Monday, 26 May 2014

TAMBAYOYI DA AMSARSU TARE DA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

___________________(49)__________________

TAMBAYA: Akramakallahu. Na ji ana cewa duk mutumin kauye ba zai yi hankali ba sai ya shekara 40. Shin wannan gaskiya ne?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh! To hankali dai ba shi da dangantaka da kauye ko birni, akwai mara hankali a kauye akwai mara hankali a birni. Amma dai abin da muka sani shi ne, kamalar mutum, na kauye ne ko na birni, shi ne cika shekara 40.

Kamalar mutum namiji sai ya shekara 40, mace kuma shekara 33. Saboda haka dan shekara 40 ana daukarsa a matsayin dattijo.

___________________(50)__________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. 'Yan uwa ne suke zaune su biyu a gida guda kowanne da matarsa. Shin ya halasta dayan ya jagoranci matan salla ko da daya maigidan ba ya nan?

SHAIKH ZAKZAKY: Mu dai abin da muka sani shi ne salla dai akan yi jam'i, kuma jam'in nan yakan zama akwai liman da sahun maza sannan sahun mata, amma ba wani wanda yake tambayar dangantaka ta auratayya tsakanin Liman da wadda take bin salla.

Sau da yawa ma shi Liman bai san su waye suke bin shi salla ba. Abin dai da aka sani shi ne sahun maza sannan sahun mata. Su matan nan ba su da wani dangantaka ta zumunci ko ta auratayya da su da liman. Kuma ma bai san suna bin sa salla ba ma, bai ma san su ba. Ba a ma ce sai ya san su ba. Sune ma yake lazim su yi niyyar ibtida'i, ba shi ne yake niyyar zai jagorance su kan salla ba, in ba dai na Juma'a bane.

__________________(51)___________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ko dan uwa zai iya shiga dakin matar wani dan uwa yana nan ko ba yana nan tunda tana sa hijabi, saboda kusanci da shakuwar da suke da juna (su 'yan uwan)?

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da aka sani shi
ne ya haramta mutum ya kadaita da wata mata 'ajnaba,' wato wadda take ba matarsa ba ba kuma muharramarsa ba a dakin da ba zai yiwu a gan su ba ko da kuwa labule ne ya rufe, ko ma daji ne, falalen dajin da ba zai yiwu a gan su ba.

Ala ayyi halin, kadaici da matar da ba matarsa ta aure ba, ba muharrama ba, ya haramta. Kadaicin kuma yana nufin
ya zama ba a ganin su. Saboda haka in dai za su kadaita ba zai yiwu a gan su
ba, zai haramta. Ko da kuwa tana sanye
da hijabi.

____________________(52)_________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Nakan ji mutane suna cewa zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. Shin wannan gaskiya ne?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh da gaskene idan mummunan zato ne, saboda zato akwai kyakkyawa akwai mummuna. To mummunan zato shi ba shi da kyau, saboda haka shi ne zunubi.

Alal misali, in ka ga wani tare da wata suna tafiya, to kada zuciyarka ta sawwala maka cewa wannan yana nufin tsakaninta da shi akwai wani abu. Sai ka ce, wane ne da matarsa ka wuce abinka.

To amma in ka munanan zato cewa yana nufin kaza ne, to ka ga ka fada cikin zunubi, ko da kuwa wannan abin da ka fada din gaskiya ne.

__________________(53)___________________

TAMBAYA: Akramakallahu. Dan kasuwa ne ya fara kasuwanci da 100,000, da shekara ta zagayo sai suka zama 200,000. Idan zai fitar da khumusi zai hada da uwar kudin ne ko a ribar kawai zai fitar?

SHAIKH ZAKZAKY: A riba kawai zai fitar da khumusi. Shi kuwar kudi tunda shi ake jujjuyawa, ba abin da ya hau kansa.

Da a ce ajiye uwar kidin ya yi bai juya ba sam-sam, to da shi ne sai ya hau uwar kudin, amma tunda ya juya shi, to abinda ya hau shi ne zai fid da khumusi a kai.

__________________(54)___________________

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Mahaifiyata ta kamu da ciwon da ya yi sanadiyyar rasuwarta, kuma ya zamana ba ta sami damar yin azumin watan Ramadan ba, kuma ni kadai ne danta. Shin ya kamata na rama mata azumin nata da ba ta yi ba? Kuma yaya zan rama din?

SHAIKH ZAKZAKY: Ya ma wajaba ne, idan ya zama a surar cewa za ta iya ramawa amma ba ta sami ramawa ba.

Amma idan a surar da ba ma za ta iya ramawa bane, kamar ta rasu a cikin rashin lafiyan kuma ba ta warke ba, ko a Ramadanan ma, to zai zama mustahabbi ne, ba wajibi ba ya rama mata.

Kuma yadda zai rama din yadda duk ya yi masa sauki ne, ba a ce lallai ya jera kamar yadda ta bari ba. Abin dai da zai biya shi ne adadin kwanakin da ta sha. Duk yadda ya saukaka masa da niyyar cewa yana rama mata azumi ne.

__________________(55)___________________

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Na kasance nakan kwana da niyyar azumi ba tare da na yi sahur ba, shin ya inganta?
Alkasim Zakariyya kasuwar Barci Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: Eh! Ya inganta saboda ba a shardanta sahur a sharuddan niyya ba. Abin da yake sharadi kawai shi ne ya kwana da niyyar zai yi azumi ne, shi kenan ya wadatar.

Wato da a ce mutum zai yi niyyar azumi da daddare, amma sai ya manta har ya wayi gari, to in ya tuna, yana nan yana azuminsa. Ba a ce sharadi ne sai ya tuna lokacin sahur ballantana ma cin sahur.

Cin sahur kuwa yana da kyau ne, bai zama sharadi a ingancin azumi ba ballantana niyya.

___________________(56)__________________

TAMBAYA: Akramakallahu. Ina mai da hankali sosai a wajen addu'o'in Ma'asurat na safe da yamma fiye da karatun Alkur'ani. Ko ina da laifi?

SHAIKH ZAKZAKY: To ya kamata ka yi 'balance' ne, ya zama kana karatun Alkur'ani kuma kana addu'a. Domin ya zo a Hadisi cewa wanda karatun Alkur'ani ya shagaltar da shi da ga barin addu'o'i, Allah zai ba shi fiye da wanda yake ba masu addu'a. Saboda haka karatun Alkur'anin ya fi addua din.

Amma ala ayyi halin ba a ce ka yi daya ka bar daya ba, duk biyun za ka yi. Kamar yadda kake mayar da hankali wajen addu'o'i, to ka kuma mayar da hankali wajen karatu Alkur'ani, ka yi su duka. Duk ka mayar da hankali ka yi ta ta yi.

No comments:

Post a Comment