Da yawa daga cikin matasa sukan tambayi kansu, me muka mallaka ne na daga dukiya ballan-tana ma mu dinga tunanin yadda za mu ingantata da kuma amfani da ita cikin rayuwarmu ta yau da kullum.....
Me yiyuwa ne wasu su ga kansu a matsayin marasa abin hannu saboda ba sa aikata abin da sauran manyan mutane suke aikatawa.....wannan tunani ne da ke cike da kuskure. Hakan shi ne yake sanya da yawa daga cikin matasa suke ganin rayuwa a matsayin wani duhu, musiba da kuma bala'i.....
Misali, wata matashiya 'yar shekara goma sha shida, yayin da take rubuta tarihin rayuwarta, ta rubuta cewa:
"Ba zan iya bayyana kome ba.....na wayi gari na kusan rasa duk abin da na sani, na kasance mai yawan tunani da fargaba, mara amincewa da kaina. Duk wani aikin da na fara yi sai in fara jin tsoron sakamakonsa, don haka sai in fara kokonton aikata shi, kullum cikin damuwa da bakin ciki nake. Duk lokacin da na dubi fuskata cikin madubi sai in ganta ba kyan gani, don haka sai na fara tsanan kaina, ina mai burin da ma ba a halicce ni ba".
Wani matashi kuma cewa ya yi:
"A duk lokacin da na dubi kaina cikin madubi, ga ni saurayi, sai in tambayi kaina.....shin wai wannan da nake ganinsa yana kama da ni, zai yiyu in so shi da a ce zai fito daga cikin wannan madubi da izinin Allah kana ya rayu da ni?......"
A wasu lokuta matashi yakan mai da alhakin abin da ya same shi ga iyalansa, musamman ma mahaifansa; don kuwa ba shi da wanda zai mai da wannan tuhuma gare shi in ban da su.
Sannan an hakaito cewa wata matashiya 'yar shekara sha biyar ta ziyarci wani likita ma'abucin littattafan kan yara da kuma matasa. Ko da ta shigo wurinsa tare da mahaifiyarta sai ta bukaci da ta tattauna da shi a kebance......
Ko da suka kebance, sai wannan matashiya ta fara sukan mahaifanta da zarginsu da cewa sun hana ta dama, suna takura mata......
To sai wannan hazikin likita ya tafi wurin mahaifiyar yarinyar don ya ji ra'ayinta dangane da wannan 'ya tata, to amma sai ya ji maganarta sabanin na 'yartata. Daga nan sai ya binciki lamarin kana kuma ya yi amfani da dimbin ilimin da yake da shi, sai ya gano cewa wannan yarinya tana tsoron rashin samun nasara ne da kuma rashin damuwa da sauran mutane suka yi da ita a matsayin cikakkiyar 'ya mace. Ta ki yarda ta mai da laifin ga kanta, don haka sai ta mayar da laifin ga mahaifanta daga lokacin da suka hana ta wani abin da take so.
Hakika muna bukatuwa da kulawan iyaye a yanayi na kebance kana da kuma kulawan manyan mutane a yanayi na gaba daya, sai dai mu ba yara ba ne da za mu dogara gaba daya a kansu.....
Iyali shi ne matakin farko na tafiya, kamar yadda matafiyi ya ke fara tafiyarsa, ko kuma kamar yadda mahayin dutse ya ke fara hawa jikin dutsen......
Sannan kuma iyali shi ne mafaka, wanda muke komawa gare shi a duk lokacin da muka bukaci hakan, musamman ma a mataki mafi tsanani na rayuwa don mu sami matsuguni da kwanciyar hankali......
Duk da irin wannan matsayi da muhimmanci da iyali suke da shi, to amma dole ne mu yi shiri a wannan marhala ta rayuwa, wato lokacin samar-taka, don mu dauki wasu nauye-nauye na rayuwa, don a hankali a hankali mu sami damar daukar dukkan nauyin kawukanmu, kai har ma da na iyalanmu gaba daya a nan gaba, ko kuma al'umman da muke rayuwa a cikinta.....
