Sunday, 25 May 2014

SABAWA MAHALICCI DA SAKAMAKONSA


Sabo Da Kuma Sakamako
A bisa mahangar Musulunci, ana ganin mutum a matsayin shugaban dukkan halittu duniya. Don haka duk ayyukansa, wadanda suka dace da wadanda ba su dace ba, sun kasance a karkashin tasirin "Ka'idar Zamantakewa", wanda ke nuna cewa ayyuka da dabi'un dan'Adam, kyawawa ko munana, sun cancanci sakamako ku azabar da ta dace da su. Idan har aka rasa wannan ka'ida, wato ka'idar sakamako, to kokari da kuma ayyukan mutum za su rasa wani amfani kana kuma kimar rayuwa za ta kasance cikin rudu, bugu da kari kuma adalcin Ubangiji zai zamanto ba shi da wata ma'ana. Bisa la'akari da cewa dan'Adam halitta ce mai tsananin son kanta, don haka Musulunci sai ya yi amfani da wannan so wajen tsara dokoki da ka'idojin ukuba. Don kuwa wadannan dokoki za su hana shi jin dadi da walwala da kuma sanya shi cikin wahala, to hakan yakan sa shi a wasu lokuta ya nesance su.
Haka nan kuma, Allah Ya tsara azabobi wadanda ayoyin Alkur'ani suka bayyana su a matsayin sakamakon ayyukan dan'Adam da kuma tabbatar da adalci da hikimar Ubangiji. Bisa dubi cikin bayanan Alkur'ani kan azabtarwa, za mu iya gani wadannan abubuwa, kamar haka:

(1)- Azabtarwa a matsayin "Ka'ida ta Dabi'a" wanda suke da alaka ta kurkusa da sauran ka'idoji na ayyukan dan'Adam da na al'umma. Alkur'ani mai girma yana bayanin wannan al'amari kamar haka:
"...lalle, idan wani mai gargadi ya zo musu, tabbas za su kasance mafi shiryuwa, daga dayan al'ummomi. To, a lokacin da mai gargadi ya je musu, bai kara su da kome ba face gudu. Domin nuna girman kai a cikin kasa da makircin cuta. Kuma makirci na cuta ba ya fadawa face a kan mutanensa. To, shin, suna jiran (wani abu ne) face dai hanyar (kafiran) farko. To, ba za ka sami musanya ba ga hanyar Allah. Kuma ba za ka sami juyarwa ba ga hanyar Allah.

Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin kasa, domin su duba yadda karshen wadanda suka gabace su ba? Alhali kuwa sun kasance mafifita karfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayarsa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kasa. Lalle Shi ne Ya kasance masani, Mai ikon yi". (Surar Fadir, 35: 42-44)
"Kuma, hakika, mun halakar da al'ummomi daga gabanninku, a lokacin da suka yi zalunci, kuma Manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu, amma ba su kasance suna imani ba. Kamar wannan ne, muke sakawa ga mutane masu laifi. Sa'an nan kuma muka sanya ku masu mayewa a cikin kasa daga bayansu, domin mu ga yaya kuke aikatawa". (Surar Yunus,10: 13-14)
"Kuma wani Annabi bai je musu ba face sun kasance, game da shi, suna masu yin izgili. Sai Muka halakar da wadanda suke su ne mafiya karfin damka daga gare su. Kuma abin misalin mutanen farko ya shude". (Surar Zukhruf, 43: 7-8)
"Kuma babu abin da ya hana mutane su yi imani a lokacin da shiriya ta zo musu, kuma su nemi gafara daga Ubangijinsu, face hanyar farko ta je musu ko kuma azaba ta je musu nau'i-nau'i". (Surar Kahfi, 18: 55)

