Wednesday, 28 May 2014

HAWAN HUKUNCI A KAN BALIGI


HAWAN HUKUNCI AKAN BALIGI
Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Kuma mun yi imani cewa: Babu makawa Allah madaukaki ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari’o’in abin da yake na maslaharsu da alherinsu da rabautarsu ta har abada, ya kuma gargade su ga barin abin da yake akwai barna da cutuwa a kansu da mummunan karshe gare su, ko da kuwa ya san cewa su ba zasu bi Shi ba, domin wannan tausasawa ce da kuma rahama ga bayinSa domin su suna jahiltar mafi yawancin maslaharsu da hanyoyin samunta a nan duniya da kuma lahira. Suna kuma jahiltar da yawan abubuwan da zasu jawo musu cutarwa da tabewa, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai, kuma Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa da yake mustahili ne ya rabu da shi har abada.
Ba ya janye wannan tausasawa da wannan rahama domin kasancewar bayinsa sun bujire wa bin sa, sun ki bin abubuwan da ya yi umarni da abubuwan da ya hana.

No comments:

Post a Comment