Yana da kyau tun da farko tun kafin mu sanya kafafunmu cikin wannan rayuwa ta duniya, mu tambayi ce wa; wani guzuri ne wannan rayuwa ta tanadar mana na daga dukiya, karfi da iyawa, don mu yi amfani da su a cikin wannan tafiya tamu ta rayuwa? Wani karfi da iko ne Allah Madaukakin Sarki Ya tanadar mana don mu sanya su zama mana
uwar kudi ko kuma jari a wannan rayuwa, har mu ba da kokari wajen ci gabantar da su da kuma amfani da su a dukkan rayuwarmu? Don haka ya zama wajibi mu kirga irin abubuwan da muke da su mu gani.
1-HANKALI
Wannan shi ne mafi girman dukiya da kuma ma'ajiyar da mu 'yan'Adam muka mallaka kana kuma da shi ne muka bambanta da sauran halit-tu.....kuma shi ne kwanon da yake dauke da ilimi, tunani, masaniyya da kuma kwarewa.....sannan kuma shi ne mai shiryar da mu zuwa ga tafarkin tsira da kuma alheri, wanda kuma yake bambance mana karya da gaskiya, sharri da kuma alheri.....kuma shi ne ke kula da dukkan takun da muka yi don kada mu kauce daga hanya madaidaiciya.....
To amma shin hankali yana iya zama dukiya kana guzuri ga mutumin da ya ki amfani da shi kana kuma ma bai san girma da kimarsa ba?
Masu iya magana sukan ce hankali shi ne matai-maki (waziri) mai yin nasiha; don kuwa shawarar waziri tana amfani ne a lokacin da sarki ya mai da shi mai ba shi shawarar.....to shin za mu sanya hankalinmu a matsayin wazirinmu?
2- IKO
Shi ne wanda a wasu lokuta ake kiransa da 'yancin zaben abin da mutum yake so..... dukkanmu muna da 'yancin yin wani aiki ko kuma barinsa. Iko a wajen mutum yakan sanya shi ya zamanto sama da dukkan halittu wajen aikata abin da yake so, ko kuma barin aikata wani abin da yake bukatuwa da shi, kamar barci, hutu, ci da sha, saboda wata manufa da take sama da wadannan abubuwa.....
Da dama daga cikin magabata sun rage lokutan barci da hutawansu don bincike da kuma karatu, ta yadda suka sami ilimi mai yawan gaske kana kuma suka sami matsayi a wajen al'umma, duk kuwa da cewa ba sa tare da su......
Haka nan ma muminai sukan nisanci ci da sha yayin da suke yin azumi don su bauta wa Ubangijinsu da kuma koyon hakuri da kuma daidaita kansu da marasa abin hannu. Idan har hakuri ya kasance al'ada a gare su, to babu makawa zai iya jure wa da yawa daga cikin wahalhalun rayuwa.
Babu shakka, iko, hakuri da juriya su ne hanyo-yin nasara ga dan'Adam cikin mafi yawan ayyukansa.
3- TAUSAYI
Sanannen abu ne cewa tausayi yafi kasantuwa a wajen matasa, musamman ma a wajen budurwaye don kuwa su ne iyayen gobe..... muna iya ganin yanayinsu na kuka da kuma irin alaka mai tsanani da ke tsakaninsu da kawayensu ko kuma malamansu.......
Hakika ana kirga tausayi a matsayin dukiyar dan'Adam, yakan yi mu'amala da abubuwan da suke kewaye da shi (tausayi), ya so wasu kana ya ki wasu, ya yarda da wasu kana kuma ya ki yarda da wasu, ya yi fatan samun wasu kana kuma ya wofantar da wasu.....
Tausayi shi yake hada mutum da sauran mutane 'yan'uwansa, kana kuma ya dada kara masa kauna da kusanci ga masoya da kuma iyalansa da kuma damuwa da abubuwan da suke damunsu.....
Tausayi da ji a jiki sukan girma a rayuwar matashi ta yadda zai wayi gari yana mu'amala da abubuwan da suke tare da shi cikin tausayi. Za ka gan shi yana komawa karanta wakoki da labarai, kuma yana kaunar zane-zane da abubuwa masu kyau, da kuma kokarin bayyana abubuwan da yake ji a jikinsa ta hanyar zane-zane ko kuma ta hanyar baitocin wake da dai sauran hanyoyi.....
Babu shakka tausayi da ji a jiki dukiyoyi masu muhimmanci ga mutum matukar dai ya san yadda zai yi amfani da su a rayuwarsa.
