Saturday, 31 May 2014

MALAMI DA MALUNTA A KASAR HAUSA


1.0 Gabatarwa
A cikin wannan makala za mu yi bayani filla-filla a kan abin da ake nufi da malami, da rabe-raben aikin malami da kuma lakuba da ake kiran malami da su a kasar Hausa. Manufar wannan makala ita ce nuna muhimmanci da kuma martabar da malami yake da shi ko ita a da, da yanzu, da kuma nuna yadda canje-canje na zamani suka shafi matsayin malami da sana'ar malanta a kasar Hausa1.

2.0 Ma'anar Malami
Abin da muke nufi da malami a wannan makala shi ne masanin Alkur'ani Mai girma, da ilmin Furu'a, da shari'ar Musulunci, da na harshen Larabci. Almajiri kuwa, shi ne mai yawon neman ilmi ko sadaka2. A kasar Hausa malami shi ne wanda yake da ilmin addinin Musulunci kuma yake karantar da shi. In malami ne da ilmin addinin Musulunci amma ba ya karantarwa, ya kuma kama sana'a, ba a lissafa shi cikin sahun malamai. Haka nan kuma, in malami ya shagala da neman abin duniya, mutane ba su dubansa da mutunci domin za su dauka ya ci amanar ilmi ke nan. Wani lokaci akan lissafa shi cikin masu bidi'a.

3.0 Sunayen Malamai
A kasar Hausa akwai sunayen iri-iri da ake kiran malami da su. Akwai malamin sunna,3 da malamin bidi'a,4 da malamin tsibbu,5 da sarkin malamai, da malamin malamai, da shehun malami, da kuma waliyyin malami. Ga takaitaccen bayani a kan kowannensu.

3.1 Malamin Sunna:
Shi ne malamin da ke da ilmin addinin Musulunci gwargwado, kuma yana karantar da shi ga jama'a. bugu da kari, yana da takawa da natsuwa da tsentseni da gudun duniya na inna naha. Kuma ga shi ba shi da tsoron fadin gaskiya a kan komai da kowa. Haka kuma, bai damu da fushin wani ba a wajen fadin gaskiya. Ire-iren wadannan na da wuyar samuwa. Amma ana samunsu domin bayin Allah nagari ba su karewa.

3.2 Malamin Bidi'a
Shi ne wanda yake da ilmin addinin Musulunci, kuma yana karantar da shi ga mutane, amma yana da kwadayin abin da ke hannun mutane da kuma tsananin son dukiya a zuciyarsa.

3.3 Malamin Tsibbu
In malami ya shagala da ba maras lafiya magani ta hanyar amfani da ayoyin Alkur'ani Mai Girma, da yin layu, kuma yana bugun kasa don ya fada wa mutane alherin da za su samu ko cutar da za ta same su, to akan kira shi malamin tsibbu6.

3.4 Sarkin Malamai
A wasu wurare cikin kasar Hausa, in malamai na da yawa, sarkin garin yakan nada musu shugaba. Shugaban malamai a gari ko a kasa, shi ne sarkin malamai wanda yake ba dole ne ya zama ya fi dukkan malaman garin ilmi ba. A halin yanzu akwai sarkin malamai a Sakkwato.

3.5 Malamin Malamai
Idan malami ya shahara kwarai da gaske a kan ilmin addinin Musulunci, har wasu malamai da almajirai na zuwa daga nesa saboda neman ilmin a wurinsa, akan kira wannan malami da lakabin 'Malamin Malamai'. Hausawa sun sami wannan suna ne daga Larabawa da ke kiran wasu malamansu da lakabin “Shaykh al-shuyukhi”. Da “Al'allamat”, da faridu dahrihi”. Ana nufi da wadannan lakubba babban malami wanda babu na biyunsa a kasarsa ko a zamaninsa.

3.6 Shehun Malami
Shi ne malamin da ya yi zurfi a cikin ilmin Sufanci da darikun waliyyai magabata. Haka nan kuma, akan kira irin wannan malami da sunan “Malamin darika”. Wani lokaci in malami ya tsufa kwarai har ya ba shekara sittin baya, akan kira shi “Shehun Malami”7.

