___________________(124)_________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Wace addu'a ake karantawa don fid da aljannu daga jiki ta bangaren Iyalan gidan Manzo(S)?
SHAIKH ZAKZAKY: Irin wadannan ruwayoyin suna da yawa. Mutum zai iya duba su a mahallansu, musamman littattafai ma'asurai na addu'a, wadanda ga su nan latu'addu wala tuhsa. Zai ga
wadansu wadanda aka ruwaito.
Akwai ma wadda Manzon Allah ya taba ba shi wata wasika, ya ce ya je ya aje a dakin. Kuma har ya ji su suna kururuwa, suna cewa ya dauke musu wannan wasikar.
A ciki Manzon Allah ya ce wannan daga Manzon Allah ne zuwa ga aljanun da suke wurin a kan cewa su fita. Sai dai
muhallinsa ya kamata ya nema, ya samu
a cikin littattafan addu'o'i ma'asurai.
___________________(125)_________________
TAMBAYA: Akramakallahu. Mutum ne Direban mota, sai ya yi hatsari, mutane 50 suka mutu, kuma ba tukin ganganci ya yi ba. To menene sakamakon wannan mutumin. Kuma idan shi ma ya rasa ransa, to hukuncin kan wa ya hau kenan?
Kuma wasu direbobin kan buge mutum har ya rasa ransa, amma sai a ce an yafe masu, shin wannan ya halasta?
SHAIKH ZAKZAKY: Tunda ya ce ba na ganganci bane, wato kenan hadari ne ya auku, ba sakamakon sakacin direba ba, to zai zama kenan ba abin da ya hau kansa.
Amma da a ce sanadiyyar hadarin sakaci ne daga nasa bangaren, to ko da mutum hamsin ne ko fiye to yana daidai da hukuncin wanda ya kashe su bisa kuskure. Kuma zai hau kansa ya biya diyyarsu, ya kuma yi kaffara.
A kaffarar, na azumi tunda ba zai yiwu ba, sai a koma ga ciyarwa. Kuma idan mutumin ya tabbata ya yi ganganci, har kuma ya zama sanadiyyar rasuwarsa shi a kan kansa da kashe wasu, to shi dangane da rasuwarsa shi ya kashe kansa kenan, amma sauran zai koma ga magadansa. Sune alhakin biyan diyya ya hau kansu.
Tunda shi yake kaffara kuma ya mutu, to shi kenan wannan ya fadi. Sai dai su yi masa addu'ar Allah ya yafe masa.
Kuma idan ma'abota hakki na diyya suka ce sun yafe, to shi kenan ya halasta, ya yafu.
____________________(126)________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Akwai ruwan wani itace a kudancin kasar nan wanda ake kira bammi, ana sha, kuma yana bugarwa kamar giya. Amma a nan Arewa ana ba yara in suna yin kyanda, kuma suna warkewa, to menene hukuncinsa a wajen yaran?
SHAIKH ZAKZAKY: Ba a magani da giya, sai idan ya zama dole. Saboda haka sai a nemi wani magani ba wannan ba.
Giya kuma, in dai abu na bugarwa sunansa giya, komai karantarsa, in dai mai yawansa zai bugar, kadan din sa ma wanda ba zai bugar ba ya haramta.
Hatta in da ma za a surka shi da ruwa, ya zama giyan dan kadan ne, duk da haka zai haramta. Saboda haka ana magani da giya kawai in ya zama dole ne. In ya zama ba a san wani magani ba illa wannan, zai zama babu laifi da shi gwargwadon da ba zai iya bugarwa ba ko a sha ko a shafawa.
_______________(127)_________________
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan aka soya ko aka dafa kifi wanda ya halasta a ci da wanda bai halasta a ci ba tare, ya halatta mutum ya ci wanda ya halatta a ci, ko ya sha miyar ko kuwa gaba daya bai halatta mutum ya ci ko ya sha miyar ba?
SHAIKH ZAKZAKY: Abin da ya haramta a ci bai kamata har wala yau ya zama an sha ruwansa ba, don shi ma ruwan bangare ne nasa. Sai dai dangane da sha'anin su nama, tana iya yiwuwa a dafa wani bangare wanda yake shi an hana ci.
Kamar nama, bangaren da ba a ci, to ana iya hada shi da wanda ake ci a dafa, amma in an zo a fid da shi.
Kamar misali mu kaddara ka sai balangu, ya zama da saifa, to in ka tsittsince saifar ka zubar ba laifi. Haka zalika kashi, kodayake shi kashi akwai sabani. Wasu suna haramtawa, wasu sun ce in ya inganta ba ya cutarwa ana iya ci, to shi ma za a iya tsotsewa a yar. Wannan dangane da nama ne.
Amma in aka ce wannan kifi ne wanda ya haramta a ci, to shi ba za a saka shi a cikin miya a dafa shi ba, tunda shi ma kamar an ci shi ne. Haka zalika nau'o'in nama na abin da aka haramta a ci, kamar misali gafiya, wadda take haramun ce, a hada ta da naman kaza. Ba zai halatta ba.
___________________(128)_________________
TAMBAYA: Ina hukuncin wanda ya sanya yaro dan shekara 9 ko 10 ya karya azuminsa?
SHAIKH ZAKZAKY: Idan yana nufin Uba ya tilasta ma dansa ya ci abinci ne alhali ya shekara 9 ko 10, to sai mu ce lallai ya yi laifi, kodayake su wadannan, takalifin azumin bai hau kansu ba. Amma in za su iya yi ya kamata a kyale su, sai dai in an ga azumin zai cutar da su ne.
_________________(129)___________________
TAMBAYA: Namiji mai mata biyu, shin shi ne ke da hakkin ba kowacce lokacin saduwa ko sai sun nema?
SHAIKH ZAKZAKY: Abin da aka sani shi ne akwai abin da ake ce ma rabon kowace mace a daurar kwana hudu tana da kwana daya. Amma wannan ba yana nufin saduwa ba, in jima'i yake nufi da saduwa din. Shi saduwa daidai gwargwadon bukatar kawannen su ne.
Hakkinsa ne hakkinta ne, saboda hakkinsu ne su biyu, bai kebanta da ita ba, bai kebanta da shi ba, tsakaninsu ne. Kuma shi rabon kwana ba lallai yana nufin jima'i bane.
___________________(130)_________________
TAMBAYA: Shin mutum zai iya hada Azahar da la'asar sannan ya yi nafilolinsu 16?
SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani dai shi ne ana yin nafilolin zawwal kafin azuhur ne,
raka'a 8. Sannan kuma bayan an yi azuhur sai a yi nafilolin la'asar raka'a 8.
Amma in wani dalili ya sa an bi shi bashi, yana iya biya bayan la'asar ko ma bayan isha. Amma ba wai 'ihtiyaran' ba.
Ba 'ihtiyaran' ya zama dama haka yake yi bisa zabin kansa. Kamar yadda shi a nan yana nufin cewa musamman sai ya hada azuhur da la'asar sannan ya zo daga baya ya zo da nafilolin, in ya yi haka nan kamar ya yi wani abin da ba shi aka sani ba, in dai ba wata lalura ce ta sanya, kamar kurewar lokaci, masalan. Sai ya zo da la'asar ya jinkirta nafilolin zuwa wani lokaci.
No comments:
Post a Comment