__________________(75)_________________
TAMBAYA: Ko ya halatta mutum ya yi addu'a don neman mukami, kamar kansila ko waninsa?
SHAIKH ZAKZAKY: To ita dai addu'a ibada ce, kuma duk abin da mutum ya roka wajen Allah, sawa'un na duniya ne ko na lahira, ya nuna ya san Allah ne Mai bayarwa don haka ya nema a wurinsa.
Sai dai abin da ya fi alheri, shi ne mutum in yana neman abu, ya ce "Ya Ubangiji in ka san wannan shi ne mafi alheri gare ni a duniyata da lahirata da magaggabcin al'amarina da majirkincinsa, kuma shi ne a gare mu gyara kuma gare ka akwai yarda, to ka biya mana." Ya kamata ya sa sigar wannan.
Saboda haka duk addu'ar da mutum zai yi, in dai ya roki Allah, ya ce, Allah in dai wannan al'amari akwai gyara, maslaha ne gare ni, kai kuma akwai yarda gare ka ka biya mani," to Insha Allah zai ga biyan bukata kamar yadda Allah yake so.
__________________(76)___________________
TAMBAYA: Ana cewa duk wanda ya kashe wani kisan ganganci, to dukkan laifukan wancan suna kansa. Shin haka ne?
SHAIKH ZAKZAKY: A'a, ba haka bane, shi dai ya yi laifin kisan ganganci. Saboda haka laifin kisan gangancin ne ke kansa. Amma shi wancan wanda aka kashe, kyawawan ayyukansa nasa, munanan ayyukansa nasa.
____________________(77)_________________
TAMBAYA: Ko ya halatta mutum ya yi layya da dabbar da aka dandake?
SHAIKH ZAKZAKY: Eh, za a iya yi, saboda dandaka ba tawaya ne ba. Abin da aka hana layya da shi, shi ne abin da ya sami tawaya wanda za a ce masa tawaya, wato bai kammala ba. Kamar a ce misali mai karyayyen kaho ko yankakken kunni ko gutsirarriyar kafa ko tamikakken dabba ko mara kitse, ko abin da ya yi kama da haka nan wanda shi wannan tawaya ne.
Amma dandaka shi wannan kamar ma gyara nama ne da cikar dabba. Saboda haka bai maishe shi aibi ba. Wato a takaice dabbar da aka hana a yi layya da ita ita ce wadda take da aibi, shi kuwa dandaka ba aibi bane, gyara ne ma.
___________________(78)__________________
TAMBAYA: Menene hukuncin wanda ya yi sata yana yaro karami bai balaga ba? Shin laifin na kan iyayensa ne ko kuwa?
SHAIKH ZAKZAKY: Laifi ba zai iya hawa kan iyayensa ba sai idan iyayensu suka taimaka a kan yin laifin. In ba haka ba, shi yaro kafin ya balaga ba a rubuta masa laifi. Kamar yadda ya zo a hadisi
cewa, an dage alkalami daga mutum uku, yaro har sai ya balaga, mai barci har sai ya farka, mara hankali har sai ya sami hankali.
Saboda haka shi lallai laifi bai hau kansa ba, bai hau kuma kan iyayensa ba, sai dai idan su ne suka sa shi.
____________________(79)_________________
TAMBAYA: Ko ya halatta Malamin makarantar allo ya sa almajiransa noma idan suna zaune a karkara ne, in kuma a birane ne su ke karbar wani abu daga hannun yaran, musamman da yake ba biyan sa ake ba?
SHAIKH ZAKZAY: To shi dai wajen koyar da yaro, an yarda a karbi lada wajen koyar da yaro karatun Alkur'ani. Saboda haka duk yadda ya zama yarjejeniya tsakanin Malami da uban yaro. Idan bangaren yarjejeniyar shi ne yaron zai yi aiki a gona, daidai gwargwadon aikin da ba zai hana shi karatu ba, ya zama bangaren ladan karantar da shi; in dai sun yi yarjejeniyar, babu laifi.
Amma abin da aka sani dai shi ne, ana iya karbar lada. Amma dai ba a kayyade bayar da yanayin ladan ba.
___________________(80)__________________
TAMBAYA: Menene adalci ga wanda yake da mata biyu ko fiye da haka wajen daidata tsakaninsu, shin zai iya yi a kan abin da yake wajibinsa ko har ma da abin yake kyautatawa ne a gare su?
SHAIKH ZAKZAKY: To har da na kyautatawan, domin kuwa idan ya biya wajibi sannan sai a nafila sai ya fifita wata, ya yi rashin adalci.
Alal misali kamar a ce bayan ya yi suturar dole sai kuma ya yi kayan ado ya kebance wata da shi hususan, to ka ga rashin adalci ne wannan saboda in zamansu tare ne, zai zamo wata rana da labarin ya yi wa wancan kaza (ya je gare ta), kuma za ta ga ita ina nata?
Saboda haka lallai daidai gwargwado duk abin da yake rabawa, sawa'un na dole ne ko na ihsani ne, duk dai ana son ya yi adalci.
___________________(81)__________________
TAMBAYA: Ko ya halatta ga mai mata biyu ko fiye ya fi kyautata wa daya saboda ta fi yi masa biyayya ko kuma saboda ita ya auro ta daga gidan masu wadata, saboda wasu na cewa wai kowace mace ana ba ta abinci gwargwadon yadda take samu a gidan su?