Bisa wadannan kalmomi na Allah, an bayyana azabtarwa a matsayin tabbataccen sakamakon aiki wanda ke tabbatuwa a duk lokacin da aka samar da abubuwan da suke tabbatar da shi, kamar lalacewa, zalunci, cin mutunci da sauransu.
(2)- Sau da dama azabtarwa tana ta'allaka ne da wani takamammen aiki, ba wai kawai wani al'amari ne da aka dora wa raunanan mutane tare da wani dalili ba.
(3)- Azabatarwa tana da alaka ta kurkusa da adalcin Ubangiji wanda hakan yana nuna cewa Allah ba zai bar azzalumai su tafi haka kawai ba tare da yi musu azaba ba. Sannan su kuma wadanda aka zalunta a dauko musu fansa. Alkur'ani mai girma ya na cewa:
"Yana mai karkatar da sashensa domin ya batar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yana da wani wulakanci a duniya, kuma Muna dandana masa azabar gobara a ranar lahira. (A ce masa) wancan azaba saboda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah Bai zama Mai zalunci ga bayinSa ba". (Surar Hajj, 22: 9-10)

4- Alkur'ani mai girma ya bayyana nau'o'i hudu na irin azabar Ubangiji:
(A)- Azabtarwa irin ta kotu.
(B)- Azabtarwa irin ta al'umma.
(C)- Azabtarwa irin ta Ubangiji.
(D)- Azabtarwa irin ta Lahira.

(A)- Azabtarwa Irin Ta Kotu.
Wannan ya hada da duk wadansu matakai na hukumce-hukumce, ka'idoji, dokoki da cin tara wadanda ake gudanarwa a dokokin laifuffuka (a kotuna) kamar su hukumcin kisa, tilasta biyan hakki da kuma yanke hukumci.

(B)- Azabtarwa Irin Ta Al'umma.
Irin wannan azabtarwa tana faruwa ne a sakamakon bijirewar mutane ga sakon Ubangiji da kuma aikata ayyukan sabo wanda ke kawo wahalhalu, bakin ciki da bala'i na gaba daya. Wannan tabbatac-cen bala'i yana faruwa ne a sakamakon kauce wa hanya madaidaiciya wacce Ubangiji Ya zaba. Inda daga karshe, azabobi kala-kala za su sauko wanda za su iya sa dukkan al'umma cikin halin kaka-ni-kayi. Saboda haka ne, wasu ayoyin Alkur'ani da hadisai suka tabbatar da faruwar irin wadannan azabobi a duk lokacin da mutane suka kauce wa hanya madaidaiciya kana suka ci gaba da aikata munanan ayyuka. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
"Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku, daga bisanku, ko kuwa daga karkashin kafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku kungiyoyi, kuma Ya dandana wa sashenku masifar sashe. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsam-maninsu suna fahimta".(Surar An'am, 6: 65)
"Barna ta bayyana a cikin kasa da teku, saboda abin hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su komo". (Surar Rum, 30: 41)
"Kuma Allah Ya buga misali, wata alkarya ta kasance amintacciya, natsattsiya, arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri, sai ta kafirta da ni'imomin Allah saboda haka Allah Ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro, saboda abin da suka kasance suna sana'antawa". (Surar Nahli, 16: 112)
"Kuma lalle ne, hakika, mun kama mutanen Fir'auna da tsananin shekarun fari da nakasa daga 'ya'yan itace, tsammaninsu suna tunawa". (Surar A'arafi, 7: 130)

Dangane da hakan kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Alamar yardar Ubangiji ga bayinSa shi ne adalcin shuwagabanninsu da kuma saukin kayayyaki (a kasuwa), kana kuma rashin yardarSa, ita ce zaluncin shuwagabanninsu da kuma tsadar kayayyaki"[11].
"Duk yadda kuka kasance, za a mulke ku".
Sannan kuma yana cewa:
"A duk lokacin da lalatattun mutane suka zama masu mulki, kuma Dagattansu suka zamanto marasa mutunci, sannan kuma ake girmama fasikai, to su saurari saukar bala'i"[12].
Sannan kuma yana cewa:
"Muminai suna cikin wahalhalu har sai an gafarta musu dukkan zunubansu".
Imam Ali (a.s.) yayin da yake shawartar 'ya'yansa, yana cewa:
"Kada ku taba barin umurni da kyawawan ayyuka da kuma hani da munana, domin in kuka yi haka, to mafi sharrin al'ummarku za su mulke ku, kuma ba za a amsa muku duk salloli da addu'oinku ba"[13].

