An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Monday, 26 May 2014
TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)_
__________________(45)___________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halasta musulmi ya ba da zakka ga wanda ba musulmi ba?
SHAIKH ZAKZAKY: Eh! Ta fuskacin jawo hankalinsa ya shiga Musulunci. Shi ne wanda a nassin Alkur'ani ana ce masa "Mu'allafati kulubuhum" wato wanda ake jan hankalinsu, ana iya ba su zakka. Ta wannan unwanin kawai. Wato ta fuskacin jawo hankalinsa ya ga kyawun Musulunci, da fatan ya musulunta.
Amma in ba ta wannan fuskar ba, mujarradin kawai a ba shi ne kawai, to ba zai halatta ba.
___________________(46)__________________
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Meye hukuncin masu biyan wasu suna rubuta masu jarabawar gaba da sakandare, don su sun manta da karatun saboda sun wuce wannan 'level' din?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba zai halatta ba, saboda wannan ya zama tamkar yaudara kenan. In dai har za a ba ka takardar shaida cewa ka ci jarabawa, to wanda duk ya ga takardar, abin da ya fahimta shi ne kai ka rubuta jarabawar
ka ci.
Saboda haka in har ma za a ba ka aiki bisa la'akari da cewa wannan kai ka
rubuta jabawar ka ci, saboda haka nan ne ma aka dauka ka iya aikin aka ba ka,
aka kuma biya ka lada.
Saboda haka in ka sami wannan aikin da takardar shaida ta jabu, to zai zama abin da ake ba ka ma zai yiwu ya haramta maka. Wannan kamar cin amana ne.
___________________(47)__________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halasta musulmi ya sayi bidiyo da talabijin don ya rika kallo?
SHAIKH ZAKZAKY: Kallo dai, mujarradin kallo, ba shi ne zai zama haramun ba, amma a cikin abubuwan da ake kallo din akwai haram da halas.
Saboda haka abin da ya halatta ka kalla ne kawai za ka kalla. Kuma abin da ya haramta ka kalla ba za ka kalla ba.
___________________(48)__________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan wanda ba musulmi ba ya yi wa musulmi sallama, wace amsa zai ba shi?
SHAIKH ZAKZAKY: To masana fikihu suna cewa ya ba shi amsa wadda shi zai
gamsu dai an ba shi amsa, amma ba irin
wadda zai yi wa dan uwansa musulmi ba.
Alal misali, ba zai ce "wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu" ba. Sai ya yi masa raddi da 'alaikum' ko 'wa alaikum'ko kuma wata kalma mai ma'ana, kamar 'yawwa, madalla, eh, muna lafiya ko barka ka dai,' da abin da
ya yi kama da haka nan.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment