To alal akalla kada mu yi haka da abokan gabanmu na daga kwayoyin cuta.....shin za mu yi haka da sauran nau'in kwayoyin cuta, wato kwayoyin cutar munanan ayyuka?.
Akwai wata kissa ta sahabban Annabi (s.a.w.a.) lokacin da suke tare da shi a wani bushasshen guri kuma ga shi ana tsananin sanyi. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tambaye su ko za su iya tattaro itatuwa don su kunna wuta da kuma jin dumi?
Sai dukkan sahabban suka ce: babu tsiro ko bishiya a wannan wuri ya ya za su iya hado itatuwa?
Sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce musu: to kowannen-ku ya tafi ya nemo abin da ya sawwaka.
Sai sahabbai suka bazama don nemo duk wani abin da suka gani na daga kayoyi da busassun tsirrai, daga nan sai suka zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da itatuwa masu yawan gaske.
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) yace musu, da haka ne kananan zunubai suke taruwa da yawa kamar yadda kuka tattaro wadannan itatuwa. Sannan kuma ya ce musu: ina gargadinku da kananan zunubai.
Shin muna daga cikin wadanda ba sa gani face abubuwan da suke gaban kafufunsu, kuma ba sa ganin abubuwan da za su faru nan gaba sannan kuma suke jahiltar karshen al'amurra?
Da wuya ace dokin da ke daure a jikin injin tatsan rake don jujjuya shi, kamar yadda ake yi a da ko kuma a halin yanzu a wasu wurare, zai nuna bacin rai kan wannan aiki ga shi kuwa yana tafiyar dubban mila-milai ba tare da ya bar inda yake ba.....
Mai yiyuwa ne hakan ya faru saboda shi abin da ke gaban kafafuwansa kawai yake gani, to amma wanda yake ganinsa daga nesa da kuma wajen injin zai tausaya masa halin da yake ciki.....
Shin muna daga cikin wadanda suke ba da muhimmanci ga harkokinsu ne kawai?
Idan har al'amarin haka ne, to mun kasance kamar kwadon da ke cikin rijiya kuma ba ya so ya bar cikinta, amma yana ganin duniya kawai ita ce abin da ke kewaye da wannan rijiya, bai san abin da ke wajen wannan rijiya ba da suka hada gonaki da sauran ruwayen da suke gudu a wajen rijiyar.
Shin muna daga cikin mutanen da suke fara tafiya ba tare da sun duba kawukansu ba?
Hakan shi ne yanayin matafiyin da ya zabi batacciyar hanya ba tare da kula da alamomin da suke gefen hanyar ba, sannan kuma bai tambayi kowa ba...to matukar dai wannan matafiyi ya ci gaba a irin wannan yanayi, to babu yadda za a yi ya kai ga inda yake son zuwa ko da kuwa ya kara saurin tafiyarsa don saboda karin nisan inda zai je din.
Shin muna daga cikin mutanen da suke barin aikata ayyukan alheri har zuwa wani lokaci?
Alal misali, mu ce akwai isasshen lokaci a nan gaba da za mu aikata alheri.....ko kuma mu ce mu har yanzu yara ne da ba mu da wani nauyi a kanmu, da dai makamantan irin wadannan maganganu da kuma tunani.....
Hakan kuwa yana nufin kenan muna son mu bar kofofin sharri a bude ba tare da mun bude na alheri ba.....bayan dan wani lokaci sai mu ga ma'ajiyar zuciyarmu ta cika da sharri; don kuwa mun riga mun rufe kofofin alheri ba tare da mun ba shi daman cika zukatanmu da kuma kawata rayuwarmu ba.
Shin muna abota da ashararai ma'abuta munanan ayyuka ne?
Shin a shirye muke mu kulla alaka da irin wadannan mutane?
Idan haka ne kuwa, to za mu karfafa hannayen sharri a tattare da mu kenan ta yadda a sannu-sannu za mu fada cikin rijiyar bala'insa; don kuwa kusanta hannun sharri da kuma misaltuwa da shi yana nesanta mu daga hannayen alheri ne.
Shin za mu yi amfani kwakwalwarmu da kuma ci gaba da shirye-shiryenmu na kyawawan dabi'u?
Idan har muka bari kwayoyin cutar sharri suka shiga cikin wadannan shirye-shirye namu, shin muna neman wata hanya mafi saurin da za mu fitar da su? Kamar yadda muke yi ga kwamfutocinmu da suke cikin gidaje, ko kuma kamar yadda muke yi a makarantu da kuma wuraren ayyukanmu.....
Akwai tambayoyi da yawan gaske da muke tam-baya don sanin hanyoyin da sharri yake bi wajen shiga rayuwarmu. Misali, muna iya tambaya, shin muna daga cikin mutanen da suke damuwa da adon zahiri da kuma adon tufafi da dai sauransu? Ko kuma muna damuwa da kawan badini da kuma kyawawan dabi'u?
Kana kuma, shin muna iya bambance alheri da sharri?
Mai yiyuwa ne sharri ba zai bayyana mana a matsayi mai muni ba, face dai zai zo mana ne da yanayi mai kyau yana hade da guba da kuma zuma.....
Don haka mu kula da sharri dukkan kula musam-man ma idan ya sanya tufafin alheri.
Hakika mafi kyawun tafarkin gano sharri ko kuma hakikanin ayyukan da ake kiransu da sharri da munanan ayyuka ko kuma zunubai shi ne mu yi dubi cikin karshe da kuma sakamakonsu.
To daga cikin sakamako da kuma karshen wadannan ayyuka akwai, tabewa, shaye-shaye, aikata muggan laifuffuka, shiga gidan yari da dai sauransu.....
Daga karshe muna iya cewa alheri shi ne yada kyawawan siffofi cikin rayuwarmu da kuma rayuwar wadanda suke kewaye da mu.....hakan kuwa yana nufin amfani da kuma jin dadin ni'imomin rayuwa da kuma kyawunta tare da kwanciyar hankali, daidaituwa da kuma sa'ada.
Sannan kuma ba makawa sharri ba zai samar mana da hakan ba, face dai zai bayyana cewa zai samar mana da hakan ne, amma karya ce kawai.
Shin rayuwar son kai ba tare da kula da sauran mutane ba yana daga cikin alheri? Shin yana daga cikin alheri mutum ya dinga wasa da abinci alhali kuwa miliyoyin yara suna mutuwa da yunwa?
Irin wadannan tambayoyi sukan samu yin tunani don zaban rayuwar da za mu yi don kada mu fada cikin sharrin da wasunmu suka fada. Sannan kuma mu yi amfani da damar rayuwa wajen tafarkin kiyaye mutum da al'ummarsa daga hatsarori da kuma matsalolin rayuwa.
Daga Karshe....
Ba abin da za mu ce a karshen wannan dan karamin littafi, "Shingen Matasa", face dai muna kira ga masu karatu, membobin "Dandalin Matasa", samari da 'yan mata da su rubuta mana ra'ayoyinsu kan wannan littafi da kuma abin da ya kumsa.....
Muna maraba da duk wanda yake ko take son ya/ta aiko da ra'ayinsa/ta a wannan dandali, kana kuma muna maraba da duk wanda yake ko kuma take son taimakawa da ra'ayinsa/ta wanda zai taimaki matasa..
Hakika duk wani taimako daga gare ku zai kasance abin alfahari gare mu.
No comments:
Post a Comment