4- RIYAWA
Hakan ba kamar yadda wasu suke tunanin cewa yakan kawar da matashi daga hakika, ko kuma ya sanya shi ya dinga iyo cikin wata duniya ta daban, ta yadda daga baya zai lalata iko da karfinsa. To amma riyawa (wato mutum ya riya wani abu a zuiyarsa) abu ne mai kyau da kuma amfani, don kuwa tana da gudummawa mai girman gaske a
rayuwar dan'Adam.....
Mai yiyuwa ne mutum ya gudu da abin da yake riyawa daga hakikanin al'amari mai daci, to amma a lokuta da dama mutum yakan koma ga riyawa da kuma jirinjiritsi, ta haka sai ya sami tsammanin faruwar alheri gare shi don kuwa yana so ya zamanto abin koyi ga saura. Kana kuma yana so ya zamanto mutum tsarkakakke marar aibi, don shi kamar yadda mai bincike ko matafiyin da yake tunanin inda zai je ko kuma abin da zai binciko tun ma kafin ya fara tafiyar ko kuma binciken yake ji, to haka shi ma yake ji......
Hakika wannan riyawa abu ne mai kyau ga wannan matafiyin ko kuma mai binciken don kuwa yana da alaka da duniyar hakika......
Riyawa dukiya ce ta hakika gare mu matukar dai mun sami damar hada ta da rayuwarmu ta hanyoyi daban-daban. Kada mu bar riyawa tayi galaba a kan hakikanin al'amurranmu ta yadda za mu ci gaba da zama cikin kogin fata da buri, haka nan kuma kada mu bari hakika ta galabci riyawa, don kada burace-burace da fatanmu su kasance a takure. Ya kamata mu bar wa riyawa gudummawarta ta fata da buri, sannan kuma mu yi riko da hakika wajen cimma wadannan burace-burace da kuma fata.
5- LAFIYA....Kaddara Ce Da Ba 'a Kwatantata Da Dukiya...
Ya zo cikin hadisi cewa wajibi ne mu ribanci abubuwa biyar kafin faruwar wasu abubuwan biyar:
samartaka kafin tsufa, faraga kafin ayyuka su yi yawa, karfi kafin rauni, rashin lafiya kafin ciwo.....
Ya rage mana mu dakata mu dan yi tunani kan wannan dukiya da Allah Ya arzurtamu da ita.....yaya za mu yi idan muka rasa ta ba tare da mun shirya ba.....
Da dama daga cikin marasa lafiya sukan yi burin ina ma da suna da lafiya, don su ci gaba da ayyukansu na rayuwa.......
Hakika lafiya kaddara ce wacce dole ne mu kula da kuma kare ta ta hanyar ba ta abincin da ya dace, tsabta da kuma wasannin motsa jiki.....sannan kuma dole ne mu ba da muhimmanci ga daya bangaren kiwon lafiyan, shi ne kuwa tsabtace kawukanmu daga munanan ayyuka, keta, hassada, kiyayya da kuma canza su da kyawawan ayyuka, kamar yadda muke kula da tsabtar jikinmu.
Bayan samuwar wadannan kaddarorin, shin a matsayina na matashi zan ji cewa ni fakiri, marar abin hannu ne, musamman ma cewa wadannan ni'imomi ba wai sun kare a kan ni'imomin da na hadu da wanina a kansu ba ne, a'a akwai wadansu ni'imomin da suka kebanta da ni kawai. Don ko wane mutum akwai ni'imomin da ya kebantu da su shi kadai.....ba abin da ya rage masa face kawai ya yi amfani da kuma daukaka su kamar yadda dan kasuwa yake amfani da uwar kudinsa wajen nemo riba da hada su da uwar kudin nasa don ya ci gaba da jujjuya su.....
Bayan dukkan hakan, akwai wadansu ni'imomin da muna iya sanya su cikin rayuwarmu, kuma su haifar mana da canje-canje masu girman gaske cikin rayuwarmu sannan kuma su sanya mu mu zamanto masu iya kirkiro muhimman ayyuka da za su kai mu ga manufofi da kuma hadafofinmu na rayuwa. Wadannan ni'imomi kuwa suna nan a cikin rayuwarmu, musamman ma a shekarun samartaka, da za su iya tabbatar mana da wadansu abubuwan da ba za mu taba tunanin afkuwarsu ba.....daga cikinsu, akwai:
1- KIRKIRA
ita ce karfi, shiri da kuma iyawan da mutum yakan samu ta hanyar hankali, ilimin da kuma masaniyar da yake da shi......