SHAIKH ZAKZAKY: Ba a ce wani abu mai kama da haka nan ba. Abin da aka ce dai kawai akwai abin da ake ce ma 'kafa'a'. Abin da ake ce ma 'kafa'a' shi ne daidai matsayi da ma al'ada.
Alal misali kamar idan wasu abincinsu burabusko, wasu tuwo, to ka ga kowacce ita irin abin da ta saba ci ne za ta yi.
Wannan ba yana nufin ana fifita wata ne ba. Saboda ita mai cin wancan, idan aka ba ta wannan za ta ga ba ta da bukata ne. Shi wannan ne kawai aka ce, amma ba ana nufin cewa, yanzu idan misali, sai in abinci mai dadi ne sai ya ce ai 'yar gidan masu wadata ne sai a ba ta abinci mai dadi. An ce maka in mutum ba shi da
wadata ba ya cin abinci mai dadi ne?
Saboda haka lallai ba nan ne kafa'a take ba. Kafa'a shi ne a al'adar mutum shi in ana masa wannan, ba ya ganin ma an kyautata masa ne, sai a yi masa abin da shi a wurinsa shi ne kyautatawa. Amma ka san 'yar talakawa ba za ta ce idan an
ba ta abinci mai dadi ba a kyautata mata ba, a ba ta mara dadi.
Saboda haka ya kamata a gane ma'anar kafa'a a sa ta a muhallinta.
___________________(82)__________________
TAMBAYA: Wasu na cewa Imamai Ma'asumai (AS) ba su zama ma'asumai ba sai ta hanyar aikin da suke yi. Shin wannan aikin da ya kai su ga samun wannan daraja, a nan duniya ne suka yi shi ko kuwa a ina ne?
SHAIKH ZAKZAK: Su da ma can zababbun Allah ne wanda Allah (T) ya kyautata tarbiyyarsu, ya kuma yi su yadda ya dace da sakon da ya dora
masu.
Na'am su ma mutane ne. Saboda haka suna da wadansu abubuwa da suke bijiro masu irin na sauran mutane, amma su sun fi karfin su aikata laifuffuka. Saboda su a matsayinsu, ba zai yiwu ma su aikata laifin bane, saboda zuciyarsu ba irin na wanda za su so su yi laifin bane.
Saboda haka ka ga in haka nan ne, sun kai mustawa ne da in suka yi abin kirki, ya zama abin yabo gare su. Wato ba wai an yi su ne kamar inji, wanda yake yana aikin kawai ba tare da ya san abin da yake yi ba. Suna da 'yancin zabi amma abu mai kyau suke zaba, ba su mummuna.
Shi ya sa ka ga Allah (T) yana yabon bayinsa Annabawa a cikin Alkur'ani, kamar yadda yake yabon Ayyub, yake cewa "Inna wajadnahu sabiran ni'imal abd innahu awwab." Mun same shi mai hakuri da dauriya, madalla da bawa mai yawan komawa da al'amarinsa zuwa ga Allah.
Da sauran yabo wanda aka yi wanda aka yi wa Annabawa, kamar Ibrahim da Isma'il da cewa shi mai cika alkawari ne, da ire-iren wadannan. Ka ga wato ayyuka kenan.
Abin da nake fata shi mai tambayar ya fahimta shi ne, matsayin isma ba matsayi ne da kake tsuwurwurta da aikinka ba, wanda yake wanda wani wanda yake in ya so sai ya yi ta yin aikin kirki sai ya koma ya zama irin shi ba. Wato kamar annabci, ba ana yin aiki ne mai kyau sai a zama Annabi ba. Da ma su Annabawa zababbu ne tun asali.
Haka ma matsayin Imamai, shi ma ba wani aiki ne mutum yakan yi in ya kai wani mustawa sai a ce yanzu ya zama ma'asumi ba, da ma can su Ma'asumai
Allah ya yi su haka nan ne. Shi kuwa
abin da muke cewa, su zababbu ne kuma
ayyukan daidai da matsayinsu ne.
___________________(83)_________________
TAMBAYA: Akwai wani hadisi da aka ce Allah ba ya karbar sallar wandanda suka yi hukunci da abin da ba Allah ya saukar ba. Menene ingancin wannan hadisin, kuma yaya matsayin sallar mutanen Nijeriya da suke bin dimokradiyya?
SHAIKH ZAKZAKY: Ko ba komai, wannan dai misdakin fadin Allah (T) ne, "waman lam yahkum bi ma anzalallahu…" Saboda haka ka ga ko da ma bai san ingancinsa ba ya san cewa aya ma ta zo da siga shigen irin wannan. Kuma in dai ya fahimci abin da yake nufi, abin da hadisin yake nufi, to sai ya yi kokari daidai gwargwado ya ga ya misaltu da wannan.
Amma dangane da hukunta matsayin wani, to wannan ai ba aikinmu bane. Mu ce ai tunda haka aka ce, to wane kaza ne. Shi dai wannan abin da hadisi ya ce kenan kuma ya yi daidai da ma'anar aya.
No comments:
Post a Comment