TANBAYA: Da watan azumi na ji a cikin wa'azi an ce duk wanda ya yi wa Allah laifi kuma yake neman gafarar Allah, to ya yi tuba gami da tawassuli da Imam Aliyu Ridah (AS). Don haka nan sai na ci gaba da yin tawassuli da Imam din. Shin ina iya in ci gaba da yi?
SHAIKH ZAKZAKY: To (shi dai) tawassuli ba a kayyade shi da wani Imami kebantacce ba. Tawassuli dai yana nufin kana rokon Allah ne kana gama shi da bayin Allah nagargaru.
___________________(132)_________________
TAMBAYA: Ina tambaya ne game da falalar zikiri kamar yadda ya zo a Arba'una Hadith na Imam Khomaini. Shin falalar ta takaita ne ga wanda ya yi zikirin Khasatan ko har da wanda ya yi don neman biyan bukata?
SHAIKH ZAKZAKY: Shi dai zikiri yana nufin tuna Allah ne sabanin gafala ga barinsa. Kuma jimlar abubuwan da suka shiga duk tuna Allah, sun shiga cikin zikr, musamman salla da karatun Alkur'ani da addu'o'i da tasbihohi da tahmidodi da sauransu.
Saboda haka in mutum yana da wata bukata wajen Allah, ya gabatar da sallah sannan ya yi wata addu'a ta neman biyan bukatarsa, shi ma zikr ne. Kuma addu'ar ma in mutum ya roki Allah ya ba shi wani abu, ko ma wannan abin na duniya ne mutukar bai haramta a bidi wannan abin ba, shi ma ya yi zikr ne ai.
___________________(133)_________________
TAMBAYA: Abu ne ya shiga tsakanin Uba da 'yarsa har ya kai matsayin ga ya tsine mata, kuma har ya ce ko ya mutu kada a ba ta gadonsa. To idan ya mutu shi kenan gadon ya haramta a gare ta ko kuwa?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai matukar 'yarsa ce, wannan rabo ne da Allah (T) ya riga ya yi. Saboda haka tana da gadonta, shi bai isa ya fitar da ita daga gadon ba.
Gado Allah (T) ne ya raba ba iyaye ne suke rabawa ba.
___________________(134)_________________
TAMBAYA: Ya matsayin azumin mai ciwon ULCER? Zai ciyar ne ko zai rama idan azumin ya warke?
SHAIKH ZAKZAKY: Da ma ramuwa zai yi sai dai idan ciwon ya zarce da shi har ya zuwa wani azumi ba tare da ya warke ba, ko kuma ba a sa tsammanin ma wani Ramadan ya zo alhali yana da lafiya. Wato ana tsammanin ci gaban ciwon, an tabbatar da haka nan, to sannan zai koma ma tun asali ya zama ciyarwa maimakon ramuwa.
Amma abin sani shi ne mai ciwo yana biya ne in ya warke; in kuma Ramadan ya sake cimmasa ba ta tare da ya warke ba, shi kenan ramuwa ta fadi a kansa sai ya koma ga ciyarwa.
___________________(135)_________________
TAMBAYA: Meye hukuncin sukuwar dawaki wanda akan sa wata kyauta ga wanda ya yi na daya?
SHAIKH ZAKZAKY: To in dai shi bai sa kudi ba, shi wanda ya shiga takarar, to ya halasta. Amma in su masu takarar ne suka zuba kudi, dayansu ya ci, to ta zama caca.
___________________(136)_________________
TAMBAYA: Muna so a taimaka mana da hakikanin fassarar ayar nan da take cewa; "mazinaci ba ya aure face mazinaciya, haka mazinaciya ba ta aure face mazinaci" Har ya zuwa karshen ayar.
SHAIKH ZAKZAKY: Eh, to aure a nan ya zo da ma'anarsa ne na luga, wato ainihin zinar ake nufi kenan. Wato saduwar namiji da mace shi ne aka kira aure.
Wato ka ga shi mazinaci ba zai yi jima'I da wata ba ta fuskacin zinarsa in ba ita ma irinsa ce mazinaciya ba. Haka nan kuma ita ma mazinaciya ba za ta sami wanda za ta iya yin zina da shi ba sai dan uwanta mai ra'ayi irin nata, mazinaci.
Wato aure a lugga yana nufin shigar wani abu a wani abu ne. Kuma a wannan ma'anar aka yi amfani da shi a nan.
_________________(137)___________________
TAMBAYA: Batun ayar da ta hana Bani Isra'ila kamun kifi ranar Asabar. Shin har yanzu wannan ayar tana aiki?
SHAIKH ZAKZAKY: To duk shari'o'in Manzannin da suka gabata, shari'ar wannan Manzo namu ya riga ya shafe ta.
Saboda haka in dai Ba'isra'ile yana nan yanzu ko da zai ga sahihiyar Attaurar Musa, in ya bi ba za a karba masa ba saboda an aiko da hukuncin da ya shafe wadancan hukunce-hukunce.
Allahumma sai dai in ba shi da labarin aiko Manzon Allah, to sai ya zama yana kan wannan abin nasa, to za a iya amsa masa. Amma ban sani ba ko akwai wadansu mutane yanzu da suke addinin Yahudu da Nasara alhali ba su da labarin an aiko Manzon Allah, in dai akwai su to suna da hujja. Sai mu ce gare su wannan ayar tana nan tana aiki; in akwai su!
_________________(138)___________________
TAMBAYA: Mahaifin Imam Ali Abi Dalib shi ne sunansa kenan ko alkunyarsa ne?
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai sunansa ne. Kuma dai abin da ya shahara da shi kenan, ba a san ana kiran sa da wani abu ba banda Abu dalib din.
________________(139)____________________
TAMBAYA: Meye hukuncin mutumin da yake shan hannu da abokin kasuwancinsa wanda ba musulmi ba?
SHAIKH ZAKZAKY: In musafaha yake nufi, to ba wani abin da ya hana yin musafaha da wanda yake ba musulmi ba, sai dai idan hannunsa da jibi, zai lizimta wa mutum wanke hannu saboda rashin amintuwa da tsarkakar wannan hannun nasa da ganin cewa su ba su san meye najasa ba da meye mai tsarki ba.
Amma idan hannuwan nasu busassu na guda biyu babu komai.
___________________(140)_________________
TAMBAYA: Ina hukuncin wanda yake sayar da gwanjo sai ya wanke su ya sa masu sitati su yi karfi don jawo hankalin masu saye?
SHAIKH ZAKZAKY: Babu laifi in masu sayen sun fahimci cewa gwanjo suke saye. Sai dai in ya yi masu yaudara, ya nuna masu cewa sababbi ne, kamar ya sa su a cikin leda sai su fito a matsayin sababbi, to shi ne zai zama ya yi yaudara kenan. Amma matukar su masu saye sun san gwanjo suke saye, to babu laifi.
No comments:
Post a Comment