Kirkira tana daga cikin sirrorin da suke haifar da daukaka a rayuwa, kuma takan sa ma'abucinta ya sami daman gano sabbin hanyoyin canza duniya da kuma tsira daga rashin ci gaba.....
Idan har muna son binciko irin wadannan iyawa a cikin rayuwarmu, dole ne mu sanya wadansu alamomi a gabanmu, mu bi hanyar kirkira tare da su. Wadannan alamomi kuwa su ne:
• Karfafa riyawa da ji a jiki.
• Karkatar da ji-a-jika zuwa ga kyawawan manufofi.
• Raya tunani, wayewa da kuma masaniya.
• Saukaka rayuwa da rashin kuntata wa kai.
• Haifar da tsari ga abubuwa marasa tsarin.
• Haifar da sabbin abubuwa a ko da yaushe.
• Mu so kanmu da sauran mutane, to amma son namu ya kasance fiye ga Mahalicci.
• Mu yi abokantaka da ma'abuta kirkira.
• Mu dinga karanta littattafa, labarai da wakokin da za su sanya mana tunanin kirkiran abubuwa, ba mu kasance masu koyi ba.
2- IMANI
Karfi ne mai girman gaske wanda muke samunsa ta hanyar ingantacciyar akida da yarda da Mahaliccin duniya kana kuma Mai jujjuya ta, bugu da kari kan ganin girma da kamalarSa cikin dukkan halittu, manya da kananansu da kuma jin rahamarSa wacce ta mamaye dukkan kome. Sannan kuma ta hanyar bauta maSa, wacce take kawata mutum da karfin ruhi, mutum yakan zama mai karfi da juriya yayin wahalhalu.....
Imani ni'ima ce wacce matashi yakan same ta cikin sauki sama da waninsa saboda zuciyarsa a bude take wajen karbar yanayin rayuwa, shin wannan yanayi na madda (duniya) ne ko kuma na ma'anawiyya (na ruhi da lamurra lahira).
3- MADAUKAKIYAR HIMMA
Wannan wata ni'ima ce da kuma karfi mai girman gaske da ke kai mutum zuwa ga manufarsa da kuma nesantar da shi daga fargaba da kuma yanke kauna.
An ruwaito wani hadisi yana cewa mutum yana tashi da himmarsa kamar yadda tsuntsu yake tashi da fuka-fukansa.....don haka mutum yana bukatuwa da himma madaukakiya a hanyarsa ta isa ga sa'ada da kuma ci gaba.....wannan hanya da take tabbatar masa da manufarsa ta rayuwa.....
Lalle babu makawa muna iya isa ga wannan babbar ni'ima idan muka yi riko da wasu ka'idoji a rayuwarmu, su ne kuwa:
1. Mu dinga tuna cewa mu mutane ne kuma za mu iya kaiwa zuwa ga kamalar da muke so.
2. Mu daure taragonmu zuwa ga tauraro (sama), kamar yadda masu iya magana su kan ce wai: himma bata ga rago.
3. Kada mu shagaltar da kanmu da kananan al'amurra marasa muhimmanci.
4. Mu kyautata alakarmu da sauran mutane, kada mu bari maslaharmu ta kewaye mu.
5. Mu kasance masu kula da ka'ida hatta cikin zaben manufofi da hanyoyin da za mu isa gare su.
6. Mu ba da muhimmanci ga kyawun badini kamar yadda muke kula da kyawun zahiri.
7. Mu zabi abokai masu madaukakiyar himma.
Abubuwan da muka ambata a wannan fasali su ne mafi muhimmancin ni'ima da kyautar da muka mallaka mu matasa, ko kuma abubuwan da muke da damar samo su ta hanyar karfi da kuma shirin da muke da shi. Lalle ya kamata mu yi imani da cewa rayuwa da kuma Mahaliccinta Suna iya kara mana wadannan ni'imomi, matukar dai muka ci gaba da bincike da kuma bahasi, don kuwa ajiyoyin rayuwa ba sa da iyaka "....kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba.....".
No comments:
Post a Comment