Monday, 26 May 2014

TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

___________________(80)__________________

TAMBAYA: Menene adalci ga wanda yake da mata biyu ko fiye da haka wajen daidata tsakaninsu, shin zai iya yi a kan abin da yake wajibinsa ko har ma da abin yake kyautatawa ne a gare su?

SHAIKH ZAKZAKY: To har da na kyautatawan, domin kuwa idan ya biya wajibi sannan sai a nafila sai ya fifita wata, ya yi rashin adalci.

Alal misali kamar a ce bayan ya yi suturar dole sai kuma ya yi kayan ado ya kebance wata da shi hususan, to ka ga rashin adalci ne wannan saboda in zamansu tare ne, zai zamo wata rana da labarin ya yi wa wancan kaza (ya je gare ta), kuma za ta ga ita ina nata?

Saboda haka lallai daidai gwargwado duk abin da yake rabawa, sawa'un na dole ne ko na ihsani ne, duk dai ana son ya yi adalci.

___________________(81)__________________

TAMBAYA: Ko ya halatta ga mai mata biyu ko fiye ya fi kyautata wa daya saboda ta fi yi masa biyayya ko kuma saboda ita ya auro ta daga gidan masu wadata, saboda wasu na cewa wai kowace mace ana ba ta abinci gwargwadon yadda take samu a gidan su?

SHAIKH ZAKZAKY: Ba a ce wani abu mai kama da haka nan ba. Abin da aka ce dai kawai akwai abin da ake ce ma 'kafa'a'. Abin da ake ce ma 'kafa'a' shi ne daidai matsayi da ma al'ada.

Alal misali kamar idan wasu abincinsu burabusko, wasu tuwo, to ka ga kowacce ita irin abin da ta saba ci ne za ta yi.

Wannan ba yana nufin ana fifita wata ne ba. Saboda ita mai cin wancan, idan aka ba ta wannan za ta ga ba ta da bukata ne. Shi wannan ne kawai aka ce, amma ba ana nufin cewa, yanzu idan misali, sai in abinci mai dadi ne sai ya ce ai 'yar gidan masu wadata ne sai a ba ta abinci mai dadi. An ce maka in mutum ba shi da
wadata ba ya cin abinci mai dadi ne?

Saboda haka lallai ba nan ne kafa'a take ba. Kafa'a shi ne a al'adar mutum shi in ana masa wannan, ba ya ganin ma an kyautata masa ne, sai a yi masa abin da shi a wurinsa shi ne kyautatawa. Amma ka san 'yar talakawa ba za ta ce idan an
ba ta abinci mai dadi ba a kyautata mata ba, a ba ta mara dadi.

Saboda haka ya kamata a gane ma'anar kafa'a a sa ta a muhallinta.

___________________(82)__________________

TAMBAYA: Wasu na cewa Imamai Ma'asumai (AS) ba su zama ma'asumai ba sai ta hanyar aikin da suke yi. Shin wannan aikin da ya kai su ga samun wannan daraja, a nan duniya ne suka yi shi ko kuwa a ina ne?

SHAIKH ZAKZAK: Su da ma can zababbun Allah ne wanda Allah (T) ya kyautata tarbiyyarsu, ya kuma yi su yadda ya dace da sakon da ya dora
masu.

Na'am su ma mutane ne. Saboda haka suna da wadansu abubuwa da suke bijiro masu irin na sauran mutane, amma su sun fi karfin su aikata laifuffuka. Saboda su a matsayinsu, ba zai yiwu ma su aikata laifin bane, saboda zuciyarsu ba irin na wanda za su so su yi laifin bane.

Saboda haka ka ga in haka nan ne, sun kai mustawa ne da in suka yi abin kirki, ya zama abin yabo gare su. Wato ba wai an yi su ne kamar inji, wanda yake yana aikin kawai ba tare da ya san abin da yake yi ba. Suna da 'yancin zabi amma abu mai kyau suke zaba, ba su mummuna.

Shi ya sa ka ga Allah (T) yana yabon bayinsa Annabawa a cikin Alkur'ani, kamar yadda yake yabon Ayyub, yake cewa "Inna wajadnahu sabiran ni'imal abd innahu awwab." Mun same shi mai hakuri da dauriya, madalla da bawa mai yawan komawa da al'amarinsa zuwa ga Allah.

Da sauran yabo wanda aka yi wanda aka yi wa Annabawa, kamar Ibrahim da Isma'il da cewa shi mai cika alkawari ne, da ire-iren wadannan. Ka ga wato ayyuka kenan.

Abin da nake fata shi mai tambayar ya fahimta shi ne, matsayin isma ba matsayi ne da kake tsuwurwurta da aikinka ba, wanda yake wanda wani wanda yake in ya so sai ya yi ta yin aikin kirki sai ya koma ya zama irin shi ba. Wato kamar annabci, ba ana yin aiki ne mai kyau sai a zama Annabi ba. Da ma su Annabawa zababbu ne tun asali.

Haka ma matsayin Imamai, shi ma ba wani aiki ne mutum yakan yi in ya kai wani mustawa sai a ce yanzu ya zama ma'asumi ba, da ma can su Ma'asumai
Allah ya yi su haka nan ne. Shi kuwa
abin da muke cewa, su zababbu ne kuma
ayyukan daidai da matsayinsu ne.