3.7 Waliyyi
Wani lokaci akan samu malami mai tsananin tsoron Allah da natsuwa da gudun duniya da yawan ibada da ilhami. Har ma in ya yi magana a kan wani abu da zai auku, sai abin ya auku yadda ya ba da labari. Malamai masu irin wadannan siffofi da muka zana, akan yada cewa su waliyyai ne. Abin da ake nufi da waliyyai, shi ne bayin Allah da Allah ke so, wadanda za su shiga Aljanna. Hausawa sun dauka cewa waliyyi yana da ikon nuna karama yadda ya so, kuma a lokacin da ya so. Sun yi imani cewa, waliyyi na iya abin da sauran mutane ba za su iya yi ba, kamar tafiya a kan ruwa ba tare da jirgi ba, ko tafiya wuri mai nisa cikin lokaci kankane, ko kuma rayuwa wata da watanni ba tare da ci da sha ba. Da kuma makamantansu 8.
A kasar Hausa akwai malamai da yawa wadanda suka shahara da walitaka. Mutane da yawa sun dauke su waliyyan Allah ne wadanda za su shiga Aljanna kai-tsaye, ba tare da wahala ba. Daga cikinsu akwai Wali Danmarina,9 da Wali Danmasani,10 da Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo11. Haka nan kuma akwai karamomin iri-iri da aka danganta ga kowannensu.

3.8 Malamin Allo
Malamin da ke karantar da yara Alkur'ani Mai Girma da allo, shi ne ake kira 'Malamin allo'. Sau da yawa malamin allo almajiri ne. Bayan yara sun tashi daga makarantarsa, yakan tafi wajen babban malami wanda ya fi shi sani don daukar ilmi.

3.9 Malamin Zaure 12
Akan kira malamin allo 'Malamin zaure' in ya kasance yana karantar da yara karatun Alkur'ani da allo, kuma yana karantar da manyan littattafai kamar su Lahalari da Ishmawi da Izziyya da Risala.

3.10 Alaramma
Wannan shi ne lakabin malami da ke da sanin Alkur'ani sosai. Asalin kalmar Larabci ce (Allahu Yarhamu ka). Ma'anarta, 'Allah shi rahamshe ka'. Kafin a kira malami alaramma, sai ya haddace Alkur'ani Mai Girma, kuma yana iya rubuta shi da ka, hakanan kuma yana iya bayanin tsari da rabe-raben surorin Alkur'ani da ka.

3.11 Malamin Gafaka
Wannan shi ne malami wanda yake yawo da almajiransa daga wani wuri zuwa wani wuri. Ba shi da sana'ar neman abinci ban da karantar da yara Alkur'ani Mai Girma. Ya dogara ne a kan sadakar da mutane kan ba shi da kuma hidima da almajiransa ke yi masa.

3.12 Ustazu 13
Yanzu Hausawa kan kira mutum 'Ustazu' in sun ga alama cewa yana yin shiga irin ta malamai, kuma yana da ra'ayin rikau game da sha'anin addini, ko da kuwa ba shi da isasshen ilmin Addinin Musulunci. Haka kuma akan kira mutum Ustazu in malami ne shi, amma ba ya son darika, kuma ba ruwansa da ilmin Sufanci. Wani lokaci akan kira irin wannan malami 'Malamin Izala'.

4.0 Aikin Malami
4.1 Karantarwa
Babban aikin malami a kasar Hausa shi ne karantar da mutane addinin Musulunci, Alhakinsa ne ya karantar da mutane Alkur'ani Mai Girma, da Furu'a, da dukkan abin da ya shafi Shari'a. Karantarwa ce ke sa wani lokaci malami ya shahara. Sai sunansa ya kai wurare da dama, kuma almajirai su yi ta zuwa wajensa daga kusa da nesa domin neman ilmi da albarka a wajensa.14

4.2 Wa'azi 15
Wa'azi shi ne kiran mutane zuwa hanyar Allah. Manufar wa'azi shi ne shiryar da mutane yadda ake ibada da zaman lafiya tare da jama'a. Mai wa'azi yakan yi bayanin yadda ake Alwala, da Sallah, da Azumi, da Zakka, da aikin Hajji. Malami mai wa'azi yakan yi albishir ga masu saurarensa. Yakan yi musu albishir da shiga Aljanna in aka yi aikin kwarai a nan duniya. Haka kuma yakan yi gargadi a kan wutar lahira da azabarta wadda Allah Ya tanada wa Fir'auna, da Karuna, da Hamana, da wadanda suka yi aikin assha irin nasu.
A majalisar wa'azi, malami yakan gamu da wautar mutane daban-daban. Wasu sukan halarci wurin wa'azi saboda su kure malamin da tambaya. Wasu kuma sukan zo domin sukan halayen malami mai wa'azi don mutane su watse daga wurin wa'azinsa.16 Wani lokaci akan sami wasu mutane da ke surutu da izgili lokacin da ake wa'azi. Su ba su sauraron wa'azin da ake yi, kuma ba su barin masu saurare su ji abin da ake fadi. Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo ya gamu da ire-iren wadannan abubuwa da muka zana yayin da yake wa'azi a kasar Hausa a cikin karni na goma sha tara na Miladiyya17.


4.3 Talifi
Burin malami shi ne dalibansa su gane abin da yake koya musu. In malami ya gane dalibansa na fama da rashin gane wani littafi saboda tsaurinsa, sai malamin ya yi wa dalibansa sharhi ko bayanin littafin a rubuce don saukin fahimta18.
Saboda haka ne Shehu Usmanu da mukarrabansa suka yi talifi da yawa a kan fannonin addinin Musulunci daban-daban ga jama'ar Musulmi don su gane addini cikin sauki. Kuma ya yi kira ga malaman kowane zamani su yi talifi ga jama'arsu saboda su suka fi sanin matsalolin zamaninsu da na mutanensu19.
Shehu Usmanu ya nuna misali da yin talifi fiye da dari. Haka nan kuma kaninsa Malam Abdullahi Ibn Fodiyo, da kuma dansa Sarkin Musulmi, Muhammadu Bello 20.

4.4 Alkalanci
Babu wanda ya cancanta ya zama alkali sai malami mai tsoron Allah, kuma adali. A kasar Hausa, in aka ga malami yana da takawa da ilmin Shari'a mai zurfi, ga shi kuma adali, akan nada shi alkali. Kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka kasar Hausa 21, mafi yawan sarakunanta malamai ne. Kuma su ne ke alkalanci ga jama'arsu. In aiki ya yi wa sarki yawa ne yake nada wani malami alkali. Zuwan Turawa kasar Hausa ya sa alkalai cikin halin kaka-nika-yi. In sun yanke hukunci a bisa Shari'ar Musulunci, sai Bature ko dan korensa ya soke in ya ga dama. Wannan ya sa yanzu malamai masu tsoron Allah suna guje wa aikin Shari'a. Abin ya kai ga lahaula, har jahilai ne ma ake nadawa alkalai a wasu kotuna yanzu.


4.5 Limanci
Limancin Sallah yana daya daga cikin muhimman ayyukan malami. A kasar Hausa akwai limamai biyu “Limamin Khamsu Salawatu” (Salloli Biyar), da kuma “Limamin Masallacin Jumu'a”. Na farko suna da yawa. Kusan akwai su a kowace unguwa. Na biyu kuwa, sarkin gari, ko hakimi, ko mai unguwa tare da yardar wasu malamai ne ke nada shi. Har ila yau, malami ne ke limancin sallar gawa, da ta Idi, da ta rokon ruwa da ta husufin rana da wata.

4.6 Shawara
Malami mai basira shi ne sarki ke neman shawararsa in yana da matsala. Shi ne kuma babban abokin shawara ga sarki. Saboda haka, a cikin majalisar sarakunan kasar Hausa, akan sami akalla malami guda wanda zai dinga ba da shawara ga sarki a kan al'amuran yau da kullum, da kuma wadanda suka shafi addinin Musulunci.
Wani lokaci akan kira malamai masu ba sarki shawara da “Malaman Fada”. Amma su malaman sun fi son a kira su da sarautar da sarki ya fi ba malamai; wadda ita ce: Waziri, da danmasani, da Sarkin Malamai, da dai makamantansu.

