Saturday, 31 May 2014

TARIHIN SHEKH MAHMUD GUMI

An haifi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi (R.A) ne a cikin garin Gumi a Jahar Sakkwato a Arewacin Nijeriya, a shekara ta 1340 bayan Hijira dai dai da shekarar Miladiyya 1922.

Mallam ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya da natsuwa da tsafta da neman Ilimi karkashin kulawar mahaifin sa (Alkalin Gumi a wancan zamanin). Kuma yayi karance-karance na zaure a majalisi daban-daban na Malaman da suka shahara anan kasar Hausa a wancan lokaci, tare da karatu na nizamiyya daga nan kasar har kasar Sudan da kasar Saudi Arabiya.

Shaikh Abubakar Gumi mutum ne mai kokarin binciken Al-kurani da Sunna kan hukunce-hukuncen Shari’a, tun daga abin daya shafi Tauhidi, Hadisi, Fikhu da luggar Larabci, wanda karantarwar da yayi ta tabbatar da haka.

Muna fatan Allah (SWT) cikin Rahamar Sa yayi gafara da jin kai da daukaka ga wannan bawa na sa, wanda ya jaddada Da’wah ta Sunna a wannan kasa mai albarka, tun bayan wafatin Shaikh Usman Dan Fodio (RH).

No comments:

Post a Comment