Monday, 26 May 2014

TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

___________________(106)_________________

TAMBAYA: Akramakallah. Ko ya halasta mutum ya rika amfani da kayan da ya jingina, kamar gona, gida, ko mota?

SHAIKH ZAKZAKY: To da ma jingina, kamar yadda sunan ya nuna da Hausa, ana jingine abin ne, har sai ya biya bashin sai ya zo ya karbi kayansa.

Saboda haka ba a amfani da kayan jingina. Wannan shi ne abin da aka sani cewa; mutum in ya karbi ko da gona ce, ba zai noma ta ba. Za a bar ta ne har sai ya biya bashin, sannan sai ya mai da wa mai kayan.

Sai dai idan da ma tun farko a yarjejeniyar ya ce, "to idan ruwan shuka ya fadi fa, na samu in noma gonar nan?" Domin gonar tana nan a gonar mai gona.
"Kuma in na noma nawa zan ba ka? Tunda gonar tana nan a gonar mai gona, ba ta zama gonar wanda ya karbi jingina ba. Saboda haka sai zama ya ba shi izini in har bai iya biyan bashin ba shi ya noma gonar, amma ya ba shi galla.

Ko kuma ya zauni gidan (in gida ne) ya biya shi haya. Ko in wani abin amfani ne ya yi amfani da shi, amma ya biya shi haya. In ya yarda, in an yi yarjejeniyar a kan haka. In ba haka ba ajiyewa ake yi har sai ya biya bashi din.

____________________(107)________________

TAMBAYA: Akramakallah. Mutum ne ya gina masallaci a gidansa, daga baya sai matsalar kudi ta same shi. Ko zai iya matsar da masallacin ya yi amfani da filin?

SHAIKH ZAKZAKY: To masallatai dai iri-iri ne dama, akwai masallacin gida, wanda yake mutum ne ya kebance wani wuri a cikin gidansa don ya rika salla, ko ma a dakinsa ne ma. Daidai inda ka yi shimfida kake salla a dakinka ana ce masa masallacinka, in ka so kana iya canza wannan, irin na gida.

Akwai masallacin Unguwa, akwai wanda ake ce ma masallacin kabila, ko masallacin gari, na Juma'a kenan.

To su na kabila da na gari, wannan har abada na Allah ne. Saboda haka ba za a je gare su da wani abu ba sai abin da zama maslaha.

Yana iya halatta idan ya zama maslaha ne ga masallacin da al'ummar da suke salla su canza wa masallacin wuri. Wannan zai yiwu. Ko kuma wani dalili wanda yake don maslahar al'umma, ko hanya, ko hanyar ruwa, ko wani abu da ya yi kama da haka nan, ya tilasta a yi haka nan, ana iya yi.

Saboda haka in masallacin gida ne yake nufi, wannan duk abin da ya ga dama yana iya yi. Amma in masallacin Unguwa ne, to, da ma na al'umma ne, ba nasa bane.

___________________(108)_________________

TAMBAYA: Akwai kuma wadanda masu kudi kan gina a gidajensu wanda ake ce wa "Allah-ga-naka"?

MALAM ZAKZAKY: To idan masallacin gida, duk yadda ya ga dama yana iya yi da shi saboda shi masallacin gida bai da wannan matsayin masallacin Unguwa da na Juma'a.


___________________(109)_________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, shin me ke kawo girgizar kasa ne, fushin Allah ne ko yanayi ne?

MALAM ZAKZAKY: To ita girgizar kasa tana daga cikin ayoyi. Don haka ne ma ake yin sallar Aya a lokacin da ta auku, kamar na khusufin wata da rana, duk ana yin sallolin ayoyi. Ko ma wadansu abubuwa wadanda mutane sukan gani, wadanda ba a saba ba, masu figitarwa.

Amma ita girgizar kasa tana iya zuwa ta hanyoyi daban-daban. Kamar yadda ka san yawan ruwa, ko ambaliyar ruwa shi ma yana iya zuwa. Amma ba yadda za a yi mutum ya ce lalle in ya auku yana nufin fushin Allah ne.

Kodayake Allah (T) ya halaka wasu al'ummu a baya da girgizar kasa. Amma ba wai lalle abin da yake nufi kenan ba, domin yanayi na iya kawo shi, tunda in ka lura a wadansu wurare ba ma a yin ta sam, kamar mu a nan nahiyarmu ba a san ta ba. Ga wadansu wurare, kuma wuri ne mai yawan aukuwa kowane lokaci.

Domin ana cewa a cikin motsin duwatsu da ke karkashin kasa ne ke kawo ta, wanda wani dutsen nan da nan sai ya motsa ya Ci wani wuri, sai ya bar wagegen gibi na kasa, sai ya rinka tasowa sama, har yayin da ya bayyana sama sai kasa din ta yi motsi.

To kuma wannan akwai wuraren da ake yawan samun sa.

__________________(110)__________________

TAMBAYA: Shin mutum zai iya yin hijira zuwa wata kasar da ake yin shari'a Musulunci, musamman a irin wannan lokacin?

SHAIKH ZAKZAKY: Ina ganin ita hijira ai ba wai kawai haka nan kawai kana zaune ne sai ka ce bari ke tashi ka yi hijira ba.

Da haka Annabi (S) ya yi da ba a sami addini ba. Zai gudu kenan. Ba sai ya tashi ya yi kira ga shari'a din ba? Ai sai ya yi ta kokari a yi shari'a din.

Amma na'am, idan ya ga akwai wani muhalli da ake addini wand yake can ya fiye masa, in ya fita can ba laifi. Sai dai ba sunansa ya yi hijira bane, sunansa ya gudu ne!

__________________(111)__________________

TAMBAYA: Dangane da yadda mutanen gari suke sakin matansu shin sun saku, kuma dan uwa na iya aura?

SHAIKH ZAKZAKY: To idan ya inganta a wajen su mutanen garin shi kenan, ko da a wurinsa shi bai inganta ba, in dai a wurinsu bisa mazhabarsu a yadda suke gani a hukuncin da ke hannunsu cewa wannan matar ta saku, to shi kenan ta saku din. Shi ma sai ya iya auren ta.

Kamar alal misali wadda ta gama idda bayan an sake ta saki uku a kalma daya masalan, mu a wurinmu wannan sakin bai inganta ba, ba ta 'ba'intu' daga gare shi ba, amma tunda su suna ganin ta 'ba'intu' shi kenan.

Ba zai ce tunda an yi sakin da ya saba ka'ida a wurina, saboda haka ta nan a matar wancan mutumin ba, don shi mutumin a ganinsa an riga an gama, ita ma tana ganin an riga an gama.

Saboda haka ita ba matar wancan bace, in ta gama iddarta shi kenan za ta iya halatta gare shi ya aure ta.

No comments:

Post a Comment