Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ce:
"Ni ina kin a ce mutum ya mutu alhali akwai wata ta'adar Manzon Allah (s.a.w.a.) da ta rage bai aikata ba[207]".
Babu shakka Ahlulbaiti (a.s) sun ba da muhimmanci kwarai wajen ilmantarwa da tarbiyyar mabiya da sahab-bansu da kuma shiryar da su zuwa hanya sahihiya ta tabbatar da rayuwa irin ta mai akida da halayen kwarai da biyayya ga hukumce-hukumcen Musulunci. Sun karfafa kan gina tarbiyyar musulmi bisa dacewa da Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) domin samar da gwarzaye masu daukar hasken Musulunci da kira zuwa gare shi ta yadda hasken zai watsu kan sauran jama'a su amfana da ilmi da kuma aiki. Ahlulbaiti (a.s) sun yi hakan ne saboda tabbatar da haraka ta Musulunci cikin al'ummar duniya bayan da muggan manufofin masu neman ruguza addini suka bayyana ko ina. Muna iya ganin wannan kokarin nasu a fili cikin halayensu da wasiyyoyinsu da tarbiyyarsu ga mabiyansu. Daga cikin maganganun Imam Bakir (a.s.) akwai raddi kan masu cewa duk wanda ya kaunaci Ahlulbaiti (a.s) ba ya bukatar lizimtar farilloli Musulunci. Imam ya bayyana musu tafarkin Musulunci na gaskiya wanda Ahlulbaiti (a.s) suke kai, kuma suke kaunar dukkan musulmi ya yi riko da shi. Idan ba ka san shi ba, to shi ne tafarkin ilmi da akida ta gaskiya da aiki da duk abin da Alkur'ani ya zo da shi, Annabi (s.a.w.a) kuma ya iyar da shi ya kuma rayu a kansa. Imam din ya ce:
"Wallahi ba mu da wata kubuta daga Allah, babu wata dangantaka tsakaninmu da Allah, ba mu da wata hujja a kan Allah, kuma ba a kusantar Allah sai da biyayya. Wanda ya zama mai biyayya daga cikinku to jibintarmu za ta amfane shi, wanda kuwa yake mai sabo daga cikinku, jibintarmu ba za ta amfane shi ba[210]".
Amru bn Sa'id bn Hilal ya ce da Abu Ja'afar (a.s.): 'Allah Ya sanya ni fansar ka! Ni da kyar nake saduwa da kai, sai dai bayan shekaru, to ka yi mini wasicci da wani abin da zan rika', sai ya ce masa:"Ina maka wasicci da tsoron Allah da tsantsaini da kokari, ka sani cewa tsantseni ba ya amfani sai tare da kokari[211]".
Daga cikin abin da Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci da shi ga wani mabiyinsa, Abu Usama ya kuma umurce shi da ya isar da shi ga sauran mabiyansa, shi ne cewa:
"Ku ji tsoron Allah ku kasance ado a gare mu, kada ku zamo abin kyama. Ku janyo mana dukkan soyayya, ku ije mana duk wani mugun abu, domin mu ba kamar yadda aka fada dangane da mu muke ba. Muna da hakki cikin Littafin Allah da dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da tsarkakewa daga Allah, da haifayya tsarkakakkiya, ba mai ikirarin hakan, koma bayanmu, face makaryaci [212]. Ku yawaita ambaton Allah da tuna mutuwa da karatun Alkur'ani da salatin Annabi (s.a.w.a) domin akwai (ladan) kyawawan aiki goma ga ko wane salati a gare shi [213]".
Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci wa Isma'il bn Ammar, daya daga cikin sahabbansa, da cewa:
"Ina ma wasicci da tsoron Allah da tsantseni da gaskiya cikin magana da mai da amana da kyautatawa makwabta da yawan sujada, don da wannan ne Annabi (s.a.w.a) ya umurcemu[214]".
Hisham bn Salim ya ce: 'Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana fada wa Hamran cewa:
"Ka dubi wanda ya kasa ka, kada ka dubi wanda ya fi ka, domin haka ya fi (tabbatar da) wadar zuci ga abin da aka yanka maka, kuma za ka fi cancantar kari daga Allah. Ka sani cewa kadan na dawwamammen aiki wanda aka yi yakini, a wajen Allah, ya fi mai yawa dawwamamme amma babu yakini a cikinsa. Ka sani cewa babu tsantsenin da ya fi nisantar ababen da Allah Ya haramta, da kuma kamewa ga barin cutar da musulmai da yi da su. Babu kuma abin da ya fi kyan hali faranta rai. Kuma babu dukiyar da tafi amfani daga wadatuwa da kadan mai biyan bukata. Babu jahilcin da ya fi jiji da kai daci[215]".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan siffofin muminai cewa:
"Wanda ya yi bakin cikin mummunan aikinsa, ya yi farin ciki da kyakkyawan aikinsa, to mumini ne[216]".
Wadannan bayanai suna nuna siffar mumini mai riko da addini irin wanda Ahlulbaiti (a.s) suka yi kokarin samarwa kuma wannan shi ne tafarkinsu na tarbiyyar al'ummar musulmi. Shi ne kuma kiran da suka yi wa al'ummar Annabi (s.a.w.a) na lizimtar Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.) da gina rayuwa bisa wannan shiriya da tafarki mai karfi. Babu abin da ya fi dacewa ga musulmi sai bin shiryarwarsu da wasiccinsu da kuma wa'azinsu.
No comments:
Post a Comment