Monday, 26 May 2014

GAME DA BAI'AR IMAM ALI (a.s)


Game Da Bai’ar Imam Ali (A.S) Ga Halifofi Uku
Sun kawo matsalar cewa imam Ali (A.S) ya yi wa halifofi uku bai’a, suka raya cewa wannan bai’ar kuma ba zai yiwu a ce domin maslaha ya yi ta ba, ko domin takiyya, ko tilastawa, domin wannan yana nuna tauye matsayi na imam Ali (A.S). Amsar da zamu bayar ita ce: Game da tilasta shi wannan abu ne a fili, da masu tarihi suka rawaito.
Buhari yana cewa: “Ali (A.S) ya ki yin bai’a ga Abubakar tsawon wata shida har sai da Fadima (A.S) ta rasu” [105]. A hadubar imam Ali (A.S) ya fadi dalilin da ya sa ya yi bai’a, a hudubarsa da yake cewa:

A- “Na rantse da Allah ba domin tsoron rarraba ba, kafirci ya dawo, addini ya rushe, da mun kawar da wannan jagoranci, amma sai muka yi hakuri a kan wasu zogi da bakin ciki da yake damun mu” [106].

B- Yana fada a Nahajul Balaga: “Sai na duba, sai ga shi ba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) sai na yi wa mutuwa rowarsu, na kuma runtse idanuna a kan wannan kwantsa, na yi himmar hadiyar bakin ciki, na yi hakuri a kan juriya da kuma hakurin dacin da ya fi na madaci” [107].
Shin zai yiwu a zo da wani bayani wanda ya fi wannan zama karara?! In ba haka ba menene ya sa duk wannan bayan irin wannan kokawa da kai kara? alhalin shi ne mafi sanin mutane da halin da ake ciki da sakamakon abin da ya faru.
Da a ce bai kafa musu hujja ba ya baro janazar Manzo (S.A.W) ya tafi Sakifa ya bar jikin masoyinsa (S.A.W) bai wanke shi ba, ya zo ya dora hannunsa a kan hannunsu ya yi bai’a da ba ma’ana ya zo da irin wannan kafa hujja. Idan ya tabbata ta hanya sahihiya Ali dan Abi Dalib (A.S) cewa ya soki nazarin shura ya kuma shelanta cewa ta saba wa shari’a… ya kuma fadi cewa an tilasta shi ne ya yi bai’a ga halifofi uku to bai’arsa ba ta da wani dalili na shari’a a kan halifancinsu kamar yadda wannan ya tabbata a fili daga maganganunsa.
Sannan ya bayyana cewa shi ne ya fi cancanta da halifanci, shin zai yiwu mu ce cancantarsa ga halifanci tana nufin shi ya fi, da ma’anar cewa duk da shi ne ya fi amma da waninsa zai karbi halifanci da ba komai? ko kuwa tana nufin shi ne kawai ya cancanta da halifanci?
Wannan ra’ayi na farko ba daidai ba ne saboda nassin hadisai da kuma maganganun imam Ali (A.S) yayin da yake cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar alhalin ni ne na cancanci in sanya rigata wannan (wato in yi halifanci) daga garesu”. Wannan yana nufin cancantar da ta kebanta da shi, ba wai yana nufin fifikon cancanta ba ta yadda wani ma yana iya cancanta da ita, domin ba ma’anar ya ce rigarsa ce sannan ya zama ba ya nufin cancanta, domin mai riga shi ne mai ita mai cancanta da ita mai mallakarta.
Sannan ga fadinsa da yake cewa: “…Na zama ina mai kai-kawon ko ina tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu, da babba yake tsufa a cikinsa yaro kuma yake girma a ciki, mumini yake shan bakar wahala a ciki har sai ya riski Ubangijinsa.
Sai na ga hakuri a kan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa” [108].
Ma’anarsa sai na samu kaina tsakanin ko in karba da karfin da bai isa ba kamar yadda ya zo a fadarsa (A.S): “Sai na duba, sai ga ba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) sai na yi wa mutuwa rowarsu”. Wato da ya sami karfi isasshe da ya yaki ma’abota Sakifa kamar yadda yake a maganarsa da aka sani da yake cewa: “Da na samu mutum arba’in masu niyya da gaskiya da na kawar da mutunen”.
Wannan mataki na imam Ali (A.S) ba yadda za a fassara shi da ma’anar ya fi cancanta da ma’anar wani ma yana iya rikon jagoranci, wannan a fili yake cewa ya yi daidai da ma’ana ce ta cancantar kebantaka da shi. Hakanan fadinsa (A.S): “Ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu…”. Ma’anarsa abin da ya faru ba kawai kwacen mulki ba ne, sai dai wannan yana zama farkon faruwar canji ne da zai iya kai al’umma ga bata, Shi ya sa ya karfafa wa mutane bayan kashe Usman dan Affan yayin da suka zo domin yi masa bai’a: “Ku rabu da ni ku nemi wanina domin tafarki ya bice hujja kuma an yi musun ta” [109], da fadinsa garesu: “Ni ina ji muku tsoro ne ku kasance cikin wani yanayi na lokaci, alhalin da can wadansu al’amura sun faru sun wuce da kuka karkata zuwa garesu karkatar da kuka zamo ba abin yabo ba ne ku a guna” [110].105.

 Sahihul Buhari: 5\288 Da Tarihin Tabari: 2\234.
106. Nahajussa’ada: 1\248 Na Shaikh Mahmudi.
107. Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 68, Huduba 26.
108. Biharul Anwar: 28\313, Daga Ibn Abil Hadid: 10\151.
109. Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 136, Huduba 92.
110. Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 2\256, Huduba 178, da Shubahtun wa Rudud: 3\47.

No comments:

Post a Comment