*~ ZUWA GA IYAYEN 'YA'YA DA MASU NEMAN AURE ~*
* Wani mutumi ya zo wajen Imam Hasan (AS) yana neman shawararsa akan zai aurar da 'yarsa.
Sai Imam Hasan (AS) ya ce masa:
“ Ka aurar da ita ga mutum mai tsoron Allah, domin shi zai girmamata idan yana sonta, kuma ba zai zaluncetaba idan baya sonta ”
* Manzon Allah (S) kuwa yace:
“ Idan wanda ku aminta da (kula da) addininsa, da amanarsa ya zo yana neman (aure) daga gare ku, to ku aurar masa. In ba ku aikata hakan ba, fitina za ta kasance a doron kasa da kuma fasadi (barna) mai girma ”
~ Wadannan Hadisan sun zo a cikin littafin Muzanul-Hikma, J-2, sh-1184.
* Imam Ali Bin Musa Arridha (AS) yace:
“ Idan wani mutum da ka yarda da Addininsa da 'Dabi'unsa ya nema (aure) a wajenka, to ka aura masa, kar ka damu da talaucinsa ko wadatarsa ”
Allah (T) yana cewa:
“ In sun kasance Fakirai (matalauta) Allah zai wadatasu daga falalarsa. ”
_ ~ Surar Nur: 32.
~ Wannan Hadisin ya zo a cikin littafin Muzanul-Hikma, J-2, sh-1183.
• Ga kai kuma mai neman aure:
* Annabi (S) ya ce:
“ Ana auren mace saboda abubuwa guda hudu: - Saboda kudinta (dukiya), - saboda addininta, - saboda kyanta, - saboda nasabarta.”
Sai Manzon Allah (S) ya ce:
“ Na hore ka da ka auri ma'abociyar addini. ”
~ Kanzul-Umal, J-2, sh-446.
* A wani hadisin kuma Manzon Allah (S) yace:
“ Duk wanda ya auri mace, ba dan komai ba sai don kyan (surarta), ba zai taba ganin abin da yake so ba a tare da ita. ”
~ Kanzul-Umal, J-19, sh-235.
* Har wa yau, Annabi (S) ya kara da cewa:
“ Kar ku zabi kyan fuskar mace diye da kyawun addininta. ”
~ Kanzul Ummal, H-44590.
* Manzon Allah (S) ya kare jan kunnenmu da cewa:
“ Duk wanda ya aureta (mace) saboda dukiyarta, Ba shi zai aureta (mallaketa) ba, ita ce zata mallake shi, kuma Allah zai daurata a kansa. Dan haka na horeku da (neman auren) ma'abociyar addini ”
~ Bihar, J-19, H-235.
No comments:
Post a Comment