Wednesday, 28 May 2014

HUKUNCE-HUKUNCENADDAI


HUKUNCE-HUKUNCEN ADDINI
Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi - mustahabbi- a garemu.
Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma hakika yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Sai dai wasu daga daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali.
Kamar yadda suka halatta wa Allah ya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Hakika ya gabata cewa wannan magana akwai ketare iyaka -sabo- mai girma a cikinta, ba domin komai ba sai domin lizimta danganta jahilci da gazawa ga Allah (S.W.T).
A takaice dai abin da yake ingantacce a yi imani da shi, shi ne : Ubangiji madaukaki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa.

No comments:

Post a Comment