Sunday, 25 May 2014

GUDUN MOWAR AHLULBAITI {a.s} A FAGEN SIYASA


Babu shakka al'ummar musulmi ta san matsayin Ahlulbaiti (a.s) da hakkinsu a kan wannan al'umma na shugabantarta. Domin haka ne za a iya ganin cewa Ahlulbaiti (a.s) suna matakin kololuwa a fagen siyasa da shugabancin Musulunci, domin su shiryar da al'umma, su tabbatar da gyara da aiwatar da hukumce-hukumcen addini da tsayar da adalci.
Duk wanda ya karanci tarihin Musulunci zai gani a sarari cewa shugabantar al'umma bayan zamanin Khulafa'u al-Rashiduna ta koma mulukiyya mai dora kanta bisa bayin Allah da jan hankulansu da dukiya da mukamai da kuma dankwafe hukumce-hukumcen shari'a da wasa da su. Wannan wasa da shari'a da makomar al'umma ya janyo sassabawa da juyin-juya-hali da jayayya mai tsanani da zubar da jinin kungiyoyi masu sabanin ra'ayoyi da tunace-tunace masu warware juna sun zama sakamakon wannan. Wasunsu suna goya wa sarakuna baya kan zaluncinsu da kuma horar da mutane su mika wuya da hana su bijirewa da warware mubaya'arsu ga azzalumai. Wasu kuma sun yi amfani da wannan damar (ta jayayya tsakanin musulmi) wajen tabbatar da mugun nufinsu na ruguza addini yayin da suka dora kira da halalta dukkan haram da dukiyoyi da mata da rusa wajibai, kungiyoyi irinsu 'yan Karamida, Mazdakiyya da Kharmiyya da dai sauransu. Wasu kuma suka dora kira zuwa ga rudani da rusa dukiyar hukuma da zubar da jini da kafirta kowa da kowa kamar su Khawarijawa.
Da wannan fantsamar ra'ayoyin siyasa masu sassabawa da fitinu da yake-yake na cikin gida, al'umma ta fuskanci hadari mai munin gaske. Ahlulbaiti (a.s), a matsayinsu na jagororin al'umma, sun kasance mafus-kanta da tushen sakon Musulunci wanda duk wata mishkila ta akida da tunani wacce ta kalubalanci musulmi ana iya warware ta a hannunsu. Domin wannan matsayi nasu na matabbacin tafarkin gaskiya, musulmi suna bin ra'ayinsu da riko da matsayin da suka dauka kan al'amurra. Face wadanda suka damfaru da masu iko, masu kare ayyukansu domin biyan bukatar kansa.
A nan za mu yi dubi cikin tafarkin Ahlulbaiti (a.s) akan abubuwan da suka shafi ayyukan siyasa.

No comments:

Post a Comment