An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Monday, 26 May 2014
TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)_
__________________(27)___________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan za ka yi tafiya, da ka fara ganin daji shi kenan kasaru ta kama ka ko kuwa?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba inda aka fadi haka nan. Ba a ce sai in ka ga daji ne za ka fara kasaru. Tana iya yiwuwa ma a yanzu yadda wurare suka caccanza, ina jin sai ka yi tafiya wanda ya kai 'musafa' ba ka ga dajin ba ma samsam, saboda duk an bi an nonnome wurin, an yi gidaje wurare da kauyuka da sauransu.
Tun farko ma ba a taba cewa daji ba, abin da aka sani shi ne, idan ka bar ganuwar gari ko kuma ka daina jin sauti da ganin garin a lokaci guda, idan garin maras ganuwa ne.
Saboda haka tun farko ba inda aka taba cewa in ka ga daji ballantana maganar daji ya fito. Kuma mafaran kasaru shi ne makaransa in ka dawo.
____________________(28)_________________
TAMBAYA: Akramakallahu. Menene hukuncin ajiye kare a cikin gida?
SHAIKH ZAKZAKY: To, haramun ne mutum ya ajiye kare in ba bisa wata lalura ba. Akwai wuraren da aka halatta amfani da kare, kuma wannan zai iya yiwuwa ya halatta a ajiye shi domin wannan amfanin. Amma haka kawai a ajiye kare domin nishadi kamar yadda mutane sukan yi na sha'awa, to wannan ya haramta ga musulmi.
A inda kuma ya halatta, shi ne kamar wajen farauta don neman abinci, ko don gadi, inda wani abu ba zai tsaya ma a matsayin karen ba.
__________________(29)___________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Na ga wasu sukan yi shafa'i sai su bar wutiri. Shin haka bai da wata matsala?
SHAIKH ZAKZAKY: To, duk salla raka'a biyu sunanta shafa'i. Amma dai ana son in mutum zai yi wutiri, to ya yi raka'o'I biyu saukaka kafin ya yi wutirin.
__________________(30)___________________
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ni Malamin asibiti ne, wata mata tana nakuda, amma mijinta da iyayenta ba su kai ta asibiti ba, sai suka nemi da in duba ta. Da na je sai na yi mata allurar da ta dace, sai abin ya hadu da karar kwana. Idan mijinta da iyayenta sun yafe, kaffara ta hau kaina?
SHAIKH ZAKZAKY: (To, ya ce dai allurar da ta dace, a nazarinsa). Watakila wannan za a kai hukuncin wajen wani ne ba shi ba, ya ga ko allurar ta dace. Idan ya tabbata cewa allurar da ya yi ne ya yi sanadiyyar mutuwarta, to lallai kaffara ta hau kansa ko da sun yafe masa diyya. Idan kuma ba allurar ne ta yi sanadiyyar rasuwarta ba, to ba wani abin da ya hau kansa.
Amma wannan kamar yadda na ce, hukuncin ba shi zai yi ba, sai a kai ma wani wanda ya fi dacewa da sassan wannan. Ya ce allurar ta dace, saboda haka mutuwar Allah da Annabi ne ta yi, ko kuma ya sami tangarda wajen yin allurar, ta yiwu maganin allurar ya dace, amma wajen yi ya dan janyo sanadiyyar a rasu.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment