Wednesday, 28 May 2014

AIKI A KARKASHIN HUKUMA AZZALUMA


AIKI A HUKUMA
Idan har taimakar azzalumai koda da rabin dabino ne, kai hatta ma son wanzuwarsu suna daga mafi tsananin abubuwa da lmamai (AS) suka yi gargadi game da su, to menene hukuncin tarayya da su a cikin hukunci da shiga cikin ayyukansu da rikon ofisoshinsu. Menene kuma hukuncin wadanda suke daga wadanda suka assasa daularsu, ko kuma ya zama cikin rukunan shugabacinsu masu dulmuya cikin karfafa hukumarsu, (domin karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta, da raya barna dukkaninta, da bayyana zalunci da fasadi) kamar yadda ya zo a Hadisi a "Tuhaful Uku1" daga Imam Sadik (AS).
Sai dai kuma halaccin aiki a karkashin azzalumi ya zo daga gare su (AS) idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Ya zo a ruwaya cewa "Allah yana da wadanda ya haskaka hujjoji da su, ya ba su iko a kasashe a kofofin azzalumai, da su ne yake kare waliyyanSa, ya kuma gyara al'amuran musulmi da su, wadannan su ne muminai na hakika, su ne manarorin Allah a bayan kasa, su hasken Allah ne a cikin bayinsa". Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Imam Musa Bin Ja'afar (AS). A wannan Babin akwai hadisai da dama da suke bayyana tafarkin da ya kamata masu rike ofis da ma'aikata su gudanar da ayyukansu a kai, kamar abin da ya zo a wasikar Imam Sadik (AS) zuwa ga Najjashi Shugaban Ahwaz .

Umarni Da Kyakkyawa, Hani Ga Mummuna
Suna daga cikin farillai kuma mafiya daukakarsu, kuma da su ne ake tsayar da farillai, kuma wajabcinsu yana daga cikin larura na addini, hakika littafi mai girma da hadisai madaukaka sun kwadaitar a kansu, da mabanbantan lafuzza.
Allah (S.W.T) ya ce: "Lalle ne wata al'umma daga cikinku ta kasance mai kira zuwa ga alheri, mai yin umarni da kyakkyawa kuma mai yin hani ga mummuna, kuma wadannan su ne masu rabauta". Ali Imran: Aya 104.
Allah (S.W.T) ya ce: "Kun kasance mafificiyar al'umma da aka fitar wa mutane, kuna horo da kyakkyawa kuma kuna hani ga mummuna, kuma kuna yin imani da Allah". Ali imran: aya 110.

An karbo daga Manzo (S.A.W) cewa: "Al'ummata ba zata gushe a cikin alheri ba mutukar sun yi horo da kyakkyawa kuma sun yi hani ga mummuna, kuma sun yi taimakekeniya a kan aikin biyayya (ga Allah), idan kuwa ba su aikata haka ba, za a debe musu albarku, kuma a sallada sashinsu a kan sashi, kuma ba zasu samu mai ceto a doron kasa ba, ko a sama".
An karbo daga imam Ali (A.S) cewa ya yi huduba wata rana, sai ya yi godiya ga Allah kuma ya yabe shi, sannan ya ce: "Amma bayan haka, kadai abin da ya hallaka wadanda suka gabace ku shi ne; yayin da suka aikata sabo sai malamai masana Allah da masu bauta ba su hana su ba, hakika yayin da suka zurfafa a cikin sabo kuma malamai masana Allah da masu bauta ba su hana su ba sai ukubobi suka sauka a kansu, ku yi horo da kyakkyawa ku yi hani ga mummuna, ku sani cewa, lalle horo da kyakkyawa da hani ga mummuna ba su taba, kuma ba zasu taba kusanto da ajali ba, sannan ba su taba, kuma ba za su taba yanke arziki ba".

Umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, wajabcinsu na isarwa ne idan wasu suka tsayar da su, to ya sauka daga kan kowa.
Da aiwatar da wata farilla ko kawar da wani mummuna daga al'umma ya hau kan wasu gungun mutane, to wajabcin ba ya saraya don wasu sun yi aiki da shi, kuma ya wajaba a hadu a kan wannan gwargwadon iko.
Wajibi ne mai umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ya kassance ya san cewa abin da baligi ya bari ko ya aikata kyakkyawa ne ko mummuna, don haka umarni da kyakkyawa da hani da mummuna bai wajaba ga wanda ya jahilce su ba.
Ya wajaba ga wanda yake son yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, ya yi tsammanin tasirin yin hakan, da zai san ko ya yi tsammanin rashin tasirinsu, bai wajaba ya yi umarni ko hani ba.

Wajibi ne yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna idan mai sabon ya ci gaba da yi, duk sadda aka san ya daina, wajabcin ya saraya.
Da zai sani ko ya yi tsammani mai karfi cewa; a cikin yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna akwai hadari ga rayuwarsa, ko mutuncinsa, ko rayukan mumunai, ko dukiyar su, ya haramta ya yi hanin, sai in ya kasance umarnin da hanin suna daga cikin lamuran da shari'a mai tsarki take ba su mihimmanci, kamar kiyaye rayukan wasu kabilu daga musulmi, da keta alfarmarsu, ko shafe alamomin musulunci, da shafe hujjarsa, ta yadda zai kai ga bacewar musulmi, ko shafe sashin alamomin musulunci, kamar dakin Allah mai girma, ta yadda za a shafe alamominsa, a nan babu makawa a lura da mafi muhimmanci.
Da wata bidi'a zata auku a musulunci kuma yin shirun malaman addini, ya kasance zai kai ga keta alfarmar musulunci, da raunana akidar musulmai, to ya wajaba garesu su musa ta, ta kowace irin hanya, shin musantawar zata yi tasiri a wajen tsige barnar ko kuwa.
Umarni da kaykykyawa da hani ga mumuna suna da matakai, wanda ya fara daga zuciya, zuwa harshe, sannan aiki, ta yadda ya wajaba a yi aiki da su bisa matakai, ta yadda idan matakin farko ya isar don yin umarni ko hani, ba zai yi amfani da martaba ta baya ba.
Musantawa ta zuci ita ce ya yi wani aiki da zai nuna damuwarsa daga cikin zuciyarsa ga mummunan aikin, kamar runtse ido, da murtukewa, da kauracewa, da kin yin mu'amala da shi, da makamancin wannan.
Haramun ne yarda da munkari da kuma barin kyakkyawa.
Da zai san cewa abin neman ba zai samu ta hanyar matakin farko ba, ya wajaba ya ciratu zuwa mataki na biyu, idan ya yi tsammanin cin nasara da dadadan kalmomi, to bai halatta ba ya kausasa magana. Idan kuwa gusar da mummuna da tsayar da kyakkyawa ya tsayu a kan kausasa magana da tsanantawa a cikin umarni da tsoratarwa a cikin hani, ya halatta a yi hakan.

Idan ya san cewa ko kuma ya nutsu da cewa ba za a cimma buri ta hanyar martabobi biyu da suka gabata ba, wajibi ne ya ciratu zuwa ta uku, shi ne: yin amfani da iko yana mai kiyaye mafi sauki sannan mafi sauki.
Bai halatta ba ga mai horo da kyakkyawa da hani ga mummuna ya aikata zunubi ko wani kuskure, kamar alfasha da karya da wulakanci.
Ya kamata mai horo da mai hani su kasance a cikin horonsu da haninsu kamar likita ne mai yi wa maras lafiya magani, kamar uba mai tausayi wanda yake kare maslahar wanda yake aikata sabo, kuma ya yi nufin yin hakan don Allah da neman yardarsa, kuma ya tsarkake aikinsa daga son rai, da kuma neman girma.
Yana daga cikin mafi daukakar nau'o'in horo da hani mutum a kankansa ya kasance wanda ya dabi'antu da kyawawan halaye madaukaka, yana mai aiki da mafifitan halaye, kuma wanda yake barin kaskantattun ayyuka, ta yadda rayuwarsa zata zama abin koyi ga wasu, kamar yadda Imam Sadik yake cewa: "Ku kasance masu kira tare da yin shiru".

No comments:

Post a Comment