4.7 Rabon Gado
Rabon gado wani babi ne mai wuyar sani a cikin ilmin Furu'a. Amma ga malami mai zurfin sani, abu ne mai sauki. Saboda haka, in magada suka rasa sanin yadda za su raba dukiyar gado a tsakaninsu, sukan nufi malam don ya ilmantar da su a kai, kuma ya raba musu dukiyar gadon, ko kuma a kai wurin alkali.

4.8 Daurin Aure Da Radin Suna Da Saukar Alkuri'ani
In za a daura aure, akan gayyaci malamai su albarkaci taron, da kulla auren, da kuma yin addu'a. Galibi, malamai kan yi wa waliyyansu nasiha a kan hakkokin ma'aura. Kuma sukan roki Allah Ya albarkaci zamansu na aure, da zuriya mai albarka, da 'ya'ya managarta, da kuma yalwar arziki da zaman lafiya. Haka kuma suke yi in an gayyace su wurin radin suna.

4.9 Biyan Bukata
A kasar Hausa, mutane da yawa sun dauka cewa malami yana da tsarkin zuciya da imani fiye da sauran mutane. Saboda haka, sun yi imani Allah ya fi sauraron rokonsa fiye da na wani.
In Allah Ya ba malami ijaba, sai ka ga attajirai, da saraki, da talakawa, da masu sana'o'i iri-iri maza da mata na ta tururuwa zuwa gidansa saboda neman biyan bukata. Wasu tsari suke nema da zai kare su daga sharrin bil'adama da sauran halittun Ubangiji. Matan aure kan so malam ya rokar musu Allah Ya ba su zuriya mai albarka in ba su da da, ko kuma kada Allah Ya ba mazansu ikon yi musu kishiya. Sarakuna sukan nemi addu'ar malami, Allah Ya kare su da jama'arsu daga sharrin abokan gabansu, ya kuma ba su lafiya da zaman lafiya da damina mai albarka. Attajiri yakan je wajen malami don neman tsari da karin arziki. A takaice dai, ba jinsin mutane da ba su zuwa wajen malami saboda wata bukata.

5.0 Matsayin Malami A Yau
A yau an samu sauyi sosai game da aikace-aikacen malami a kasar Hausa. Saboda huldar al'ummar Hausawa da Turawan Mulkin Mallaka da wasu kabilu daban-daban a cikin kasarsu da wajenta. Matsayin malami ya bambanta da yadda aka sani da can karni biyu da suka wuce.
A halin yanzu, an fara samun malamai a kasar Hausa masu ba da taimako ga 'yan fashi da barayi, da 'yan daudu da karuwai. Haka nan kuma, yanzu ana samun malamai masu zaman bauta ga masu hannu-da-shuni. Sai mai hali ya gina katon gida da masallaci da makaranta da gidan yara. Sai ya sa malami a gidan yara yana ciyar da shi da iyalansa. Shi kuma malamin yana karantar da yaran mai gida da matansa ilmin addini, kuma yana ba da sallah a cikin masallacin gida. In mai gidan mai hali ne sosai, sai ya biya wa malamin kujerar Hajji. Amma abin ban haushi shi ne, ranar da malamin ya yi wa mai gidan laifi, sai mai gidan ya kore shi daga gidansa korar kare.

6.0 Kammalawa
A cikin wannan makala mun yi bayani a kan malami a kasar Hausa. Mun tattauna abubuwa da yawa a kan sunayensa, da aikace-aikacensa, da kuma matsayinsa a cikin jama'a a da, da kuma yanzu. Babu shakka, wanda ya yi tsokaci a kan abubuwan da muka fada, zai gane cewa, ba karamin matsayi ne malami yake a cikin al'ummar Hausawa ba. Saboda muhimmancinsa, an dauke shi kamar gishiri ne ga miya. Da shi jama'a ke zama salihai. In kuma sun lalace (Allah Ya kiyaye). Jama'a sun shiga uku. Abin farin ciki kuma shi ne ba ga mutane kawai malami ke da daraja ba. Malamai masu aiki da ilminsu na da daraja a wajen Mahaliccinsu Allah har ma ya ce: “Masu tsoron Allah cikin bayanisa, su ne malamai”22. A wajen Manzo Allah ma, malamai masu daraja ne har ma ya ce game da su: “Malamai su ne magadan Annabawa”23. A kasar Hausa kuwa, in an kira sarki, sai a kira limaminsa.
Ina fata malamanmu za su ci gaba da yi mana jagora zuwa ga tafarkin tsira. Allah ya sa, amin.

