda wata maslaha da ta sanya bayyanawar, sa’annan daga baya sai ya shafe shi ya zama ba abin da ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S) Ya ga yana yanka shi a mafarki. A nan sai ma’anar maganar Imam Sadik (A.S) ta zama cewa: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa yayin da ya dauki ransa kafin rasuwar Imam Sadik (A.S) domin mutane su san cewa shi Isma’ila ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.
Wani abu da yake kusa da ma’anar “Bada” shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) da kuma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen da Annabinmu (S.A.W) ya zo da su.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment