Monday, 26 May 2014

TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

____(84)____________________

TAMBAYA: Ya halasta in yi wa yayan mijina sannu da zuwa lokacin da suka dawo daga aiki?

SHAIKH ZAKZKY: To ina jin mun sha amsa tambaya shigen irin wannan, kamar wani ya ce ko ya halasta ta yi sallama a amsa masa, ko kaza ko kaza?

Akwai magana wadanda ya halasta, wanda ko da a kasuwa ne ko na sayayya da sauransu. Ba inda aka ce in ita matar wani ne ba za ta magana da kowa ba, ban san inda aka sami wannan ba. Sai dai magana wala'alla wanda ya fice kan hanya ne.

Amma dai magana ba in da aka ce akwai wani wanda aka ce kar a yi masa magana. Ba wani abu mai kama da haka nan, ballantana har a ce, to wane ana iya ce masa barka da zuwa?

___________________(85)__________________

TAMBAYA: Ina zaune ne a Kaduna, amma garin haihuwata Kano. Shin idan na je ganin gida zan yi kasaru?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, idan yanzu ya tashi a mazaunin Kano, yanzu Kano ya zama masa kamar wani gari, bai da gida a can, bai da iyali a can, ba kuma ya tunanin zai koma da zama can, to ya zama wani gari.

Amma idan yana da gida yana da iyali da iyali ko kuma a'a aiki ne ya kai shi Kaduna, yana tunanin zai koma Kano din, to ya zama mai gari biyu. Saboda haka in ya je Kano zai cika sallah ne.

__________________(86)___________________

TAMBAYA: Ina da mata amma tana kaurace mani wajen kwaciya, shin ya halasta ni ma in hana ta abin da take bukata, kamar abin ci da sauransu?

SHAIKH ZAKZAKY: To, abin da dai aka sani shi ne ciyar da matarka a abin da ake ce ma Isma ya zama wajibi. Wato matukar tana gidanka dole ne ka ciyar da ita. Sai idan ta fita gidan ne ta tafi wani gida, kamar ta koma gidansu, to shi ne wannan ya fadi a kan ka.

Saboda haka matukar tana cikin isma din sa, to lallai shi zai biya ta wajibin da ya hau kansa, shi kuma ya bidi ta ba shi wajibin da ya hau kanta. In ta ki sai ya kai kara ko ya dauki wadansu matakai na neman sulhu, amma ba zai hana mata hakkinta ba.

___________________(87)__________________

TAMBAYA: Mutum ne yana da 'ya ta isa aure amma bai sami wani dan uwa da ya je yana son ta ba. Shin zai iya ba da ita aure ga wanda ba dan uwa ba?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ina fata dai abin da yake nufi dan uwa musulmi ne.

Idan kuwa haka nan ne, ka ga dole sai ya nema mata. Ya yiwu mu a nan kasar ba mu irin hanyoyin sadarwa din nan.

Tana iya yiwuwa rashin sadarwa ne, don lallai akwai gwagware masu yawa wadanda suke bidar aure, kila ba su san akwai wata yarinya wadda take ita ma tana bukatar auren bane.

In aka sami hanyar sadarwa ko da ta tattaunawa da wadansu, insha Allahu za a samu.

Amma dai bai kamata ya aurar da ita ga kowane irin mutum ba sai wanda ya aminta da addininsa.

___________________(88)__________________

TAMBAYA: Akwai wani irin aiki da Kananan Hukumomi suke dauka, ba ka da wani aiki amma duk wata ana biyan ka albashi. Shin yaya matsayin wannan albashin?

SHAIKH ZAKZAKY: Na san in dai ba ainihin wani shiri ne na almundahana da shi mai daukar ka aikin ya yi domin ba ka aikin ka rinka karbar kudi kawai ba, dole zai zamana in dai an dauke ka aiki ne an cika takardu, ko da kuwa ba ka aikin ya zama cewa an hana maka ka yi aiki, domin wani aikin in ya taso.

Amma dai ban san takamaimai abin da yake nufi ba. Illa iyaka dai abin da zan ce shi ne, in da gaske ne akwai wani aiki da za a dauke ka amma ya zama babu aikin
yanzun, amma wata rana yana iya tasowa, yana iya yiwuwa saboda wannan, saboda haka kai ma'aikaci ne ko da ba ka yi aikin ba.

