An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Monday, 26 May 2014
TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)_
___________________(39)__________________
TAMBAYA: Akramakallahu. Dangane da wankan janaba na mata, wasu matan sukan kitse kansu yadda ruwa ba ya shiga ko'ina a kan nasu. Wasu kuma suna shafa ruwa kawai a kansu sai su ce ya wadatar da su. Shin wankan nasu ya Inganta kuwa?
SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani shi ne cewa duk jiki sai ya sami ruwa a wajen wanka, ruwan kuma ya wanke shi da ma'anar wankewa, wato ya gudana a jikinsa kenan har ya zube. Kuma gashi yana daga cikin bangaren jikin mutum. Saboda haka ko silin gashi daya in bai
sami ruwa ba da sunan ya wanke shi a wanka ba, to janaba tana nan.
Saboda haka lazim ne mace ta tabbatar da cewa dukkan gashinta ya sami ruwa da sunan wanki, ba wai an shafa masa ba, an wanke shi da ruwa.
Batun kitso kuwa, idan kitson zai hana ruwan ya shiga ya wanke gashin, to zai zama wajibi ne a warware shi. Amma idan ko yana daure, ruwa zai iya wanke shi ya tabbata kuma ya wanku. Ba batun kitson muke magana ba, batun wanke gashin muke magana. Saboda haka in dai gashin ya wanku, to ya wadatar.
Ka ga abin da yake wajibi shi ne wake gashin ta kowane hali, kamar sauran abin da bayyana zahiran a jikin mutum a wajen wankan janaba, dole ya wanke shi.
__________________(40)___________________
TAMBAYA: Akramakallahu, Uba ne da dansa suna tafiya a mota sai suka yi hadari duk suka mutu, amma ba a san wanda ya riga wani mutuwa ba daga cikinsu. To wa zai ci gadon wani?
MALAM ZAKZAKY: Duk cikarsu za su gaji juna ne, uba zai gaji da, da zai gaji
uba. Sai a fara rabon gadon uba, sai a cire wa da kasonsa, sannan bayan kuma an gama sai a raba gadon da a cire wa uba kasonsa. Sai sauran magadan uba su sake gadon abin da ya gada daga dansa. Magadan da kuma su gaji abin da da ya gada daga wajen ubansa.
____________________(41)_________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Yaya matsayin wanda ya ba maroka kudi a gidan suna ko biki?
SHAIKH ZAKZAKY: Ba a ce ba a ba maroka kudi ba, a suna ne ko a biki ko ba a ko daya ba. Sai da ba a karfafa gwiwar ba su da yawa, ana cewa a ba su kadan ne don a tsira daga sharrinsu.
__________________(42)___________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan wani zai roki wani abu a wajen wani nakan ji yana cewa "don Zatin Babanka." Yaya halascin yin wannan abu yake a Musulunci?
SHAIKH ZAKZAKY: To shi dai in ya zo da unwanin sadaka ne, ana yin sadaka domin Allah ne. In yana nufin don wanene ya ba da? To sai ya zama dole zai bayar domin Allah ne.
Amma gamar da mutum ya yi wani aiki na alhairi da darajar wani, ba yana nufin wannan aikin an yi wa wannan din ne ba.
Ana iya ce maka albarkacin wane ka yi kaza, amma in ka yi din ba yana nufin wane din ka yi wa ibada ba, sai dai in ya yi da nufin shi wannan ibada ne, to shi ne zai zama tamkar ya bauta masa kenan.
___________________(43)__________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan mutum ya sami sabani da matarsa, sai ta ce ya sake ta, to wane mataki zai dauka?
SHAIKH ZAKZAKY: To akwai matakai da aka ba miji da mata shawarar yadda za su dauka don warware matsaloli.
Kamar wa'azi, wa'azin bai yiwu ba, an kaurace kauracewar ma bai yiwu ba. Sannan sai kai abin gaba ga wadansu wadanda za su sasanta tsakanin miji da mata din. Sai su su duba su ga ina za su Iya sa yabo, ina ne za su sa laifi da kuma mene za su yi ya zama maslaha a tsakaninsu? Amma ba saki ne kawai aka sani yake warware maganar aure ba.
___________________(44)__________________
TAMBAYA: Akramakallahu. Zan iya yi wa Mahaifina layya duk shekara, duk da cewa ya rasu?
SHAIKH ZAKZKY: A'a, ba za ka iya masa layya ba. Ta fuska guda zai yiwu ka yi, shi ne inda dama ya yi tanajin rago zai yi layya din sai Allah ya yi masa rasuwa, to za a iya a yi masa layya din. Ko kuma an ji ya furta cewa yana da niyyar ya yi, to shi ma ana iya yi masa, amma banda sauran shekaru kuma da suka biyo baya, ba zai yiwu ba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment