TAMBAYA: Shin ina matsayin cin abinci da wanda ba musulmi ba, ko wanda ba musulmin ba ya ci ya rage?
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai akwai daukar wulakanci a ciki, kuma abin da duk za ka yi ya zama ya wulakanta matsayin musulmi da Musulunci dole ka bar shi. In dai da daukar wulakanci.
Allahuma sai dai bisa ta fuskacin lalura.
___________________(142)_________________
TAMBAYA: Mutane na cewa wai in talauci ya dame ka, to ka kara aure. Yaya wannan hadisin?
SHAIKH ZAKZAKY: To ban san me ya sa ya ce masa hadisi ba? Tunda mutane ne suke cewa, sai ya ce ya fadin wadannan mutanen? Sai in ce kila su mutanen al'adarsu ce ko camfinsu. Amma dai cewa hadisi, ba gaskiya ne ba.
Ko da akwai wani abu da suka kira shi hadisi, to ba shi da wani tushe
________________(143)____________________
TAMBAYA: Mutum ne matarsa ta mutu tana bin sa bashi har N1500. Shin yaya zai biya ta?
SHAIKH ZAKZAKY: To zai biya bashin ne a yayin da za a raba gadonta. In ma babu, sai ya sanar da cewa tana bin sa bashi, alabashi tunda yana da gadonta kila kason ya fada a abin da shi zai gada, sai ya zama ba sai ya biya ba kenan.
___________________(144)_________________
TAMBAYA: Mutum ne bayan ya gama sallah yana sauraren wata sallar sai maziyyi ya fito masa. Yaya alwalarsa?
SHAIKH ZAKZAKY: To ai maziyyi ba shi daga cikin abubuwan da suke warware alwala. Yana da kyau mutum ya karanta babin abubuwan da ke warware alwalla ya gani a cikin 'Risala amaliyyan'.
__________________(145)__________________
TAMBAYA: Ina so Malam ya yi mani bayanin yadda ake yin taimama a Jafariyya da kuma niyya.
SHAIKH ZAKZAKY: To wannan yana da kyau ya zama ya karanta ne a cikin Risala amaliyya, domin ita taimama tana da wadansu abubuwa da suka shafe ta wadanda suka shafi ba kawai yadda ake yin ta ba, har da dalilan da ke sa a yi ta.
To, kuma a takaice dai, ana bugun kasa ne da ma'anar bugu, a shafi goshi da gira har ya zuwa doron hanci da wani abu na kunci da hannuwa biyu, sannan sai a shafi bayan dama da cikin hagu. Sannan a shafi bayan hagu da cikin dama, kowanne daga gaba zuwa karshen yatsu.
Sai dai na fi son ya karanta don akwai wadansu abubuwa baya ga 'kaifiyya', ba kawai yadda ake yin ne shi kenan ba.
___________________(146)_________________
TAMBAYA: Ni ina kiran Wana da Yaya kamar yadda mahaifiyata ta koya mani, amma ni kuma 'ya'yana suna kiran Yayyensu da sunayensu. Ko akwai Laifi?
________
SHAIKH ZAKZAKY: To al'adar mutane ne, kuma yana dai da kyau abubuwa irin na ladabi a ce ana koya wa yara irin wannan. Ba ma kawai babu laifi ga yi bane, muna iya cewa ma yana dai da kyau a koyar da mutane abubuwa irin na ladabi.
Kamar yadda yake ce wa wansa Yaya, to ya koyawa 'ya'yansa na kasa ya rinka kiran na gaba da Yaya, shi kuma Baba a ce masa Baba ko Abba ko abin da ya yi kama da haka nan. Ita kuma mahaifiya a kira ta Umma ko Mama ko abin da ya yi kama da haka nan, a daina kiran su da sunayensu, tunda ana ganin wannan ba ladabi bane.
_________________(147)___________________
TAMBAYA: Na kasance bayan kabbarar harama da kuma sujuda ina yin wasu addu'o'i. Ko ya dace?
_________
SHAIKH ZAKZAKY: In ma'asurai ne, domin akwai addu'o'i ma'asurai wadanda ake yi bayan kabbarori din, to babu laifi. Amma in ba ma'asurai bane, to sai mu ce abin da ya fi kawai kada ya yi.
Kada ya kirkiro wata addu'a da shi ne yake yi don kashin kansa. Amma in ma'asurai ne wanda aka samu, wato an ruwaito kenan, bayan kabbarar harama wanda akan yi har guda bakwai - bayan ukun farko akwai abin da ake fada, bayan biyu akwai da kuma bayan wasu biyu din kuma da wadansu addu'o'in ma'asurai - babu laifi.
No comments:
Post a Comment