Alal misali, akwai masu kashe gobara sai su yi wata da watanni ba su kashe wata gobara ba, amma ka ga ai an hana su su je su yi wadansu ayyuka kuma ana biyan su albashi. Kuma ana iya ma samun ma'aikaci wanda aka horar da shi ya
zauna ya yi jiran ko-ta-kwana.

Saboda haka ka ga in ana hana shi ya yi wani aiki yanzu ka ga za a biya shi albashi.

Amma idan shi ya fahimci wannan ba irin wannan bane, illa iyaka yaudara ce aka shirya, shi dai kawai an sa sunan sa ne a rinka ba shi kudi, ba wai domin da ma shi ma'aikaci bane, to ya san shi da
wanda ya taimaka masa, lallai abin da suka yi ya saba ka'ida.

Saboda haka ka ga abin da yake karba ba halas dinsa ne. Amma kasantuwar ba ya aiki, amma ma'aikaci ne bai maishe da shi laifi ba.

_______________(89)_________________

TAMBAYA: Akramakallah. Ko Sista za ta iya bude gidan sayar da abinci, kuma ya zama ita za ta sayar da kanta?

SHAIKH ZAKZAKY: To, akwai ka'idodi dai na hulda da mutane, tsakanin maza da mata ne, ko mata ya su-ya-su, ko maza ya-su-ya-su.

Saboda haka abin da za mu ce kawai shi ne wadannan ka'idodin ya kamata ta san su, ya zama su ta kiyaye.

Kamar yadda ya zo cewa; kada dayanku ya aikata aiki sai ya san hukuncin Allah a cikinsa. Saboda haka sai ta san menene haram da halas a sana'ar sayar da abincin.

Amma dai in dai ta yi abinci ne ta sayar, ya halatta. Sai dai dole ta bi ka'idodi. Sai ta nemi sanin menene ka'ida wanda ya shafi wannan aiki khasatan.

_____________________(90)________________

TAMBAYA: Idan an sami irin mummunan hatsarin motan nan, sai ya zamana an kasa tantancewa tsakanin musulmi da kafiri. Ko yaya za a yi?

SHAIKH ZAKZAKY: To ai wannan ya sha ma faruwa, kuma irin shi akan yi masu salla ne a bizne su kuma a makabartar musulmi, ko da za a yi masu rami gaba daya ne. In dai da musulmi a cikinsu, sai ya zama su wadanda suke ba musulmin ba sun raka musulmi din.

Wala'alla yana nufin siffarsu ta caccanza har ba za a iya binne jikin wani ba tare da wani ba. Ko kuma kuna ko abin da ya yi kama da haka nan. Ala ayyi halin, in dai akwai 'ishtibahi' tsakanin musulmi da kafirai, to dole kawai a yi masu daukar su musulmi ne. Har da kafiran.

Saboda haka sai ya zama za a yi masu wanka da likkafani da salla, kuma a bizne su a makabartar musulmi.

Amma wajen sigar salla, sai a yi da nufin musulmin cikinsu ake nufi. Ka ga su wadannan sun zama tamkar wadansu tarkace da suka raka musulmi kabari din.

__________________(91)___________________

TAMBAYA: Mutum ne ya wakilta wani a kan zai sayar masa da babur misali, sai shi wanda aka wakilta din ya samo wanda zai saya, amma ya kara wani abu a kan kudin da shi mai babur din ya ba da sallamin mashin din.

To ko shi ya halasta ya ci wannan abin da ya kara din, duk da cewa kuma mai mashin din zai ba shi wani abu a cikin kudin da ya yi masa sallamin mashin din.

SHAIKH ZAKZAKY: To ya danganta da yadda suka yi sigar cinikin ne. In ya ce masa ga babur dina ka sayar ne, to duk yadda ya sayar kudin mai babur ne. In kuwa tun farko ya ce masa ka sayar kaza, duk abin da ya hau naka ne, sun yi dama dawajewa a haka nan, to wannan kuwa.

Amma in dai ya ce masa ya sayar masa ne kawai, to lalle duk yadda ya sayar, duk kudin na mai babur ne. Shi kuma alabasshi a ba shi lada. Amma bai halatta gare


No comments:

Post a Comment