Sunday, 25 May 2014

AMSA WA MASU MUSUNTA HALASCIN TAWASSULI


A- Suka ce: Bai kamata ba a yi tawassuli da matattu, wannan aiki ne mummuna a hankalce, saboda matacce ba shi da iko a kan amsawa, tawassuli da shi magana ce da rasasshe[60].
Amsa: Wannan magana tasu ba daidai ba ce saboda ta ci karo da Kur’ani mai girma, ga kuma misalai kan hakan daga ayoyin da suke kore cewa mutuwa rashi ce.

1- Fadinsa: “Suna da arzikinsu (abincinsu da abinshansu) safe da yamma” [61]. Wannan aya ta sauka game da muminai domin tana bayyana nau’in kiyaye wa garesu duniya da lahira.

2- Wacce ta fi wannan aya karara: “Wuta ce da ake bujiro da su gareta safe da yamma, kuma a ranar kiyama (sai a ce) ku shigar da alayen fir’auna mafi tsananin azaba” [62]. A nan Allah yana bayyana abin da masu sabo da kafirai suke ciki na azaba a duniyar barzahu, wanda wannan yake nunawa cewa su rayayyu ne bayan mutuwa kafin alkiyama. Domin ambaton ranar kiyama ya kasance ne bayan bujuro da su ga wuta safe da yamma.
B- Suka ce: Idan ma ya tabbata cewa mutuwa ba karewa ba ce ita ma rayuwa ce, shin zai yiwu a yi alaka da matacce ko ba zai yiwu ba? Domin rayuwar barzahu zata hana iya samun alaka da shi.
Amsa: Abin da yake nuna yiwuwar alakar mutum rayayye a wannan duniya da mutum da yake rayayye a duniyar barzahu ya zo a cikin Kur’ani mai grma daga ciki akwai:

1- Kiran Annabi Salihu (A.S) mutanensa zuwa ga bautar Allah, ya kuma umarce su da kada su taba mu’ujizarsa -taguwa- da sharri, bayan sun soke taguwa sun yi shisshigi kan al’amarin ubangijinsu Allah ya ce: “Sai tsawa ta rike su sai suka wayi gari suna masu gurfanawa a cikin gidajensu. Sai ya juya ga barinsu ya ce: Ya ku mutane na isar da sakon ubangijina na yi muku nasiha sai dai ku ba kwa son masu nasiha” [63].
Sai muka ga Allah yana bayar da labari yanke da cewa al’ummar Annabi Salihu (A.S) ta wayi gari a gidajensu a gurfane, bayan nan kuma Annabi Salihu yana juya musu baya yana mai magana da su yama mai cewa: “Na isar da sakon ubangijina na yi muku nasiha sai dai ku ba kwa son masu nasiha” [64].
Magana ta zo ne daga Salihu (A.S) bayan an halakar da mutanensa da mutuwarsu, da karina ta cewa sai ya juya ga barinsu.

2- Annabi Shu’aibu (A.S) ya yi wa mutanensa magana bayan halakarsu da fadin Allah (S.W.T): “Sai ya juya ga barinsu ya ce: Ya ku mutane hakika na isar da sakon ubangijina gareku na kuma yi muku nasiha, to yaya zan yi bakin ciki a kan (abin da ya samu) mutane kafirai” [65].
Maganar Annabi Shu’aibu (A.S) ga mutanensu ya zo ne bayan halakarsu, wannan kuwa yana karfafa yiwuwar haduwa da su, ba don masu halaka da wannan tsawa sun kasance suna jin maganar Annabi Shu’aibu (A.S) ba to menene ma’anar yi musu magana’.
Kuma ba yadda za a yi a fassara cewa maganar kaico da ya yi, magana ce ta nuna jin zafinsa domin wannan ya saba wa zahirin abin da ya kunshi dokokin tafsiri.
Amma hadisai madaukaka masu yawa sun zo suna nuna yiwuwar alakar kamar haka:

1- Abin da aka rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa ya tsaya a gefen rijiyar kalib a Badar ya yi magana da mushrikai da aka kashe aka kuma jefa jikunkunansu a kalib.
Daga Anas dan Malik ya ce: Sahabban manzon Allah (S.A.W) sun ji shi a cikin dare yana cewa: “Ya ku mutanen Kalib, ya Utba dan Rabi’a! Ya Shaiba dan Rabi’a! Ya Umayya dan Khalaf! Ya Aba Jahal dan Hisham! Sai ya kirga duk mutanen da suke cikin Kalib; Shin kun sami abin da ubangijinku ya yi muku alkawari gaskiya ne? Ni na samu abin da ubangijina ya yi mini alkawari gaskiya ne. Sai musulmi suka ce: Ya manzon Allah! Kana kiran mutanen da sun zama mushe? Sai ya ce: Ku da kuke nan ba ku fi su jin abin da nake fada ba, sai dai su ba sa iya amsa mini[66].

2- Musulmi dukkaninsu sun tafi a kan yin sallama ga manzo (S.A.W) a salla, a yayin karewa suna cewa: Aminci ya tabbata gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarsa. Wannan sallama tana nuna yiwuwar alaka da ruhinsa (S.A.W) kai tana nuna wajabcin faruwarsa ne.

3- Ya zo daga gareshi (S.A.W) cewa: “Wanda ya ziyarce ni bayan wafatina ya yi mini sallama zan amsa masa sallama goma, kuma mala’iku goma zasu ziyarce shi suna masu yi masa sallama, wanda ya yi mini sallama a cikin gida to Allah zai mayar mini da raina har sai na amsa masa” [67].