TUSHEN BAYANI
1. Ka dubi The Hausa Factor in West Afircan History Mahadi Adamu, Ahmadu Bello University      Pres Zaira, 1978, saboda karin bayani a kan kasar Hausa da iyakarta.
2. Ka karanta: Islam in Nigeria A.R Doi, saboda karin bayani a kan yaduwar Musulunci a kasar Hausa, shafi na 307-333.
3. Ma'anar kalmar “Sunna” na da yawa. Ka dubi littafin da ake kira Al-Sunnat Wa Ma'anatuha Fil Islam, na likita Mustafa Alsiba'i, shafi na 45-74.
4. Ka karanta rabe-raben bidi'a a cikin Ihya'u Sunna na Shehu Usmanu Danfodiyo, shafi na 22-28, bugu na Misra wanda Sardauna Sir. Ahmadu Bello ya dauki nauyin bugawa, 1963 a Misra.
5. Asalin kalmar “Tsibbu” daga Larabci ne “Tibbu” (magani).
6. Wani lokaci akan kira malamin tsibbu, “Gobe-da-nisa” in yana ba da maganin kisan mutum.
7. Dubi kamus da ake kira, Al-Munjid Fil Lugati Wal A’lami, bugu na 21, wanda aka yi a Lebanon a 1973, shafi na 41.
8. Ka dubi Lamma Balagtu” na Shehu Usmanu Danfodiyo, za ka ga irin karamomi da Allah Ya ba shi a shafi na 14-17. bugu na madaba'ar Amiriya da ke kano.
9. Akwai labarin tarihin wali Danmarina a cikin littafin Ibrahim Yaro Yahaya Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa NNPC Zaria, 1988, shafi na 36.
10. Ka dubi Hausa A Rubuce, shafi na 37.
11. Ka dubi Hausa A Rubuce, shafi na 49.
12. Ka dubi makalar Mahmud Inuwa mai take “Malaman Zaure: A Legacy of Western Colonial Education System In Northern Nigeria”, Shafi na 13.
13. Akwai ma'anarsa ta asali a cikin “Munjid”, shafi na 10. Shehun malami mai zurfin ilmi ne ake nufi da shi, kamar su Shehu Abdullahi Danfodiyo dai malam Jibirilu dan Umar, malamin Shehu Usmanu Danfodiyo.
14. Dubi tarihin Shehu Usmanu Danfodiyo wanda Ibrahim Imam ya rubuta.
15. Domin karin bayani ka dubi Nasiha Da Wa'azi A Cikin Musulunci, tailfin Habib Alhassan.
16. Domin karin bayani ka dubi Infakul Maisuri, wanda Muhammadu Bello ya rubuta, shafi na 91-94.
17. Ka dubi Infakul Maisuri wanda Alhaji Dan'ige ya dauki nauyin bugawa, shafi na 91.
18. Shehu Usmanu ya yi wa jama'a nasiha da su yi karatun littafinsa da na sauran malamai. Ka dubi karshen littafinsa da ake kira Najmul Ikhwani.
19. Ka dubi Najmul Ikhwani, shafi na 43.
20. In kana neman sunayen littattafansa ka dubi makalar Bashir Osman Ahmad, mai take Al-Ishamul Fikri Li Ulama'i Sakkwato.
21. Saboda karin bayani ka dubi Islamic Law in Nigeria na Sayyid Khalid Rashed, lagos, Islamic Publications Bureau, 1986, shafi na 75-80.

No comments:

Post a Comment