Allah madaukaki ya kwadaitar da bayinsa muminai a kan tawassuli ya kuma halatta tawassuli nau’i daban-daban, daga ciki zamu zo da wani nau’in daga cikin:
A- Tawassuli Da Sunayen Allah (S.W.T)
Fadinsa mai girma da daukaka; “Sunaye kyawawa na Allah ne, ku kira shi da su, ku bar wadannan da suke shisshigi a cikin sunayensa, da sannu za a saka musu da abin da suke aikatawa” [28]. Wannan aya tana siffanta mana sunayen Allah dukkansu da kyawawa ba tare da bambanci ba, sannan sai ta umarci da a yi addu’a da wadannan sunaye.
Yayin da bawa yake ambaton sunayen Allah da suke dauke da dukkan alheri da kyau da rahama da gafara da izza, sannan sai ya gabata zuwa ga Allah yana mai neman gafara daga zunubbansa da neman biyan bukata, sai Allah ya amsa addu’ar mai tawassuli da sunayensa.
B- Tawassuli Da Kyawawan Ayyuka Na Gari
Aiki na gari yana daga abin da ake tawassuli da shi a shar’ance wanda ta hanyarsa bawa yake samun kusanci zuwa ga Allah (S.W.T), tunda tawassuli yana nufin sanya wani abu gaba zuwa ga Allah domin neman yardarsa, to ba makawa aiki na gari yana daga mafi girman tsani da bawa yake riko da shi domin biyan bukatunsa. Allah madaukaki ya ce: “Yayin da Ibrahim yake daukaka ginshikan gini da Isma’ila (suka ce): Ya Ubangiji ka karba daga garemu hakika kai mai ji ne masani. Ya Ubangiji ka sanya mu masu mika wuya gareka daga kuma zuriyarmu a samu wata al’umma mai mika wuya gareka, ka kuma nuna mana wurin ibadarmu, ka karbi tubanmu kai ne mai karbar tuba mai jin kai” [29]. Ayar a nan tana karfafa dangantaka tsakanin aiki na gari da kuma addu’a da Ibrahim (A.S) yake neman a biya masa na zuriyarsa ta zama al’umma ta gari.
Kamar yadda yake karfafawa da fadinsa Allah (S.W.T): “Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu mu mun yi imani, ka gafarta mana zunubbanmu ka kuma kare mu azabar wuta” [30]. Sai a nan ya gwama tsakanin neman gafara da imani da nuna alakar imani da neman gafarar.
C- Tawassuli Da Addu’ar Manzo (S.A.W)
Kur’an ya yi nuni zuwa ga wannan matsayi da daukaka da manzo yake da ita wajan Allah, da kuma bambancinsa da sauran mutane, da fadinsa; “Kada ku sanya addu’ar manzo tsakaninku kamar addu’ar sashenku ga sashe” [31]. Kuma ya yi nuni da cewa manzo (S.A.W) shi ne dayan aminci biyu a duniya, da fadinsa: “Allah ba zai azabtar da su ba alhalin kai kana cikinsu, kuma Allah ba mai azabtar da su ba ne alhalin suna masu istigfari” [32].
Sannan mun samu Kur’ani a wurare masu yawa yana gwama ambatonsa da manzo yana mai raba musu aiki daya, yana cewa: “Da sannu Allah da manzonsa zasu ga ayyukanku sannan sai a mayar da ku zuwa ga duniyar boye da sarari” [33]. Yana kuma cewa: “Ba su saba ba sai domin Allah da manzonsa sun arzuta su daga falalarsa” [34]. Da sauran ayoyin da sunan annabi ya zo tare da sunan Allah a hade, idan wannan matsayi ne wanda manzo yake da shi a wajan Allah kuma ba a mayar da addu’arsa ana kuma amsa ta, to riko da addu’arsa riko ne da wani rukuni mai karfi.