4- Manzo (S.A.W) ya ce: “Wanda ya ziyarce ni bayan mutuwata kamar ya ziyarce ni ne a rayuwata” [68].
C- Suka ce: Idan yiwuwar alaka da mutumin da yake a duniyar barzahu ya tabbata shin ya halatta a nemi wani abu daga gareshi a kuma yi tawassuli da shi domin biyan bukatu, ko kuma wannan shi ma shirka ne da Allah saboda dalilin fadinsa madaukaki: “Hakika al’amari dukkansa na Allah ne” [69].
Amsa: Hakika dukkan al’amari na Allah ne kuma da nufinsa, da yardarsa ne al’amura suke faruwa, sai dai wannan ba ya kore tabbatar ceto ga annabawa da waliyyan Allah a duniya da lahira bayan samun izinin Allah, kamar yadda muke gani a tabbatar halitta da rayar da matacce da warkar da marasa lafiya da Isa (A.S) ya yi da izinin Allah (S.W.T).
Tunda komai yana tafiya bisa dokar sababi da dalilai sai mu ga Musa (A.S) yana cewa: “Ita sandata ce ina dogara a kanta kuma ina kakkabar ganye ga dabbobina da ita kuma ina da wasu bukatu na daban da ita” [70].
Annabawa tare da ismarsu amma sun nemi taimako da wanin Allah har sai da aka saukar da aya ga manzon Allah (S.A.W) cewa: “Ya kai Annabin Allah da wadanda suke tare da kai na daga muminai sun isar maka” [71].
Zahirin aya yana nuna cewa Annabi abin taimaka wa ne daga Allah da muminai kamar karfafa Isa (A.S) da hawariyyun yayin da ya ce: Waye zai taimake ni zuwa ga (aikin) Allah” [72]. Da kuma karfafa Musa da Haruna (A.S) kuma Allah ya amsa masa da cewa: “Zamu karfafe ka da dan’uwanka” [73] [74].
Sannan mun gani cewa Allah (S.W.T) yana neman taimakon bayinsa da cewa: “In kun taimaki Allah, zai taimake ku” [75]. Da fadinsa: “Wadannan da suka bayar da masauki kuma suka yi taimako wadannan su ne muminai” [76].
D- Suka ce: Idan muka yarda da halaccin neman taimako da tawassuli da wanin Allah domin ya kasance da izinin Allah da nufinsa, to menene dalilin neman taimako da mamaci tare da cewa abin da ya tabbata da dalili shi ne tawassuli da neman taimako da annabi ko waliyyi a rayuwarsa ba bayan mutuwarsa ba?.
Amsa: Sahabbai ba su musa tawassuli da Annabi ba a lokacin rayuwarsa da bayan wafatinsa.


27. Attawassuli Na Subhani: Daga 21-68.
28. A’arafi: 180.
29. Bakara: 127-128.
30. Ali Imran: 16.
31. Nur: 63.
32. Anfal: 33.
33. Tauba: 94.
34. Tauba: 74.
35. Nisa’i: 64.
36. Munafikun: 5.
37. Hashar: 10.
38. Inshirahi: 4.
39. A’arafi: 157.
40. Tirmizi Kitabud Da’awati, Babi 119, 3578: 5\531. Da Masnad Ahmad: 4\138, H 16789.
41. Sahih Muslim Sharhin Nawawi: 1\230, 231, 232.
42. Ibn Majah: 1\441. Hadisi 1385. Da Masnad: 4\138 H 16789.
43. Tawassuli Na Subhani: 79.
44. Tirmizi: 5\531, H 3578.
45. Ibn Majah: 1\256, H 778.
46. Kashful Irtiyab: 312.
47. Addurarus Sunniyya: 27. Da Tawassul Ila Hakikatut Tawassul: 300. Da Fatahul Bari: 7\137.
48. Addurarussunniyya Fir Raddi Alal Wahabiyya: 36.
49. Wafa’ul Wafa: 2\1361.
50. Majmu’atur Rasa’il Wal Masa’il: 1\18.
51. Sahihul Buhari: Babu Salatil Istiska’i: 2\32, H 947.
52. Wafa’ul Wafa: 2\1376.
53. Sawa’ikul Muhrika: 274.
54. Ma’ida: 35.
55. Biharul Anwar: J 93, Babi 17 H 19.
56. Biharul Anwar: J 93, B 28.
57. Sahifatul Alawiyya: 51.
58. Ikbalul A’amal Na Ibn Dawus: 2\85.
59. Sahifatus Sajjadiyya: Addu’a 44.
60. Minhajussunna Na Ibn Taimiyya.
61. Maryam: 62.
62. Gafiri: 46.
63. A’araf: 78-79.
64. A’araf: 93.
65. A’araf: 93.
66. Sahihul Buhari: 5\76, Da Sirar Ibn Hisham: 2\639.
67. Sunan Abi Dawud: 2\218. Da Kanzul Ummal: 10\38.
68. Kanzul Ummal: 5\135, H 12372.
69. Ali Imran: 154.
70. Daha: 18.
71. Anfal: 64.
72. Ali Imran: 52.
73. Kasas: 35.
74. Albarahinul Jaliyya: 42.
75. Muhammad: 7.
76. Anfal: 74.

No comments:

Post a Comment