___________________(83)_________________

TAMBAYA: Akwai wani hadisi da aka ce Allah ba ya karbar sallar wandanda suka yi hukunci da abin da ba Allah ya saukar ba. Menene ingancin wannan hadisin, kuma yaya matsayin sallar mutanen Nijeriya da suke bin dimokradiyya?

SHAIKH ZAKZAKY: Ko ba komai, wannan dai misdakin fadin Allah (T) ne, "waman lam yahkum bi ma anzalallahu…" Saboda haka ka ga ko da ma bai san ingancinsa ba ya san cewa aya ma ta zo da siga shigen irin wannan. Kuma in dai ya fahimci abin da yake nufi, abin da hadisin yake nufi, to sai ya yi kokari daidai gwargwado ya ga ya misaltu da wannan.

Amma dangane da hukunta matsayin wani, to wannan ai ba aikinmu bane. Mu ce ai tunda haka aka ce, to wane kaza ne. Shi dai wannan abin da hadisi ya ce kenan kuma ya yi daidai da ma'anar aya.
__________________(92)__________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ya nemi auren wata, har ya dauki hotunansa ya ba ta, ita ma ta ba shi nata, sai aka kada shi. Shin ya halatta ya ci gaba da rike hotunan nan nata, ita ma ta rike nasa?

SHAIKH ZAKZAKY: To, da ma dai dole ne ya zama akwai hijabi. Idan hotuna ne wadanda suke akwai hijabobi, wato abin da ya bayyana kawai shi ne wanda ya halatta a gani, to zai zama babu laifi da
shi. Amma idan hotunan ba hijabi, to tun farko da ma bai halatta gare shi ya mallaki hoton ba.

Saboda haka wannan dole ya mayar mata da kayanta, ba zai halatta gare shi ya rike hotuna din ba. In ba ta hijabi din nan, da ma tun asali ka ga an yi laifi kenan. Amma in tana da hijabi shi kenan ba wani laifi. Sai dai abin da ya fi dai tunda ba shi da wata bukata dangane da al'amarinta ka ga sai ya sallama mata kayanta. Shi ma shi ya fi, ko da tana da hijabin.

__________________(83)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne aka daura masa aure, sai ya mutu tun kafin a kai amarya. Shin matar za ta yi takaba kuma za ta ci gadonsa?

SHAIKH ZAKZAKY: Sai mu ce masa eh! Haka din ne. Abin da ake nufi da takaba shi ne ta zauna cikin reshin ado da kamanninta mai bakin ciki har wannan adadin. Sannan kuma tana da gadonsa.

___________________(84)__________________

TAMBAYA: Me mutum zai yi lokacin da ya kama matarsa da kwarto?

SHAIKH ZAKZAKY: To tunda shi kadai ne sai dai li'ani. Abin da zai iya yi kawai a shari'a shi ne li'ani, tunda shi ya gani ba kuma zai iya kawo shaidu uku tare da shi ba. Sai dai ya yi li'ani. Sai ya je ya kai ta kara ya ce ta yi zina tunda shi mijinta ne, in ta yarda ta yi zina sai a yi mata hukunci. In ta ce ba ta yi ba sai su yi li'ani. In suka yi li'ani shi kenan ba aure tsakaninsu har abada.

__________________(95)___________________

TAMBAYA: Akaramakallahu. Dabba ce ta zo gidan mutum tun tana karama har ta yi girma ta haihu, sai ya kama uwar ya sayar. To ya hukuncinsa yake?

SHAIKH ZAKZAKY: To, ita dai wannan dabbar dai ba tasa bace, ta mai ita ce. Saboda haka yana ajiye wa mai ita ne, duk ran da mai ita ya zo aka same shi, to zai mai da masa dabba, sai a biya shi ladan kiwo da sauransu.

Saboda haka in ya sayar da wadansu saboda wani dalili kamar ya ga alamar za ta gaza, sai ya sayar, to har kudin ma na mai dabbar ne. Da fatan yana nan yana yi wa mai dabban ajiya, kuma yana nan yana cigiya.

To har idan ya sami mai dabbar shi kenan sai sallama masa har da kudin wanda ya sayar din. In kuma bai samu ba, to daga karshe dai shi ba nasa bane, sai mu koma hukuncin kamar tsintuwa kenan, ya samu ya sarrafa wannan dukiya ta hanyar sadaka, da fatan Allah ya kai ladan ga mai wannan. Sai dai yana cire ladan kiwon da ya yi.

___________________(96)__________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mace na iya yin yayen danta, ko sai da yardar mijinta?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, idan ya cika lokacin yaye shi kenan. In ya cika shekara biyu shi kenan wa'adin yaye ya yi. Saboda haka ba sai ta nemi yardan mijinta ba. Amma in bai kai bane, to sai sun yi yarjejeniya tsakaninsu. Sai ya
yarda, ta yarda ; dole ne su biyu su yarda kafin a yaye shi kafin shekara biyu.

No comments:

Post a Comment