___________________(7)___________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Na gani a ayyukan daren Juma'a, Imam Sadik (AS) ya ce, duk wanda ya yi waka ko da a kan gaskiya ne, to ba shi da ladan ayyukan wannan ranar. Sai kuma na ga ana shirya majalisin mawaka a ranar ko daren. Yaya abin yake?
SHAIKH ZAKZAKY: To, hukuncin yin wake a daren Juma'a da ranarta, shi ne karhanci. Wannan kuma ko ba komai yana nufin lalle waken da ya halatta ne a yi a sauran ranaku da darare.
Amma saboda muhimmancin daren Juma'a da kuma ranar Juma'a, don mutum ya shagalta da ayyukan ibada ma'asurai, shi ya sa sai aka karhanta masa yin wadannan. Kuma ba kamar yadda shi (mai tambayar ) ya fada ba, abin da hadisin ya ce shi ne;
"lam yakun lahu nasibun siwahu fi tilkal-Lailati," ko abin da ya yi kama da haka nan.
Abin da yake cewa shi ne, ba shi da wani lada sai wannan, a wannan dare ko wannan yini, wato wannan waken. Wato maimakon ka yi salloli da addu'o'i, sai ka yi wake, to, waken ne ladanka. Ka ga ka yi hasarar ladan wadancan ma'asurai.
Wannan yana daga cikin abin da ake ce wa, a hanaka abu karami don ka yi babba. Shi waken, ba haramun bane, duk ya halatta. Amma addu'ar ta fi, salloli da addu'o'i sun fi wake. saboda haka wanda ya yi wake, ladan waken ya samu. Ka ga ya yi asarar salloli da addu'o'in da bai yi ba.
Amma ba yana nufin wai haramun ne ba.
___________________(8)____________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ina da kudi kuma sai nan da wata hudu zan yi amfani da su. Shin ya halatta in sayi amfanin gona in ajiye, ko bai halatta ba?
SHAIKH ZAKZAKY: To, abin da ya haramta dangane da sayen abinci a ajiye shi ne, in ya kai haddin da ake ce masa 'Ihtikari,' shi ne boye abinci alhali al'umma tana bukata. In kayan abincin da zai saya ya ajiye din, al'ummar musulmi ba za su bukatu ya zuwa gare su ba, ta yadda shi sayen da ya yi ya boye zai cutar da su ba, to babu komai.
Wato in bai kai haddin 'Ihtikari' ba, babu komai.
___________________(9)____________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mace tana yi mani sallama kuma ba muharrama ta ba ce. Ya halatta na amsa?
SHAIKH ZAKZAKY: Eh, ya halatta in dai sallama din ne. Hatta ma in kana saye da sayarwa, ya halatta ku yi ciniki, ta taya ka ce albarka, har ku daidaita a cinikin.
Wato a kan maganar da ya halatta, ka yi da ita, ya halatta ka yi da ita, wanda ya haramta ne ya haramta.
____________________(10)_________________
TAMBAYA: Menene hukuncin yin sujada a kan siminti ko a kan kwali?
SHAIKH ZAKZAKY: To, halacci ne, wato mutum yana iya yin sujada a kan siminti, ko a kan kwali. Sai dai ba zai iya yin taimama a kan kowanne daga cikinsu ba.
No comments:
Post a Comment