Shi ya sa zamu ga Allah (S.W.T) yana umartar masu zunubi na daga musulmi da su yi riko da addu’arsa da yin istigfari a majalisinsa, suna tambayarsa ya nema masu gafara domin istigfarinsa yana zama sanadin saukar rahama da kuma karbar tubansu, Allah ya na cewa; “Ba mu aiko wani manzo ba sai domin a bi shi da izinin Allah, da dai cewa su yayin da suka zalunci kawukansu sun zo maka sai suka nemi gafarar Allah sai annabi ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai rahama” [35].
Da fadinsa madaukaki: “Idan aka ce da su ku zo manzon Allah zai nema muku gafara sai su karkata kawukansu ka gan su suna masu juyawa suna masu girman kai” [36].
D- Tawassuli Da Addu’a Ga Dan’uwa Mumini
Madaukaki ya ce: “Wadanda suka zo bayansu suna cewa ya Ubangijinmu ka gafarta mana da kuma ‘yan’uwanmu da suka rigaye mu da imani, kada ka sanya mugun kuduri a zukatanmu ga wadanda suka yi imani, ya Ubangijinmu kai ne mai tausayi mai rahama” [37].
Wannan aya tana nuna cewa muminai masu zuwa suna neman gafara ga ‘yan’uwansu, wannan kuwa yana nuna yi wa dan’uwa addu’a mustahabbi ne.
E-Tawassuli Da Annabawa Da Salihai Kansu
Wannan nau’in ya bambanta da maganar da ta gabata ta tawasssuli da addu’ar annabi, domin a nan tawasuli ne da zatin su annabawa da salihai da sanya su tsani domin amsa addu’a da kuma nuni zuwa ga matsayin da suke da shi wajan Allah madaukaki.
Idan mun kasance muna tsani da addu‘ar manzo a wajan Allah to a nan zamu sanya shi kansa manzo da karamarsa su zama tsani zuwa ga Allah ne. Sanannan abu ne cewa tawassuli da addu’ar da ta zo daga wannan mutum mai daraja da Allah ya daukaka ya girmama kamar yadda yake fada: “Mun daukaka maka ambatonka” [38]. Ya kuma umarci musulmi da su girmama shi da daukaka shi, da fadinsa: “Wadanda suka yi imani da shi suka kuma karfafe shi suka taimake shi, kuma suka bi hasken da aka saukar tare da shi, wadannan su ne masu rabauta” [39].
Idan ya kasance madogarar amsa addu’arsa shi ne shi kansa manzo (S.A.W) da yake da matsayi mai girma wajan Allah, to ashe kenan shi ya fi cancanta mutum ya yi tawassuli da shi kamar yadda yake tawassuli da addu’arsa, wanda ya yi furuci da halaccin na farko ya haramta na biyu, to ya raba tsakanin abu biyu da suke lizimtar juna. Wannan nau’in tawassuli akwai ruwayoyi da suka zo da suke karfafarsa da sanadai masu inganci da masu ruwayar hadisai suka yarda da shi[40].
F-Tawassuli Da Darajar Salihai Da Alfarmarsu Da Matsayinsu
Wanda ya bi tafarkin musulmi zai same su suna da wannan nau’i na tawassuli da matsayin salihai da kuma darajarsu gun Allah.
Muslim ya rawaito daga Mu’azu Dan Jabal ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin ka san hakkin Allah a kan bayi? Sai ya ce: Sai na ce Allah da manzonsa su ne mafi sani, sai ya ce: Hakkin Allah a kan bayi su bauta masa kada su tara wani abu da shi, sannan sai ya tafi kadan sai ya ce: Ya Ma’azu! Sai na ce: Amsawarka ya manzon Allah! Sai ya ce: Kasan hakkin bayi a kan Allah idan suka yi hakan? Sai na ce: Allah da manzonsa su ne mafi sani, sai ya ce: Kada ya azabtar da su” [41].
Ya bayyana cewa Kur’ani ya riga ya kawo mana tarihin annabawa da salihai daga bayinsa game da tawassuli, sannan sai ya kawo mana wasu nau’i na tawassuli da ya halatta, kuma bai kebanta da addu’a ba, ballantana a rarrabe tsakanin zatin annabi da addu’arsa, domin ya hada da zatin annabi kuwa.
No comments:
Post a Comment