An ruwaito Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"Allah Ya aika da daya daga cikin AnnabawanSa zuwa ga mutanensa kana Ya umurce shi da ya ce musu, babu wasu mutanen wata alkarya wadanda suka kasance suna Min biyayya, face sai sun arzurta da ni'imomiNa. Amma a duk lokacin da suka rabu da hanyaTa, to Zan bar su su wahala. Kana babu wasu mutanen wata alkarya da suka kasance masu sabo, face sai sun fuskanci fushiNa, amma a duk lokacin da suka komo ga tafarkiNa, to Zan bar su su amfana da ni'imomiNa. Sannan kuma ka gaya musu cewa rahamaTa ta gabaci fushiNa, don haka kada su yanke kauna, domin babu wani zunubi, kome girmansa da ba Zan iya gafarta shi ba. Kana ka gaya musu cewa, kada su sa kansu cikin fushiNa, kana kada su wulakanta salihan bayiNa, don kuwa Zan saukar musu da azabaTa"[14].

Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) din dai yana cewa:
"Hakika wani daga cikinku zai kasance mai yawan tsoron mahukunta, hakan kuwa saboda zunubansa ne, don haka sai ku yi iyakacin kokarinku wajen nisantar aikata zunubi, sannan kuma ku nisanci son zukatanku"[15].
Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) yana cewa:
"A duk lokacin da al'umma suka kirkiro wasu zunubai a cikin rayuwarsu wadanda da ba sa aikatawa, a sakamakon haka, Allah Zai saukar musu da bala'o'in da ba su taba saninsu ba"[16].

Daga wadannan bayanai da maganganu za mu iya fahimtar cewa:
1. Ayyukan mutum nakan kansa, na al'ummance da kuma na addinance, suna da alaka ta kurkusa da ka'idojin dabi'a wadanda su ne suke tabbatar da tafarkin haduwar al'amurran dan'Adam da sauran muhimman al'amurra.
2. Wannan haduwa, idan har aka yi ta a kan karfafaffen asasi, zai iya ba wa mutum ci gaba a cikin rayuwarsa, idan kuwa ba haka ba, to mutum ba zai sami kome ba, face mummunan sakamako, rudani da kuma wahalhalu wanda hakan ita ce bayyananniyar azabar Ubangiji.
Hakika a duk lokacin da mutane suka zamanto sun lalace, kana suka mika wuyansu ga munanan ayyuka, to ba za su taba tsira daga kasancewa a karkashin mulkin zalunci da kuma rayuwa cikin kaskanci saboda yin wofi da suka yi da ka'idojin Musulunci.

(C)- Azabtarwa Irin Ta Ubangiji
Wannan ita ce mafi girman dukkanin azabobi. Alkur'ani mai girma ya yi cikakken bayani kan tarihin mutane da al'ummomi da suka bar hanya kana suka ci gaba da aikata munanan ayyuka da kuma saba wa umurni da koyarwar Annabawa da Manzanni. Inda a sakamakon haka, Allah Ya saukar musu da azabarSa a bangaren guda a matsayin sakamakon abubuwan da suka aikata, sannan a daya bangaren kuma a matsayin hanya mafi dacewa ta gina rayuwar dan'Adam a kan tabbataccen asasi na takawa da kuma farkar da kwanyar dan'Adam ta nadama da tuba wanda ke sanya mutum ya dawo zuwa ga madaidaiciyar hanya. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Barna ta bayyana a cikin kasa da teku, saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su komo". (Surar Rum, 30: 41)
"Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku, daga bisanku, ko kuwa daga karkashin kafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku kungiyoyi, kuma Ya dandana wa sashenku masifar sashe. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsam-maninsu suna fahimta". (Surar An'am, 6: 65)

