Monday, 26 May 2014

TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)_


____________________(23)_________________

TAMBAYA: Na ji ana cewa idan mutum ya saka abinci a baka kamar nama, sai
ya fito da shi ya sake mayar da shi ya
hadiye shi, ya haramta. Mene ne
gaskiyar lamarin?

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ban san wani abu dangane da wannan ba. Sai kawai in shi yana ganin abin kyama ne.

Ta yiwu mutane suna ganin abin kyama ne abin da ya fito baki a mayar da shi,
amma dai ba wai haramci ba.

_________________(24)____________________

TAMBAYA: Ni mai sayar da littattafan addini ne, amma ina hadawa da littattafan soyayya. Shin meye hukuncin sayar da littattafan soyayya?

SHAIKH ZAKZAKY: To, idan abin da yake cikin littafin babu laifi da shi, to ba Laifi ka sayar. Amma idan akwai batsa da wasu miyagun abubuwa a ciki, wanda yake kamar kana tallata shi ma wannan batsar ne, to ba zai halatta ba.

___________________(25)__________________

TAMBAYA: Shin ko ya halatta mutum ya yi 'brushing' (wanke baki da Makilin) alhali yana azumi?

SHAIKH ZAKZAKY: To, lallai mun taba amsa wannan tambaya din. Muka ce ba
ma ya halatta bane har ma yana da kyau, don warin bakin mai azumi da aka ce ya fi kanshin Miski ba ana nufin kazantar baki ne ba.

Ana nufin hamami ne da kan fito daga ciki sakamakon rashin abinci. Yakan rinka wani irin kanshi saboda daga hanji yake fitowa.

Amma ta baki yake fitowa shi ya sa aka kira shi 'faikh'. Amma a Larabci ma ba
an ce warin baki bane, Hausawa suka ce
masa warin baki, amma 'faikh' aka ce masa, wanda kamar tururi ne yake fitowa daga uwar hanji sakamakon ba
komai a ciki.

Saboda haka wanke baki da wannan ba zai yi komai ba matukar mutum ba zai hadiye ba. Kasantuwarsa yana da dandano bai cutar ba. Da zaki yake ko daci, ko ma wane ne, bai cutar ba, matukar bai hadiye ba.

____________________(26)_________________

TAMBAYA: Mutum ne dan kasuwa mai shago kusa da masallaci kuma sauti na kai masa. Shin ko ya halatta ya rinka bin
jam'in sallah daga nan?

SHAIKH ZAKZAKY: A'a bai halatta ba. Don daga cikin ka'idar bin jam'i har sai idan ka sadu da sahu da kirjinka ko da kafadarka. Saboda haka sai dai idan sahun ne ya shigo har shagonsa jama'a suka bi ta cikin shagon nasa, to yana iya yin haka nan. Amma in ba haka ba, to
lazim ne ya sadar da sahu.

Idan ya zama da tazara tsakanin sa da masallaci, to shi sallarsa ba ta inganta ba.

No comments:

Post a Comment