Sunday, 25 May 2014

SUNA MUSUNTA AMMA LITTAFINSU YA TABBATAR DA ITA.


Suna Musun Ta Amma Littattafansu Suna Kawo Ta
Wanda ya karanta maganar masu musantawa koyarwar Ahlul baiti (A.S) a game da mas’alar Raja’a sai ya dauka cewa ba su da wannan a cikin littattafansu da akidunsu, sai dai wanda ya karanta wadannan littattafai nasu zai sami da yawa daga ruwayoyi da suke nuna samuwar wanann akida gun Ahlussunna.
Yana daga tabbataccen abu da ya zo a littattafan tarihin musulunci game da labarin wafatin Annabi (S.A.W) yayin da ya yadu tsakanin mutane sai Umar dan Khaddabi ya ce: Manzon Allah bai mutu ba har sai mun ci ta (Rum) da yaki, wallahi zai dawo kuma sai ya yanke hannaye da kafafun wasu mutane da suke rayawa cewa ya rasu[21].
A kan haka Umar dan Khaddabi yana zama farkon wanda ya zo da Raja’a a cikin musulunci ba Abdullahi dan Saba’a da aka kirkiro tatsuniyarsa ba, da ake danganta masa duk wani aibi a tarihi.

Ibn Abidduniya ya mutu (281.H.) ya wallafa littafi da sunan “Man asha ba’adal mauti” wannan littafin Darul Kutub ya buga shi a Bairot a shekara ta 1987.M.
Abu Na’im Al’asfahani ya kebanci wani babi a littafinsa “Dala’ilun nubuwwa” na mu’ujizar Annabi (S.A.W) da kuma raya matattu, haka ma Suyudi ya ambaci karamomin wasu wadanda ba annabawa ba na raya matattu [22].
Sun rawaito daga Zidu dan Harisa da Rabi’i dan Kharashi da wani mutum daga ansar da suka yi magana bayan mutuwa[23].

Tambaya Game Da Akidar Raja’a
Akidar Raja’a tana fuskantar tambayoyi da suke neman amsa gamsasshiya kamar haka:
1- Akidar Raja’a tana kai mutum ga yin sabo dogaro da cewa idan an tashe shi ya tuba?
Amsa: Wannan tambayar zai zama daidai ce idan da Raja’a ta shafi kowa ne ko kuma an ayyana sunayen mutanen da zasu samu dawowa, amma al’amarin ba haka yake ba domin Raja’a ta shafi shugabannin kafirci da imani ne kuma ba wanda ya isa ya ayyana su da sunayensu al’amarin duka yana hannun Allah ne, wannan kuwa ya isa ya sanya rashin kwadaitar da mutum ya yi sabon.
2- Akidar Raja’a tana kai musulmi ga akidar tanasuhi wanda yake bataccen lamari ne gun dukkan musulmi?
Amsa: Tanasuhi wani abu ne da ya saba da Raja’a gaba daya, tanasuhi yana nufin rayukan matattu su shiga wani jiki da zai ci gaba da rayuwa, yayin da Raja’a take nufin dawowar rayukan wasu mutane zuwa ga jikinsu kamar yadda zai faru a lahira, da Raja’a tana nufin tanasuhi da tashin kiyama a lahira shi ma yana nufin tanasuhi, haka ma raya matattu a hannun Isa (A.S) da abin da ya faru na Raja’a a al’ummun da suka rigaya.
Hadisai mutawatirai sun zo daga imamai (A.S) game da bacin tanasuhi, kuma malaman imamiyya na da, da na yanzu sun karfafa hakan, kuma sun ce yana kai wa ga kafirci. Kuma Abul Hasan Ash’ari: a littafinsa Makalatul islamiyyin ya bayyana fadin imamiyya ga Raja’a da kuma bambancinsa da tansuhi da gullat da zindikai masu musun ashin kiyama suka tafi a kai [24].
3- Wasu masu sukan suka ce: Akidar Raja’a ta bayyyana da bayyanar yahudanci a cikin shi’anci, wannan shi ne abin da (makiyin shi’a) Ahmad Amin ya fadi a littafinsa “Fajarul islam”.

Amsa: Bayyanar wasu akidu na wasu addinai da suka rigaya a cikin addinin musulunci al’amari ne da musulunci ya tabbatar da shi, domin musulunci ya shafe wasu ayyuka ne na addinan da suka gabata, amma janibin akida to akwai da yawa daga inda aka yi tarayya a ciki tsakanin addinai, musulunci shi ne yake dauke da bayanin abin da suka kunsa gaba daya, kasancewar wata akida da ta rigaya ta bayyana a cikin akidar musulunci ba aibi ba ne a musulunci, kuma wannan amsar idan an kaddara cewa da gaske ne cewa Raja’a ra’ayi ne na yahudawa kamar yadda wancan marubuci yake fada.
Akidar tauhidi da annabta, da tashin kiyama da hisabi, da aljanna da wuta, duk akidu ne da aka yi tarayya tsakanin addinan sama gaba dayansu, wata akida tana zama aibi ne idan aka aro ta daga akida batacciya da yahudawa ko kirista suke da ita a addinansu.
Raja’a ba ta cikin irin wadannan domin ita abu ce wacce Kur’ani a ayoyi masu yawa ya yi magana game da ita kamar yadda muka kawo bayani da misalai a baya.
4- Yaya za a yi imani da Raja’a ya hadu da fadin Allah (S.W.T): “Hananne ne ga wata alkarya da muka halakar cewa su ba sa dawowa” [25]. Wannan aya tana nuna rashin dawowar azzalumai, idan kuka ce wasu zasu dawo to wannan ya saba wa aya mai girma?
Amsa: Fadin Raja’a baya saba wa wannan aya, domin ita wanann aya tana magana ne game da wani nau’i na azzalumai, wadanda aka halarkar da azaba ta wannan duniya, suka samu azabar sama, amma azzalumai da suka mutu suka bar duniya babu wata ukuba ba wani bala’i aya ba ta maganarsu, shi ya sa ma wannan shirun na aya game da su yana nuna mana wani nau’i na tabbatar wa ga akidar Raja’a, ko dawowar wasu daga cikinsu daga wadanda Allah ya zaba daga ciki.

Natijar Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice
Raja’a ba mustahili ba ce ita a kan kanta, ba ta saba wa tauhidi ba, kai tana ma nuna kudura da ikon Allah ne, ta wani bangaren misalai da dama sun faru a aikace kuma Kur’ani mai girma ya yi maganarsu, kamar yadda malaman musulunci suka yi imani da dawowar wasu daga matattu zuwa duniya bayan sun mutu.
Abu na uku; hadisai da dama sun zo daga Ahlul baiti (A.S), ita Raja’a wani abu ne daga cikin alamomin tashin kiyama, ita kamar nau’in tashin kiyama ne da kafirai suke ganin ba zai yiwu ba, hada da cewa ba ta cikin usuluddin da addini ko mazhaba suka doru a kansu.
24. Makalatul Islamiyyin 1\114.
25. Anbiya: 95.

No comments:

Post a Comment