(D)- Azabtarwa Irin Ta Lahira
Alkur'ani mai girma bai taba yin cikakke da kuma karin bayani sosai kamar yadda ya yi yayin bayanin rayuwa a ranar lahira ba.
"Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to yana da goma din misalinsa. Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su". (Surar An'am, 6: 160)
"To, ya ya idan mun tara su a yini wanda babu shakka a cikinsa, kuma aka cika wa kowane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhali kuwa, su ba za a zalunce su ba?". (Surar Ali Imrana,3: 25)
"Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah mai gaggawar hisabi ne". (Surar Ibrahim, 14: 51)
"....to, wane ne mafi zalunci daga wanda ya karyata game da ayoyin Allah, kuma ya hinjire daga barinsu? Za mu saka wa wadanda suke hinjirewa daga barin ayoyinmu da mugunyar azaba, saboda abin da suka kasance suna yi na bijerewa". (Surar An'ami, 6: 157)
"Suna da wata shinfida daga jahannama kuma daga samanu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke saka wa azzalumai". (Surar A'arafi,7: 41)

Idan muka yi dubi cikin irin wannan siffantawa, za mu iya fahimtar cewa wannan takaitacciyar duniya wata gada ce ta zuwa lahira. Hakika ma dai lahira wani ci gaba ne na wannan duniya wacce ta kasance rayuwa ce wacce ba ta da karshe. A bisa bayanin Alkur'ani, mutum da ayyukansa a wannan duniya yana wakiltan farkon bangaren rayuwa ne; daya bangaren kuwa rayuwar lahira, wanda yake ci gaba ne na wannan rayuwa, ne yake wakiltarsa.
"To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
A bisa wannan bayani, za mu fahimci cewa ranar lahira, ita ce ranar da za a zo da ayyukan mutum don tantancewa da kuma yin sakamako.

Dangane da hakan, Sheikh Raghib Isfahani ya na cewa:
"Sakamako yana bukatuwa da abin da ya yi daidai da shi, in alheri to alheri, in kuwa sharri, to sharri, ana cewa an saka masa kan kaza da kaza. Allah Ya na cewa: "Sakamakon mummunan aiki, shi ne mummuna kamar sa"[17].

Alkur'ani mai girma ya yi cikakken bayani kan akidar sakamako:
"....Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su". (Surar An'am, 6: 160)
Hakika, wannan ka'ida ta sakamako wata babbar alama ce na adalcin Ubangiji da kuma kamalarSa. Daga karshe, ka'idar "Adalcin Ubangiji" ta kumshi tasirin akida, dabi'a da na ruhi ga dan'Adam.
1. Alakar dan'Adam da MahaliccinSa ta ginu ne a kan karfafan imani kana kuma dukkan ayyukansa, kyawawa da munana, Allah ne Zai yi masa hukumci.

2. Mutumin da ya yi imani da azabar Ubangiji da kuma ka'idar sakamako, to zai nesanci aikata munanan ayyuka wadanda su ne ummul aba'isin din fadawarsa cikin rudu da wahala.
Don haka, bayanin cewa ya kamata dan'Adam ya sanya muhimmancin wadannan ka'idoji a zuciyarsa, ya zamanto wani share fage ne na kokarin dan'Adam na gina kyakkyawa kana tsabtatacciyar rayuwa wacce take cike da kwanciyar hankali da daukaka.
Hakika idan aka rasa sakamako (azabtarwa), to daidaituwar alaka da ke tsakanin aiki da kuma saka-makonsu zai jirkita matukar dai ana aikata sabo, kana kuma za a rasa kimar abubuwa sannan kuma hasken adalci zai bace a cikin rayuwa.

11. Usul al-Kafi na Kulayni, juzu'i na 5, shafi na 162.
12. Tuhaful Ukul na Alharani, shafi na 25.
13. Kamar na sama, shafi na 136.
14. Usulul Kafi na Kulaini, juzu'i na 2, shafi na 274.
15. Kamar na sama, shafi na 275.
16. Kamar na sama.
17. Almufradat fi gharibil Kur'an na Raghib Isfahani, shafi na 92.

No comments:

Post a Comment