Mene ne Sabo?
Ana iya fassara sabo da cewa wani yanayi ne na kin yarda da kasancewa karkashin mashi'ar Ubangiji, wanda a hakikanin gaskiya, mashi'a ce ta alheri da adalci. Sannan kuma za a iya fassara shi da cewa wani yunkuri ne na dan'Adam wajen yin karen tsaye wa dokoki da ka'idojin rayuwar 'yan'Adam. Dukkan halittu an halicce su ne da wasu irin tsarurruka da haddodi da suka dace da su; wadanda saba musu haramun ne. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, kuma ya ketare iyakokinsa, Zai shigar da shi wuta". (Surar Nisa'i, 4:14)
Don haka, an bayyana sabo a matsayin abu mai cutarwa, wanda ya saba wa dabi'ar dan'Adam.
Su batattun mutane masu wuce haddi sun kasance suna rasa fahimtar munin wuce haddi, sannan ba sa girmama ma'ana da kimar abubuwa. Don haka ne ba sa yin mu'amala da kyawawan abubuwa, kuma suka saba wa tsarurrukan hankali da kuma mika wuya ga munanan ayyuka. A sabili da haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya siffanta shirka - don kuwa ita ce ginshikin duk wani sabo- a matsayin fadowa daga wani waje mai tsawon gaske, inda yake cewa:
"...kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yana kamar abin da ya fado daga sama, sa'annan tsuntasaye suka café shi, ko kuma iska ta fada da shi a cikin wani wuri mai nisa". (Surar Hajj, 22: 31)
A saboda haka, sabo ya kumshi duk wani aiki da ya saba wa dokokin dabi'u na kwarai wanda shari'ar Ubangiji ta zo da shi kana lafiyayyen hankali da tsarkakakkiyar fidira wacce bata ba ta shafe ta ba ta gano shi. a koyarwar Musulunci, sabo yana nufin barin wajibai da kuma aikata abubuwan da aka haramta, sannan da barin ayyukan alheri da aikata sharri da munanan ayyuka.
A wannan zamani namu, 'yan'Adam suna fuskan-tar wahalhalu masu tsanani, saboda nuna halin ko-in-kula da suka yi dangane da abubuwan da suke hara-mun. A saboda haka ne ma, gwamnatoci daban-daban suka ba da muhimmanci mai girman gaske wajen yaki da laifuffuka da munanan ayyuka, ta hanyar amfani da duk wani karfin kimiyya da na dan'Adam da suke da shi wajen gyara al'umma don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jama'a da kuma kasa baki daya. Bugu da kari kan samar da kyakkyawan yanayi na ci gaban al'umma. To amma duk da wannan kokari da suke yi wajen fada da munanan ayyuka, ba su sami nasarar kawar da laifuffuka da munanan ayyuka ba, face ma dai sai ci gaba suke yi.
Wadannan shirye-shirye da tsarurruka na gyara, ba su sami nasara ba ne saboda tsara su ne ba tare da la'akari da dokokin Ubangiji ba. Wadannan ka'idoji, mahanga da tsarurruka da wadan-nan gwamnatoci suka dauka a matsayin mahangar tsare-tsarensu na yaki da miyagun laifuffuka sun samo asali ne daga akidar da ta yi nisa da Ubangiji.
A dalilin haka, dukkan kwararrun wajajen bincike, dakunan kimiyya da kuma kungiyoyin fada da miya-gun laifuffuka suka gagara aikata wani abin a-zo-a-gani, don kuwa sun gagara fahimtar amfani da tasirin dokokin Ubangiji. Hakika da sun bukaci taimako daga dimbin ilimin Ubangiji kana suka yi amfani da hankali da kuwa sun gano mafita daga da yawa daga cikin matsalolinsu.
No comments:
Post a Comment